wikishia:Featured articles/2025

Shahadar Sayyida Faɗima (S), yana daga cikin daɗaɗɗiyar aƙidar ƴanShi'a, kamar yadda ƴanShi'a suka yi imani cewa Fatima ƴar Annabi Muhammad (S.A.W), ba ta mutu haka kawai ba, mutuwa ta ɗabi'a, a a ta yi shahada ne sakamakon abin da wasu daga cikin sahabban Manzon Allah suka yi mata, kuma babban sanadin shahadarta shi ne Umar ɗan Khaɗɗabi. Asalin sabani tsakanin Ahlus-Sunna da Shi'a dangane da sha'anin shahadarta ya samo asali ne tun lokacin gajeriyar rayuwar da ta yi bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w). Rigingimun da suka biyo bayan wafatin Annabi da abubuwan da suka faru a shekara ta 11 bayan hijira, inda aka samu saɓani dangane da ranar shahadarta bayan wafatin Annabi. Da kuma cewa ta rasu ne a matsayin shahada bayan an karya haƙarƙarinta kuma ta yi ɓarin ciki ya zube saboda dukan da halifa Umar ya yi mata, kamar yadda mafi yawan ƴanShi'a suka yi imani da shi, kuma a fili yake cewa ta rasu ne sakamakon rashin lafiya da baƙin ciki da damuwa da suka same ta a sanadiyyar rasuwar Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda Ahlus-Sunna suka yi imani.
Other featured articles: Hayyu ala Kairil Amal – Niyaba Amma – Hadis Wilaya