Ɗawasin
Ɗawasin (Larabci: الطواسين) suna ne na surorin shu'ara da ƙasas da farkonsu ya fara da "Ɗasinmim" da suratul namli tare da "Ɗasin'nun"[1] Game da falalar karatun ɗawasin, Shaik Saduƙ cikin littafin Sawabul A'amal ya naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta ɗawasin a daren juma'a, zai kasance daga waliyyan Allah, kuma zai kasance ƙarƙashin inuwar luɗufi da kariyar ubangiji, ba zai taɓa fuskantar wahala a duniya kuma ranar lahira za a bashi aljanna domin ya yarda, bari dai Allah zai bashi hurul ini guda ɗari ya yi aure da su.[2] Wasu riwayoyi daga Imam Sadiƙ (A.S) yana cewa duk wanda ya karanta ɗawasin, Allah zai sanya shi a Aljannar tare da Annabawa, manzanni, da magadansu.[3] Haka nan a cewar Allama Hilli mustahabbi ne karanta ɗawasin, musammam a daren juma'a.[4]
Bayanin kula
Nassoshi
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Tazkira Al-F
- Hawizi, Abd Ali bin Juma, Nor al-Saqlain, bugun Hashim Rasouli, Qum, Ismaili, bugu na hudu, 1415H.
- Hurru Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il al-Shi'a, Qum, Al-Bait Institute, 1414H.
- Ramyar, Mahmoud, Tarikh Qur'ani, Tehran, Amir Kabir Publications, 2018.
- fuqaha, Qum, Al-Bait Institute, 1414H.