Abdullahi Ɗan Yahaya Al-hadarami
Abdullahi Ɗan Yahaya Al-hadarami (Larabci: عبد الله بن يحيى الحضرمي) yana daga cikin dakarun rundunar shurɗatul Al-khamis, sojojin Imam Ali (A.S) a lokacin yaƙin jamal. ya yi shahada bayan sulhun Imam Hassan (A.S) sun shahadantar da shi bisa umarnin Mu'awiya, cikin wasiƙar da Imam Hassan (A.S) ya aika zuwa ga Mu'awiya ya yi ishara kan kashe Abdullahi ɗan Yahaya Al-hadarami tare da nuna hakan matsayin karya alƙawari da yarjejeniyar sulhu da suka yi.
Suna Da Nasaba
Abdullahi Ɗan Yahaya Al-hadarami ana nasabta shi zuwa yankin Hadaramauti na ƙasar Yaman, sunan shi ya zo a wasu daga cikin litattafai da Abdullahi ɗan Bahar,[1] koma Abdullahi Ɗan Nuji,[2] wannan kuskure ne da aka yi da Abdullahi ɗan Yahaya,[3] kuma alkunyar shi ita ce Abu Rida[4] ko kuma Abu Ar-radi.[5]
Mahaifin shi ne Yahaya Al-hadarami yana cikin sahabban Imam Ali (A.S) kuma yana cikin Shurɗatul Al-Khamis.[6] kuma ya kasance tare da Imam Ali (A.S) a yaƙin siffin.[7]
Halartar Yaƙin Jamal
Abdullahi ya kasance a lokacin halifancin Imam Ali (A.S) daga cikin shurdatu khamis,[8] kuma ya halarci yaƙin Jamal ya zo cewa Imam Ali (A.S) ana cikin yaƙi ya ce mishi ka yi bushara ya kai ɗan Yahaya, lalle kai da mahaifinka kuna cikin Shurɗatul Khamis, kuma haƙiƙa Annabin Allah ya bani labari da sunanka da sunan mahaifinka a cikin Shurɗatul Khamis kuma Allah ne ya kira ku da wannan suna.”[9]
Shahadantar Da Shi
Abdullahi ya kasance koda yaushe yana magana kan falalolin Imam Ali (A.S),[10] bayan shahadar Imam Ali (A.S) sai ya nunawa Mu'awiya irin san da yake yi wa Imam Ali (A.S) sai Mu'awiya ya yi umarni da a kashe shi kuma a kashe magoya bayanshi,[11] Allama Amini ya naƙalto daga littafin Al-muhabbar cewa Ziyad ɗan Abihi shi ne wanda ya rataye shi a ƙofar gidan shi kuma ya barshi rataye tsawon wasu kwanaki a.[12] kamar yadda ya zo cikin wata wasiƙa ta Imam Hassan (A.S), zuwa ga Mu'awiya cewa Ziyad ya yi isgili da gawar Abdullahi bayan ya kashe shi.[13]
Martanin Imam Hassan da Husain (A.S)
Shaik Saduƙ ya rawaito daga littafin Alfuruƙ bainal Abaɗil wa huƙuƙ cewa Mu'awiya bayan ya warware sulhu tsakanin shi da Imam Hassan (A.S), Imam ya rubuta mishi wasiƙa yana mai tina mishi warware alƙawarin da ya yi ta hanyar take sharuɗɗan sulhu, a farkon wasiƙar Imam ya yi nuni kan kashe Abdullahi ɗan Yahaya Alhadrami wanda Mu'awiya ya yi.[14] kazalika shima Imam Husaini (A.S) ya zargi Mu'awiya da kashe Abdullahi ɗan Yahaya a wata wasiƙa da ya rubuta zuwa gare shi.[15]
Matsayin Abdullahi Ɗan Yahya Kan Rawaito Hadisai
Shaik Ɗusi ya ce Abdullahi ɗan Yahaya yana daga cikin masu rawaito hadisan Imam Ali (A.S),[16] kuma ruwayoyi da yawa sun zo ta hanyar shi a litattafan Shi'a da Ahlus-sunna.[17]
Bayanin kula
- ↑ Al-Amin, A'ayan Shi'a, juzu'i na 2, shafi na 350.
- ↑ Al-Tosi, Rijal Al-Tosi, shafi na 71.
- ↑ Al-Amin, A'ayan Shi'a, juzu'i na 2, shafi na 350
- ↑ Al-Tosi, Rijal Al-Tosi, shafi na 71
- ↑ Al-Mufid, Al-IKhtisas, shafi na 3.
- ↑ Al-Khoei, Majam Rijal al-Hadith, juzu'i na 20, shafi na 98.
- ↑ Ibn Kathir, Al-bidaya waAl-nihaya, juzu'i na 8, shafi na 199.
- ↑ Al-Mufid, Al-Ikhtisas, shafi na 3
- ↑ Al-Kashshi, Al-Rijal, shafi na 6.
- ↑ Ale-Yasin,Sulhu Al-Hasan (AS), shafi na 347.
- ↑ Ale-Yasin,Sulhu Al-Hasan (AS), shafi na 347.
- ↑ Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 11, shafi na 79-80.
- ↑ Al-Tabarsi, al-Ihtijaj, juzu'i na 2, shafi na 297.
- ↑ Saduq, Ilal al-Shara’i’, juzu’i na 1, shafi na 212.
- ↑ Al-Tabarsi, Al-Ihtijaj, juzu'i na 2, shafi na 297.
- ↑ Tusi, Rijal, shafi na 71.
- ↑ Abu Maash, Al-Arabain fi Hubb Amir al-Mominin, juzu'i na 6, shafi na 118; Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 38, shafi na 304.
Nassoshi
- Abu Ma’ash, Saeed, Al-arba’in fi hubbi Amirul Muminin Ali binu Abi Talib, (A.S), Kum, wanda Al-I’tisam ya buga, 1378 bayan hijira.
- Al-Amin, Mohsen, A'ayanul Shi'a, Beirut, Dar Al-Ta'arif, 1403H.
- Al-Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir fi kitab wa Sunnah wa Adabi, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, 1416H.
- Al-Kashi, Rijal Al-Kashi (Ikhtiyar Ma’rifat Al-Rijal), Mashhad, Jami’ar Mashhad, 1348H.
- Al-Khoei, Al-Sayyid Abu Al-Qasim, Mujam Rijal Al-Hadith, Qum, Al'adun Musulunci, 1372H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar Al-Jami’a Lidurar Akhbar Al-Akhbar Al-Pure Imams, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1403H.
- Al-Mufid (Mansub), Muhammad bin Muhammad, Al-Ikhtisas, Qum, taron Sheikh Al-Mufid, 1413H.
- Al-Saduq, Ilal al-Shara’i’, Najaf, Al-Haidariyya Library Publications, 1385H.
- Al-Tabarsi, Ahmad, Al-ihtijaj ala Ahlil Lajaj, Mashhad, Mortada, 1403H.
- Al-Tusi, Mazajen Al-Tusi, Mashhad, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1413 AH/1381H.
- Ibn Kathir al-Dimashqi,Al-bidaya wa Al-nihaya, Beirut, Darul Fikr, ed.
Ale-Yasin, Radi Sulhu Al-Hasan, (A.S), Beirut, Al-Alami, 1412 AD.