Abdullah ɗan Manzon Allah
Abdullah ɗan Manzon Allah (S.A.W) (Larabci:عبد الله بن رسول الله (ص)) da Khadija wanda ya mutu tun yana ƙaramin yaro, kan asasin rahotanni daga Masadir na tarihi bayan Mutuwar Abdullah ne Asu ɗan Wa'il ya yiwa Annabi (S.A.W) gorin rashin samun zuriya ya kira shi da sunan Abtar (Mai yankakken baya) sai suratul Kausar ta sauko don raddi da martani kan maganar Asu ɗan Wa'il.
mafi yawan masadir ɗin tarihi sun bayyana cewa an haifi Abdullah bayan aiko Annabi (S.A.W)[1] na'am akwai wani naƙalin da ya ba da rahoto kan cewa an haife shi tun kafin aiko Annabi (S.A.W)[2] sannan ana yiwa Abdullah laƙabi da Ɗayyib da Ɗahir,[3] saboda bayan saukar wahayi aka haife shi.[4] [Tsokaci 1] Abdullah ya rasu a Makka tun yana ƙaramin yaro,[5] a rahoton Ahmad ɗan Yahaya Balazri cikin littafin Ansabul Ashraf bayan rasuwar Abdullah, Asu ɗan Wa'il ya kira Annabi (S.A.W) da Mai yankakken baya, saboda duk yaron da aka haifa masa mutuwa yake yi baya rayuwa, da wannan dalili ne aka saukar da suratul kausar martani kan maganar Asu ɗan Wa'il da ayar:[6]
Wannan ayar martani ce kai tsaye kan maganar Asu ɗan Wa'il.[7] Kan asasin riwayar da Kulaini ya kawo cikin littafin Al-Kafi, haƙiƙa bayan rasuwar Abdullahi Khadija ta yi kuka, sai Annabi (S.A.W) ya ce mata: Shin ba za ki yi farin ciki ba ranar Al-ƙiyama Abdullah ya tsaya ƙofar Aljanna har sai kin zo, bayan ya ganki sai ya kama hannunki ya shigar da ke mafi alherin mahallin Aljanna ba… Allah shi ne mafifici da ɗaukaka fiye da ya karɓe kayan marmarin zuciyar bawa (ƴaƴansa) daga gare shi kuma wannan bawan Allah ya yi haƙuri saboda Allah da gode masa, amma Allah sai ya azabtar da shi[8]
Bayanin kula
- ↑ Misali, duba: Ibn Hajar Asƙalani, Al-Isabah, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi:445; Moghrizi, Imta'ul Al-Asma, 1420 AH, juzu'i na 5, shafi na 333.
- ↑ Ibn Is'haƙ, Siratu Ibn Is'haƙ, 1410H, shafi na 82.
- ↑ Ibn Hajar Asƙlani, Al-Isabah, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 445; Moghrizi, Imta'ul Al-Asma, 1420 AH, juzu'i na 5, shafi na 333.
- ↑ Amin, A'ayan Al-Shia, 1406 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 223
- ↑ Moghrizi, Imta'ul Al-Asma, 1420 AH, juzu'i na 5, shafi na 333.
- ↑ Suratul Kauthar, aya ta 3.
- ↑ Balazari, Ansab Al-Ashraf, 1417 AH, Juzu'i na 1, shafi na 138-139.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1362, juzu'i na 3, shafi na 219.
Tsokaci
- ↑ a cewar Fadlu bin Hassan Tabrisi wasu sun yi kuskure sun tsammaci cewa tayyib da tahir suna ne na `ya`yan Annabi guda biyu daidai lokaci da suna ne na Abdullahi
Nassoshi
- Ibn Is'haƙ, Muhammad bin Is'haƙ, Siratu Ibn Is'haƙ, ƙum, Sashen Nazarin Tarihi da Ilimin Musulunci, bugun farko, 1410H.
- Ibn Hajr Asƙlani, Ahmed bin Ali, Al-Hadafa fi Tamiyez Sahabah, Beirut, Daral-e-Kitab Al-Alamiya, 1415H.
- Amin, Mohsen, A'ayan Al-Shi'ah, Beirut, Dar Taƙƙin Lal-Mahabbat, 1406H.
- Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Beirut, Darul Fikr, bugu na farko, 1417H.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Wari's Media with Allam Al-Hadi, ƙum, Al-Bait, bugu na farko, 1417H.
- Kulaini, Mohammad bin Yaƙub, Al-Kafi, Tehran, Islamia, bugu na biyu, 1362.
- Moghrizi, Ahmad bin Ali, Imta'ul Al-Isma'a Bima lil'Nabi min Al-Ahwal wa Al-Amwal wa al-Hefda wa al-Mata'a, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, first edition, 1420 AH.