Ƙira'ar Hafsu Daga Asim

Daga wikishia

ƙira'ar Hafsu daga Asim, wata shahararriyar riwaya ce daga ƙira'ar Asim ɗan Bahdala Abi An-najudi Kufi, ɗaya daga cikin ƙurra'us As-saba'a, wace almajirinsa Hafsu ɗan Sulaiman Asadi ya naƙalto. ƙurra'u misalin Abubakar ɗan Ayyash su ma sun naƙalto ƙira'ar Asim; amma riwayar Hafsu ta fi ta su samun shahara. Riwayar Hafsu Sakamakon gwanancewa cikin ƙira'a da fasaha da kuma kasancewa mafi ƙarantar saɓawa da ƙira'ar Asim ne ya san tafi sauran riwayoyin samun karɓuwa, wanan ƙira'a ta Hafsu ta yaɗu a wannan zamani da kusan kaso 95 a ƙasashen musulmi.

Masana ƙira'a suna ganin sanadin ƙira'ar Hafsu daga Asim ya isa ga Annabi (S.A.W) kuma ingantaccen isnadi ne, kuma suna cewa Asim ya karɓo wannan ƙira'a daga Imam Ali (A.S) ta hanyar mutum ɗaya wanda ake kira da suna Abu Abdur-rahman Sullami, malamai suna ganin Asim mutum mai amana da taƙawa, sannan kuma mutum mafi fasahar ƙira'a, haka nan shi ma Hafsu ana ganinsa mafi ilimi cikin almajiran Asim dangane da ƙir'arsa, ana ganinsa matsayin mutum da za a iya dogara da shi cikin fannin ƙira'a, an gabatar da Abu Abdur-rahman sullami matsayin amintacce mutum, mutum mai girma.

Game da sanin daga wanne zamani ne ƙira'ar Asim da riwayar Asim ta samu shahara a ƙasashen musulmi, akwai saɓani wurin malamai: Muhammad Hadi Marifat yana ganin wannan ƙira'a tun farkon samuwarta ta kasance karɓaɓɓiyar ƙira'a da ta samuwa yaɗuwa wurin bakiɗayan musulmi, wasu suna ganin cewa karɓuwa da yaɗuwar ƙira'ar Asim da riwayar Hafsu ya fara ne daga ƙarni goma bayan hijira sakamakon ƙoƙarin da daular usmaniyya ta yi kan hakan.

Matsayi Da Muhimmanci

ƙira'ar Asim tare da riwayar Hafsu ɗan Sulaiman Asadi daga ƙira'ar malaminsa Asim ɗan Abi An-najud Kufi, tana daga cikin sanannun ƙira'o'i guda bakwai.[1] an ce wannan ƙira'a tana daga cikin ƙira'o'i mutawatirai karɓaɓɓu.[2] a cewar Muhammad ɗan Isma'il Al-mash'hadani, malami mai bincike da koyar da fannin ilimin nahawu a jami'ar mosul a ƙasar iraƙi, ƙira'ar Asim da riwayar Hafsu ta samu karɓuwa da yaɗuwa a yanzu kusan kaso 95% daga ƙasashen musulmi , kaso 5% daga sauran ƙasashen suke amfani da sauran ƙira'o'i daga ƙira'o'i guda bakwai.[3]

Na'am jama'a masu yawa sun rawaici ƙira'ar Asim kai tsaye ko kuma ta hanyar wasu.[4] amma dia ita riwayar Hafsu da riwayar Abubakar ɗan Ayyash su ne suka fi samun shahara sosai.[5]

Ingancin ƙira'ar Hafsu Daga Asim

Masana fannin ƙira'o'i suna ganin riwayar Hafsu daga ƙira'ar Asim sanadinta zuwa ga Annabi (S.AW) yana da inganci;[6] saboda shi Asim ya naƙalci wannan ƙira'a kai tsaye daga Imam Ali (A.S) ko kuma ta hanyar Abu Abdur-rahman sullami, shi kuma Imam Ali (A.S) ya rawaito ta ne daga Manzon Allah (S.A.W). haka kuma, Asim ya koye ta ne a hannun Zar ɗan Habishu wanda shi ma ya koya daga Abdullahi ɗan Mas'ud shi kuma ya karɓota daga Annabi (S.A.W)[7] a gefe guda kuma wannan ƙira'a da Hafsu ya naƙalto, haƙiƙa shi hafsu ya kasance mafi kwazon almajiran Asim.[8]

Muhammad Hadi Marifat mai bincike kan ilimin kur'ani kuma malami masanin fiƙihu a shi'a (Wafati:2017.m) ya tafi kan cewa ƙira'ar Hafsu daga Asim, iata kaɗai ce ƙira'a da sanadinta zuwa ga Annabi (S.A.W) yake da inganci, tun farkon ɓullowarta ta samu ƙarfafuwa daga dukkanin musulmi, bayan wucewar ƙarnoni masu yawa al'umma bayan al'umma ta dinga samun yaɗuwa da bazuwa kuma har zuwa wannan zamani na yanzu ta kasance ƙira'ar da take yawo tsakankanin musulmi.[9]

A cewar Ibn Nadim Asim ya karɓo wannan ƙira'a ta sa daga Abu Abdur-rahman sullami da Zar ɗan Habishu.[10] Amma Abubakar Ayyash ɗaya daga cikin marawaitan ƙira'ar Asim yana cewa: “ Asim ya gaya mini, in banda Abu Abdur-rahman Sullami babu wani da koya min karatun kur'ani, lokacin nake dawowa daga wurinsa ne na bijiro wannan ƙira'a gaban Zar ɗan Habishu”.[11]

Akwai saɓani dangane da daga wurin wane sahabi ne shi Sullami ya karɓo wannan ƙira'a:[12] wasu suna cewa Abu Abdur-rahman sullami ya koyi karatun kur'ani daga Imam Ali (A.S), Usman da Abdullahi ɗan Mas'ud, kuma ya bijiro da wannan ƙira'a a gabansu.[13] an naƙalto daga wasu ba'ari cewa ya koyi kur'ani daga Imam Ali (A.S) sannan ya kaiwa Usman ya nuna masa.[14] haka nan an ce ya karɓo kur'ani daga Usman ya bijiro da shi gaban Imam Ali (A.S),[15] Muhammad Hadi Marifa da naƙali daga Shamsud-dini Zahabi yana cewa Abu Abdur-rahman Sullami ya karɓo kur'ani daga Abdullahi ɗan Mas'ud sannan ya gabatar da shi gaban Imam Ali (A.S),[16] wasu ba'ari daga masana su ma sun kasance kan magana cewa ya karɓo ne daga Imam Ali (A.S) ya kuma gabatar masa da bakiɗayan ƙira'ar.[17]

Yaɗuwar ƙira'ar Hafsu Daga Asim

Masana ƙira'a sunacewa haƙiƙa zaɓar ƙira'ar Asim da daular Usmaniyya ta yi tare da buga kur'ani da yaɗa shi a duniya kan asasin wannan ƙira'a ya faru tun kusan ƙarni na goma bayan hijira, hakan shi ne ya kasance dalilin yaɗuwar wannan ƙira'a da tabbatuwarta tsakankanin al'ummomin musulmi.[18] Ali Muhammad Dabbag, masanin ƙira'o'i mutumin ƙasar misra (Wafati:1380.h.ƙ). ya rubuta cewa fara yaɗuwa da bazuwar wannan ƙira'a a faɗin duniya ya kasance daga tsakiyar ƙarni na goma sha biyu bayan hijira.[19]

Shafi na farko tauzihat kur'an bugun kasar saudiya a shekara 1441,h.q

Su Wane ne Marawaita

Tushen ƙasida: Hafsu ɗan Sulaiman Asadi, Asim ɗan Abi An-najud Kufi

Abu Abdur-rahman sullami: ɗaya ne daga cikin tabi'ai a garin kufa kuma ya kasance daga ma'abota ƙira'ar kur'ani, ya koyi karatun ƙira'a daga ba'arin sahabban Annabi (S.A.W).[20] masana ilimin rijal suna ganin Abu Abdur-rahman sullami matsayin siƙa amintacce mai girma matsayi.[21]

Zar ɗan Habishu: kamar yadda Ibn Nadim yake cewa, haƙiƙa ya kasance wanda Asim ya gabatar masa da ƙira'a.[22] ya kasance daga tabi'ai na garin kufa, kuma yana cikin ƙurra'a ɗabaka ta bakwai.[23] kama yadda aka naƙalto an bayyana cewa ya karɓo wannan ƙira'a daga Abdullahi ɗan Mas'ud[24] da Imam Ali (A.S).[25]

Asim ɗan Bahdala Abi An-najud: wanda aka fi sani da Asim yana cikin ƙurra'us as-saba'a mutumin garin kufa.[26] galibin masana ilimin rijal suna ganin Asim matsayin siƙa amintacce kuma ma'abocin taƙawa.[27] suna ganin ƙira'arsa matsayin ƙira'a mafi cika da fasaha cikin ƙira'o'i.[28] an naƙalto daga wasu ba'ari cewa haƙiƙa Asim ya fi saura dandaƙewa da tantancewa cikin ƙira'a da kuma taka tsantsan.[29] Hafsu ɗan Sulaiman: mutumin garin kufa kuma ɗan matar Asim. Ya koyi karatun ƙira'ar kur'ani da Asim, lokuta da dama ya bijiro da ƙira'arsa kan Asim, tare da yaɗa wannan ƙira'a a garuruwan muslunci daga jumlarsu bagdad da makka.[30] ba'arin masana ƙira'a sun tafi kan ra'ayin cewa tsakankanin almajiran Asim da marawaita daga gare shi Hafsu ya fi dukkaninsu ilimin sanin ƙira'a.[31] bisa rahotannin galibin masana ilimin rijal, an bayyana cewa Hafsu siƙa ne amintacce mutum cikin kiyaye ƙira'ar Asim da tantancewa da dandaƙewa.[32]

Bambanci Tsakanin ƙira'ar Hafsu Da ƙira'ar Asim

Ana cewa a wuri guda ɗaya rak ƙira'ar Hafsu ta saɓa da ƙira'a Asim, wannan saɓani ya kasance cikin karatun kalmar «ضعف‌» cikin aya ta 54 suratul rum wace shi Asim yake karanta «ض‌» da wasalin fataha shi kuma Hafsu yana masa rufu'a.[33] daidai lokacin akwai saɓani a wurare kusan 500 cikin wasalin haruffa tsakanin ƙira'ar Hafsu da ta Abubakar ɗan Ayyash wanda shi ma ya koyi ƙira'a daga Asim kuma ya bijiro da ita kansa.[34] game da sababin saɓani ƙira'ar Hafsu da ta Abubakar ɗan Ayyash an ce ƙira'ar da Asim ya koyar da Abubakar ɗan Ayyash ƙira'ar da ya koyo daga Zar ɗan Habishu shi kuma ya karɓo daga Abdullahi ɗan Mas'ud.[35]

Hususiyoyi

Ba'arin hususiyoyi da asalan da ƙira'ar Asim tare da riwayar Hafsu ta keɓantu da su, sun kasance cikin wannan bayani da zai zo a ƙasa:

  • Asim ya kasance yana tilawar bismilla tsakanin suroru biyu, ma'ana ƙarshe da farko kowacce da farkon sura da ta biyo bayanta; in banda tsakanin da yake suratul anfal da suratul tauba.[36] ƙira'arsa cikin waɗannan wurare an naƙalto ta da tsari guda uku: waƙfu, waslu da saktu (gajeren dagatawa tsakanin kalmomi).[37]
  • A cikin ko'ina a kur'ani, daidai da riwayar Hafsu daga ƙira'ar Asim, a wurare guda huɗu ne kaɗai aka rawaito saktu, waɗannan wurare su ne: tsakanin kalma ta ƙarshe daga aya ta farko cikin suratul kahafi watau kalmar (عِوَجا) da kalmar ta farko a ayar da ta biyo bayanta (قَیماً) cikin wannan sura, tsakanin kalmar «مَرقَدِنا» da kalmar «هذا» cikin aya ta 52 suratul yasin, tsakanin kalmar «مَنْ» da kalmar «رَاقٍ» cikin aya ta 27 suratul ƙiyama da tsakanin kalmar «بَلْ» da kalmar «رَانَ» daga aya ta 14 suratul muɗaffifin.[38][Tsokaci 1]
  • Cikin ƙira'ar Asim, wuri guda ɗaya ne kawai aka yi imala, sannan ya kasance daga imalar harafin «راء» cikin «مَجْراها» daga aya ta 41 suratul hud wace ake karanta ta da tsarin kasra.[39]
  • Bakiɗayan haruffan alhamza a cikin kur'ani ana karanta su da ƙira'ar Asim tare da abin da ake kira da suna (Tahƙiƙ) a tajwidi.[40]

(Tahƙiƙul alhamza) cikin ilimin tajwidi da ma'anar furta harafin alhamza a mafitarsa tare da kiyaye siffofinsa.[41] kalmomi biyu ne kaɗai aka cire daga wannan ƙa'ida su ne «کُفُواً» و «هُزُو اً .[42] cikin kalmar «ءأعجَمیٌ» daga aya ta 44 suratul fussilat ana sauƙaƙe karanta harafin alhamza ta biyu cikin kalmar, ma'ana ana sassauta ta cikin karanta ta da sautin tsakanin alhamza da alifun.[43]

  • An siffanta salon ƙira'ar Asim da tartili sannu-sannu haɗe da tsarin salon waƙe.[44]

Nazari

Ba'arin rubuce-rubuce da aka yi game da ƙira'ar Hafsu:

  • Ahammiyat ƙira'at Asim ba riwayat Hafsu, rubutun Akram Khodayi Isfahani: ya ƙunshi fasali 11 an gabatar da Asim da ƙira'arsa, ya kuma yi bayani dangane da ma'abota ƙira'o'i da suke rawaita daga Asim misalin Hafsu da Abubakar ɗan Ayyash. A fasali na 10 ya yi ƙiyasi tsakanin riwayar Hafsu da ta Abubakar ɗan Ayyash.[45] fasali na 11 fasali da ya keɓanci saɓanin ƙira'ar Asim da sauran ƙira'o'i.[46]
  • Mabahisu fi ilmil al-ƙira'at ma'a bayan usuli riwayat Hafsu, na Muhammad ɗan Abbas baz: marubucin littafin da farko ya fara da gabatar da Asim da Hafsu tare da yin bayani kan sanadin riwayar Hafsu daga ƙira'ar Asim, bayan nan kuma ya yi bincike kan hususiyoyi da asalan ƙira'ar.[47]
  • Al-ƙima Ad-dalaliyya li ƙira'ati Asim bi riwayati Hafsu, na Muhammad Isma'il Muhammad Al-mashhadani: cikin wannan littafi an yi nazari da bincike kan ƙira'ar Asim da riwayar Hafsu daga fuskacin caccanjawar shakali da ginin ba'arin kalmomi da canjawarsu take tasiri cikin canjawar ma'anarsu. Marubucin tare da la'akari da ma'ana ta lugga, siyaƙi ayoyin kur'ani da ba'arin shaidu ya rinjayar da abin da ya zo daga ƙira'ar Asim tare da riwayar Hafsu kan sauran ƙira'o'i.[48] wannan littafi an tsara shi cikin muƙaddima guda ɗaya da khatima.[49]

Bayanin kula

  1. Dhahabi, Marafah al-Qurra al-Kibbar, 1417 AH, shafi na 53; Ma'araf, Talmahid fi Ulum al-Qur'an, 1428 AH, juzu'i na 2, shafi na 195.
  2. Marfat, Talmhid fi Ulum al-Qur'an, 1428 AH, juzu'i na 2, shafi na 246; Baz, Mabahisu fi ulum Al-qira'at ma'a bayan usul riwayati Hafsu, 1425H, shafi na 81.
  3. Ismail Mohammad Al-Mashhadani, Al-Qaima al-Dalaliya qira'ati Asim bi riwayati Hafs, 1430H, shafi na 26.
  4. Jam'i az Nawisandegan Farhannameh na ilimomin Kur’ani, 1394 AH, shafi 794.
  5. Shatibi, Matane Shatibiyyah, 1431 BC, shafi na 3.
  6. Ibn Jazari, Al-Nashr fi Al-Qira’at, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, juzu’i na 1, shafi na 156; Baz, Mabahis fi ilmi Qira’atma'a Bayan usul Ruwayat Hafsu, 1425H, shafi na 85.
  7. Dhahabi, Marifati Al-qurra Al-kibar, 1417 AH, shafi na 54; Ma’rifat, Tamhid fi ulumi Alqur’an, 1428 AH, juzu’i na 2, shafi na 248; Baz,Mabahisu fi ilmi Qira’at ma'aa Bayan usul Ruwayat Hafsu, 1425H, shafi na 85.
  8. Ma’rifat, Tamhid fi ulumi Alqur’an, 1428 AH, juzu’i na 2, shafi na 246; Baz, Mabahisu fi Ilimi Qira’at ma'a Bayan usul Ruwayat Hafsu, 1425H, shafi na 84-85.
  9. Ma’rifat, ulumin Alqur’an, 1381H, shafi na 235.
  10. Ibn Nadim, Al-Fahrist, 1417 BC, shafi na 47.
  11. Ma’rifat, At-tamhid fi ulumi Alqur’an, 1428 BC, juzu’i na 2, shafi na 246.
  12. Dhahabi, Ma’rifat al-Qurra’ah al-Kibar, 1417 BC, juzu’i na 1, shafi na 27; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 43; Ibn Jazari, Ghāt al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 413; Ma’rifat, Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 189.
  13. Dhahabi,Marifati Al-qurra Al-kibar, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 27.
  14. Dhahabi,Marifati Al-qurra Al-kibar, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 27.
  15. Ibn Jazari, Ghāyat al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurāt, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 413.
  16. Ma’rifat,At-tamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 189.
  17. , Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al-Abi Talib, 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 43; Dabaa, Al-Idha fi Bayan Usul Al-Qira’ah, 1420 AH, shafi 72; Jamal, Al-Mughni fi Ilm Tajweed, Hafs ya ruwaito daga Asim, Laburaren Samir Mansour, shafi na 46.
  18. Muflih al-Qudah wa Digaran, Mukaddimat fi ilmi Qira’at, 1422 AH, shafi na 63; Jamal, Al-Mughni fi Ilm Tajweed, Hafs ya ruwaito daga Al-Asim, Laburaren Samir Mansour, shafi na 32.
  19. Dabaa, Al-Idha fi Bayan Usul Al-Qira’ah, 1420 AH, shafi na 72.
  20. Ma’rifat, Attamhid fi Ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 189.
  21. Dhahabi, Ma’rifat al-Qurra’ah al-Kibar, 1417 BC, juzu’i na 1, shafi na 30; Ibn Jazari, Ghayat al-Nihayah fi Tabaqat al-Qurari, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 414.
  22. Ibn Nadim, Al-Fahrist, 1417 BC, shafi na 47.
  23. Ma’rifat,Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 190.
  24. Ibn Mujahid,As-sab'atu fi Al-qira'at, 1400H, shafi na 70.
  25. Ma’rifat,Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 190.
  26. Ibn Jazari, Ghayat al-Nihayah fi Tabaqat al-Qari’, 1351 BC, juzu’i na 1, shafi na 346; Khoi, Kamus na Rijal al-Hadith, Imam al-Khoei Islamic Foundation, juzu'i na 10, shafi na 195.
  27. zahabi, Mizan al-I'tidal, 1382 Q, juzu'i na 2, shafi na 357-358; Dhahabi, Siyar A`lam al-Nubala’, 1427 BC, juzu'i na 1, shafi 153; Ibn Jazari, Al-Nashr fi Al-Qira’at Al-Ashr, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, juzu’i na 1, shafi na 155; Al-Dani, Jami’ al-Bayan fi al-Qira’at al-Saba’, 1428 AH, juzu’i na 1, shafi 196; Khwansari, Rawdat al-Janat, 1390 AH, juzu'i na 5, shafi na 4.
  28. Dhahabi,Marifati Al-qurra Al-kibar alaTabaqat wa Al-Asar, 1417 BC, juzu'i na 1, shafi na 52; Ibn Jazari, Ghāt al-Nihayah fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 347; Ibn Jazari, Al-Nashr fi Al-Qira’at Al-Ashr, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, juzu’i na 1, shafi na 155; Al-Dani, Jami’ al-Bayan fi al-Saba’ al-Qira’at, 1428 AH, juzu’i na 1, shafi 195; Khwansari, Rawdat al-Janat, 1390 AH, juzu'i na 5, shafi na 4.
  29. Marifat, Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428 AH, juzu’i na 2, shafi na 246; Ibn Jazari, Al-Nashr fi Al-Qira’at Al-Ashr, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, juzu’i na 1, shafi na 155.
  30. Ibn Jazari, Ghāyat al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 254; Ma’rifat, Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 248.
  31. Ibn Jazari, Ghāyat al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 254; Ibn Jazari, Al-Nashr fi Al-Qira’at Al-Ashr, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, juzu’i na 1, shafi na 156; Ma’rifat,Attamhid fi ulumi Alqur’an, 1428H, juzu’i na 2, shafi na 248.
  32. Marafat, Attamhid fi ulumi Alqur'an,a 1428 AH, juzu'i na 2, shafi na 248; Dhahabi, Mizan al-Itidal, 1382 BC, juzu'i na 1, shafi na 558; Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 BC, juzu'i na 9, shafi na 64.
  33. Ibn Mujahid, Al-Saba’ fi Al-Qira’at, 1400 BC, shafi na 96.
  34. Ibn Jazari, Ghāyat al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 254. ↑
  35. Ibn Jazari, Ghāyat al-Nihaya fi Tabaqat al-Qurātī, 1351 BC, juzu'i na 1, shafi na 254. ↑
  36. Baz, Mabahisu fi Ilmi Qira’atma'a Bayan Usul Ruwayati Hafsu, 1425H, shafi na 86.
  37. Juma Az-Naysandegan, Farhangnameh ulumi Kur’ani, 1394 AH, shafi 795.
  38. Baz, Mabahisu fi ulumi Al-Qira’at ma'a Bayan Usul Ruwayati Hafsu, 1425H, shafi na 88.
  39. Baz, Mabahisu fi ulumi Al-Qira’at ma'a Bayan Usul Ruwayati Hafsu, 1425H, shafi na 88.
  40. Juma Az-Naysandegan, Farhangnameh ulumi Kur’ani, 1394 AH, shafi 795.
  41. Studhnia, Danish Tajweed (Satahu 2), 1396 AH, shafi na 149.
  42. Juma Az-Naysandegan, Farhangnameh Ulum Kur’ani, 1394 AH, shafi 795.
  43. Dabaa, Al-Idha fi Bayan Usul Al-Qira’ah, 1420 AH, shafi na 74; Mursafi, Hidayat Al-Qari li Tajweed kalam Al-Bari’s, Taiba Library, juzu’i na 2, shafi na 579.
  44. Juma Az-Naysandegan, Farhangnameh Ulum Kur’ani, 1394 AH, shafi 795.
  45. Khodaei Isfahani, Muhimmancin Qara’at Asim beh ruwayat Hafs, 1378H, shafi na 115.
  46. Khodaei Isfahani, Muhimmancin Qara’at Asim beh ruwayat Hafs, 1378H, shafi na 115.
  47. Baz, Mabahisu fi ilmi Qira’atma'a Bayan Usul Riwayat Hafsi, 1425H, shafi na 14-15.
  48. Ismail Muhammad, Al-qima Ad-dalaliya liqir'ati Asim bi Ruwayat Hafsi, 1430H, shafi na 19.
  49. Ismail Muhammad, Al-qima Ad-dalaliya liqir'ati Asim bi Ruwayat Hafsi, 1430H, shafi na 7-9

Tsokaci

  1. Saktu:Takaitaccen ɗan dakatawa tsakanin kalmomi ya zama dole idan an yi kuskuren fahimtar ma'anar jimlar ta haɗa kalmomi biyu tare. (Jam'i az nawisendigan, Kamus na Ilmin Alqur'ani, 1394, shafi na 587). A aya ta 14 a cikin suratul Mutafeen, misali «بَلْ رَانَ عَلَی قُلُوبِهم مَّا کَانوا یَکْسَبون. harafinn sukuni ne kuma wajibi cikin harafin «راء» ayi idgaminsa. Amma a nan idan tsakanin kalmomin,«بلْ» و «رَانَ» babu saktu kalmomin biytu za yi idgaminsu da juna za a canja su zuwa kalmar «بَرّانَ» kuma za su canja ma'anar ayar (Ruhani Isfahani, Tajweed Alqur’ani wa ikhtilaf Qira’at dar nazme Shatibiyah, 1396H, shafi na 43).

Nassoshi

  • Ibn Shahr Ashub, Muhammad bin Ali, Manaqib Ale Abi Talib, Qum, Wallafar Alama, babi na farko, 1379H.
  • Ibn Mujahid, Ahmed bin Musa, As-sab'atu fi Al-qira'at, Masar, Dar Al-Ma'arif, Babin Dom, 1400H.
  • Ibn Nadim, Abu al-Faraj Muhammad bin Ishaq, Al-Fahrist, Beirut, Dar Al-Ma’rifa, 1417 BC.
  • Ibn Jazari, Muhammad bin Muhammad, An-nahsaru fil Al-Qira’at Goma, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, Beta.
  • Ibn Jazari, Muhammad bin Muhammad, Ghayat al-Nihayya fiTAbaqat Al-qurra, Bija, Library Ibn Taimiyyah, 1351 BC.
  • Ismail Muhammad Al-Mashhadani, Muhammad, Al-Qaima al-Dalaliya li qira'ati Asim bi riwayati Hafs,iraq Cibiyar Bincike da Ilimin Musulunci, bugu na farko, 1430H.
  • Al-Dani, Othman bin Saeed, Al-Bayan Jami al-Qarayat al-Saba, Emirates, Jami'ar Sharjah, 1428 AH.
  • Baz, Muhammad bin Abbas, Mabahisu fi ilmi Al-qira'at ma'a bayan Usul riwayat Hafsu, Masar, Darul Kalama, 1425 Hijira.
  • Jam'i az nawisendigan, Farhangnameh ulumi qur'ani, Qom, Cibiyar Bincike ta Al'adun Musulunci da Kimiyya, 1394.
  • Jamal, Abdul Rahman Youssef, al-Mughni Fi Alam Tajwid bi riwayati Hafs an al-Asim, Gaza, School of Samir Mansour, Beta.i
  • Khodaei Isfahani, Akram, Ahammiyat Qira’at Asim beh ruwayat Hafs, Tehran, bugun Raizen, 1378H.
  • Mai wa'azin Baghdadi, Ahmed bin Ali, Tarikh Baghdad, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, 1417 BC.
  • Khansari, Muhammad Baqir, Rawdat al-Janat, Qum, Ismailian Publications, 1390 AH.
  • Khoei, Sayyid Abu al-Qasim, Kamus Rijal al-Hadith, Najaf, Imam al-Khoei Islamic Foundation, Beta.
  • Dhahabi, Shams al-Din Abu Abdullah, siyaru Alam al-Nubala', Bija, Al-Risala Foundation, 1405 BC.
  • Dhahabi, Shams al-Din Abu Abdullah, Marifat Al-qurra Al-kibar ala Tabaqat wal al-Asar, Beirut, Darul Kutub al-Ilmiyya, 1417 BC.
  • Dhahabi, Shams al-Din Abu Abdullah, Mizan al-Itidal, Beirut, Dar al-Ma’rifa for Printing and Publishing, babi na farko, 1382 BC.
  • Rohani Isfahani, Seydahashim, Tajweed Alqur'ani wa Ikhtilafu dar nazme Shatibiya, Tehran, Aswa Publications, 1396H.
  • Stoudhania, Muhammad Reza, Danish Tajweed (Sathu 2), Qom, Dar Al-Ilm Publications, 1396 A.H.
  • Shatibi, Abu Muhammad Qasim bin Firah, Matne al-Shatibiyyah, Madina, Library Dar al-Huda, 1431 BC.
  • Dabaa, Muhammad Ali, Al-Idha fi Bayan Usul Al-Qira’ah, Alkahira, Al-Azhari Heritage Library, 1420 BC.
  • Marsafi, Abdel Fattah, Hidayat Al-Qari ila Tajweed Kalam Al-Bari, Madina, Thebes Library, Chap Dom, Beta.
  • Marifat, Muhammad Hadi, Attamhid fi ulum Alqur'an, Qom, Farhangi Publications Foundation, Gabatarwa, 1428 A.H.
  • Maarifat, Muhammad Hadi,Ulum Alqur'ani, Qom, Farhangi Publications Foundation, Gabatarwa, Babin Chaharam, 1381 AH.
  • Muflih al-Qudah, Ahmed Muhammad wa Dijran, Mukaddimat fi ilmi Al-Qira’at, Amman, Dar Ammar, 1422 BC.