Abdullahi Ɗan Abi Husaini Al-Azdi

Daga wikishia
A banbance shi da Abdullahi Ɗan Abi Husaini Al-Azdi Al-bajali

Abdullahi ɗan Abil Husaini Al-azdi (Larabci: عبد الله بن أبي الحُصين الأَزدي) ya yi wafati a shekara ta 37 hijirar manzon Allah (S.A.W) kuma ya kasance yana daga cikin sahabban Imam Ali (A.S) kuma yana cikin shahidan yaƙin Siffin..[1] Lokacin da rundunar Imam Ali (A.S) suka isa Raƙƙa, a kan hanyar su ta zuwa Siffin, a lokacin da suke tsallaka wata gada, sai hular Abdullahi ɗan Abi Al-Husain Al-az-di ta faɗo saboda cunkuson dawakai a kan gadar. sai ya sauka ya ɗaukota, sai hular Abdullahi ɗan Hajjaj Al-azdi ta faɗo, sai shi ma ya sauko ya ɗaukota, sannan ya ce wa Abdullahi ɗan Abi Hosain Al-bajali:

"Idan zatan Azzajiri Aɗɗayyar ya kasance gaskiya, kamar yadda suka yi tinani, to za a kashe ni da wuri, kuma kai ma za a kashe ka."

Sai ya ba shi amsa yana mai cewa; ba bu abin da na ke so kamar abin da ka ambata.[2] Abdullahi ɗan Abi Hosain yana daga cikin masu karatun kur'ani, wadanda suka raka Ammar ɗan Yasir zuwa fagen daga, kuma aka kashe shi tare da Ammar,[3] Kafin ya tafi fagen daga, Mukhnaf ɗan Salim Al-azdi ya ce ma shi: Mu munfi buƙatar ka fiye da Ammar, amma ya ƙi ya tsaya tare da mu, sai ya raka Ammar aka kashe shi tare da Ammar.[4]

Bayanin kula

  1. Al-Zarkali, Al-Alam, juzu'i na 4, shafi na 83.
  2. Al-Tabari, Tarikh Al-Umamwa al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 566; Al-Manqari, Waqqa Siffin, shafi na 152.
  3. Al-Tabari, Tarikh al-umam wa Al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 566; Juzu'i na 5, shafi na 27; Ibn Khaldun, Diwan al-Mubatda wa al-Khobar, juzu'i na 2, shafi na 631; Ibn al-Athir, al-Kamel, juzu'i na 3, shafi na 281.
  4. Al-Manqari, Waqqa Siffin, shafi na 152.

Nassoshi

  • Ibn al-Atheer, Ali bin Muhammad, 'Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Sader, 1385 AH / 1965 AD.
  • Al-Manqari, Nasr bin Muzahim, 'wak'atu Siffin, editan: Abdulsalam Muhammad Haroun, Alkahira - Masar, mawallafin: Modern Arab Foundation, bugu na 2, 1382 AH, buga buga a Qom, Al -Marashi Al-Najafi Publications Library, 1404 e.
  • Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, 'Tarikh Al-umam wa al-muluk, editan: Muhammad Abu Al-Fadl Ibrahim, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Turath, 1387 Hijira / 1967 Miladiyya.
  • Al-Zarkali, Khair al-Din, ' Fitattun 'Kamus na Tarihin Rayuwar Shahararrun Maza da Mata na Larabawa, Larabawa, da 'Yan Gabas, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Ilm Lil-Malayin, 1989 AD.
  • Ibn Khaldun, Abd al-Rahman bin Muhammad, Diwan Al-mubtada'u wa Kahabar fiTarikh Araba wa al-barbar wa man asarahum min zawai sha'ani, edited by: Khalil Shehadeh, Beirut - Lebanon , Mawallafi: Dar Al-Fikr, 1408H/1988 Miladiyya.

Template:End)