Abdullahi Ɗan Abi Husaini Al-Azdi Al-bajali
- Yana da banbanci da kasida mai taken Abdullahi Ɗan Abil Husaini Al-Azdi
Abdullahi Ɗan Abil Husaini Al-azdi al-bajali, (Larabci: عبد الله بن أبي الحُصين الأَزدي البجلي) yana daga cikin sojojin Umar Ɗan Sa'ad a Waƙi'ar Karbala, kuma yana daga cikin mayakan Amru Ɗan Hajjaj, waɗanda suka kange Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi da ruwan da za su sha, Abdullahi Ɗan Abil Husaini Al-azdi al-bajali ya halaka sakamakon addu'ar Imam Husaini (A.S) ya yi a kansa.
Sunan shi Da Nasabarsa
Sunanshi Abdullahi Ɗan Abil Husaini, kuma sunanshi ya zo a wasu wurare a cikin wasu litattafai kamar haka, AbdullahiƊan Husain,[1] ko Abdullahi ɗan Hasan Al-Azdi,[2] an ambaci sunanshi a cikin ƙabilar Bajila.[3]
Gudunmawar Da Ya Bayar A Cikin Sojojin Umar ɗan Sa'ad
Abdullahi Ɗan Abil Husaini ya kasance a yakin ɗaf cikin rundunar Umar Ɗan Sa'ad, inda ya kasance a ƙarƙashin jagorancin Amir ɗan Hajjaj kuma yana daga cikin waɗanda suka kange ruwa da Imam Husaini (A.S), kamar yadda Umar Ɗan Sa'ad ya samu wasiƙa a ranar bakwai ga watan Muharram Haram daga Ubaidullah Ɗan Ziyad, ya umarce shi da su hana Imam Husaini (A.S) isa gurin ruwa su kange shi da kada ya ƙarasa gurin ruwa, sai Umar ya aika da Amir Ɗan Hajjaj da rundunarshi, suka sauka a gaban mashayar ruwan na Furat, ya zo a cikin litattafai cewa; Abdullahi ɗan Abil Husain ya yi magana da Imam Husaini (A.S) yana mai cewa.
"Ya Husaini, ba za ka kalli ruwa ba, kamar misalin zuciyar sama? Wallahi ba za ka ɗanɗana shi ba har sai ka mutu da ƙishirwa". Imam Husaini(A.S) ya ce: Ya Allah ka kashe shi yana mai jin ƙishirwa, kuma ka da ka gafarta mishi,[4] bisa abin da Hamid ɗan Muslim Al-azdi ya rawaito, Abdullahi Ɗan Abil Husaini (A.S) ya kamu da ciwon ƙishirwa bayan waƙi'ar ɗaf duk yadda ya yawaita shan ruwa to haka ƙishirwarshi za ta ƙaru har ya mutu sakamakon yawan shan ruwa .[5]
Bayanin kula
- ↑ Al-Baladhuri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 3, shafi na 181; Al-Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 2, shafi na 87; Ibn Nama, Makith al-Ahzan, shafi na 71; Al-Qummi, Nafs Al-Mahmoum, shafi na 301; Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 44, shafi na 389; Al-Tabarsi, I’lam Al-Wari, shafi na 325.
- ↑ Ibn al-Jawzi, Tadhkirat al-Khawas, shafi na 223.
- ↑ Ibn al-Atheer, Al-Kamil, juzu'i na 3, shafi na 281 da 303; Sashe na 4, shafi na 53; Ibn A’tham, Al-Futuh, juzu’i na 5, shafi na 412.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-An'ul-Mulk, juzu'i na 5, shafi na 412; Al-Balazari, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 3, shafi na 181; Ibn Atham, al-Futuh, juzu'i na 5, shafi na 412.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-umam wa al-muluk, juzu'i na 5, shafi na 412; Ibn Atham, al-Futuh, juzu'i na 5, shafi na 412; Ibn al-Athir, al-Kamel, juzu'i na 4, shafi na 53 da 54.
Nassoshi
- Ibn al-Atheer, Ali bin Muhammad, 'Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Sader, 1385 AH/1965 AD.
- Ibn A'tham al-Kufi, Ahmad, Al-Futuh, bugun: Ali Al-Shiri, Beirut - Lebanon, bugun: Dar Al-Adwaa, 1411 AH/1991 Miladiyya.
- Ibn al-Jawzi, Yusuf, Tadhkirat al-Khawas, Qom - Iran, mawallafi: Al-Sharif Al-Radi Publications, 1418 AH.
- Ibn Nama al-Hilli, Jaafar bin Muhammad, 'Mudsirul Ahzan, Qum - Iran, Mawallafi: Wallafar Mazhabar Imam Mahdi (A.S), 1406H.
- Al-Baladhuri, Ahmed bin Yahya, Ansabul Ashraf', editan: Muhammad Baqir al-Mahmoudi, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Ta'arif na Wallafe-wallafe, 1397 AH/1977 AD.
- Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-umam wa al-muluk, editan: Muhammad Abu Al-Fadl Ibrahim, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Turath, 138H/1967 Miladiyya.
- Al-Tabarsi, Al-Fadl bin Al-Hassan, 'I'lam Al-Wara, Tehran - Iran, Publisher: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, D.T.
- Al-Qummi, Abbas, Nafsul mahmum fi musibatil sayyidina Husaini almazlum,', Najaf - Iraki, Mawallafi: Al-Haidariyya Library, D.T.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar Al-Jami'a Li'drar Al-Akhbar Al-Pure Imams, Beirut - Lebanon, mawallafi: Mu'assasa Al-Wafa, 1404H.
- Al-Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad, Qom - Iran, Mawallafi: Taron kasa da kasa na Sheikh Al-Mufid, 1413H.