Zulaikha

Daga wikishia

Zulaikha (Larabci: زليخا) matar Sarkin Misra wacce ƙissar tare da Hazrat Yusuf ta zo a cikin Alkur’ani. Sunan Zulaikha bai zo cikin Alkur’ani ba, [1] kaɗai an yi ishara kanta cikin Kalmar (wacce yake cikin gidanta) [2] ma’ana Yusuf yana zaune a gidanta, da kuma (matar Aziz Misra) [3] tare da haka [4]ba’arin litattafan tafsiri, [5] da tarihi [6] da hadisi, [7] sun bayyana cewa sunanta Zulaikha, Fakhrur Razi Malamin tafsiri ya tafi kan cewa babu wata ingantacciyar madogara kan wannan suna da aka bata, [8] cikin ba’arin wasu masadir nan ma an kawo cewa Zulaikha shi ne sunan matar Aziz Misra. [9] Wasu ɓangarori daga Alkur’ani da At-Taura an yi bayani ƙissar Yusuf da Zulaikha, [10] a cewar masu bincike da nazari, akwai bambanci cikin rahotannin Alkur’ani da na At-Taura, [11] a rahotan Alkur’ani, Zulaikha ce ta nemi Yusuf da lalata amma bayan Yusuf ya ga dalilin Ubangijinsa sai ya gudu ya nufi ƙofa, [12] Nasir Makarim Shirazi daga Malaman tafsirin Shi’a ya tafi kan cewa Hazrat Yusuf tare da taimakon na gaibu ya samu kuɓuta daga saɓo, [13] sai dai cewa Zulaikha ta kai kanta ga Yusuf ta bi bayansa a guje har ta kai ga ta yaga masa riga daga baya, [14] sai kwatsam Yusuf ya yi kaciɓus da Aziz Misra a baƙin ƙofa, [15] Zulaikha da Yusuf kowanne ɗayansu ya tuhumi ɗaya da ha’ainci, [16] a wannan lokacin sai aka samu wani mutum daga dangin Zulaikha ya bada shaida cewa idan rigar Yusuf ta yage ne daga bayansa to Yusuf ne mai gaskiya, [17] da wannan dalili aka wanke Yusuf daga tuhumar ha’inci. [18] Kan asasin ba’arin rahotanni, wannan mutumi da ya bada shaida kan Yusuf ya kasance jaririn wata uku da haihuwa kuma ɗa ne ga ƴar ɗan’uwan Zulaikha, [19] wanda cikin ikon Allah bakinsa ya buɗe ya yi Magana, [20] tare da haka, cikin wasu rahotannin daban an bayyana cewa wanda ya bada shaida ya kasance wani mutum ma’abocin hikima, [21] a cewar ba’arin Malaman tafsiri, Zulaikha ta sa an jefa Yusuf a Kurkuku, [22] sai dai cewa bayan wani lokaci da kanta ta bayyana cewa Yusuf shi ne mai gaskiya. [23] Zulaikha ta kasance kyakkyawar mace mai dukiya, [24] mai bautar gumaka, [25] bata samu haihuwa daga mijinta ba, [26] kan asasin ba’arin masadir an bayyana cewa Zulaikha bayan ta tsufa ta tuba daga bautar gumaka ta rungumi addinin Yusuf da kaɗaita Allah, sannan tare da addu’ar Yusuf (A.S) ta dawo matashiya ya kuma aureta, [27] an ce bayan sun yi aure sun haifi ƴaƴa biyu [28] amma wasu ba’arin masu bincike sun bayyana cewa wannan riwaya sakamakon dalilai mabambanta misalin matsalar da aka samu a sanadinta da mataninta ba za a iya dogara da ita ba, sannan an ciro abin da yake cikinta ne daga At-Taura. [29] Kan asasin bincike da aka yi, Zulaikha ta yi matuƙar tasirantuwa da tunanin Sufanci, [30] An ce Sufaye sun yaba da yanayin Zulaikha sosai tare da bayyana ra’ayoyinsu na sufanci ta hanyar ishara da yanayinta. [31] Labarin soyayyar Zulaikha ga Hazrat Yusuf (A.S) ya yaɗu tare da tasirin sosan gaske cikin Adabin duniya, daga jumlarsu Adabin Farisanci, Turkanci da ƙasashen Turai, [32]

Bayanin kula

  1. Asadi, “Zulaikha”, shafi na 416.
  2. Suratul Yusuf, aya ta 23.
  3. Suratul Yusuf, aya ta 30.
  4. Asadi, “Zulaikha”, shafi na 414.
  5. Misali, duba Muƙatil, Tafsirin Muƙatil bin Sulaiman, 1423H, juzu’i na 2, shafi:327; ƙommi, Tafsir ƙummi, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 357; Tabarsi, Majma Al--Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 340.
  6. Misali, dubi Maƙdisi,Albada'u wa al-Tarikh, Maktabatr Al-Thaƙafah al-Diniyah, juzu'i na 3, shafi:68; Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408 AH, juzu'i na 2, shafi na 45; Ibn Jowzi, al-Muntazem, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 315.
  7. Misali, duba Sheikh Sadouƙ, Ilalul Al-Shara’i, 1385, juzu’i na 1, shafi na 55; Khazaz Razi, Kefaya Al-Athar, 1401 AH, shafi na 264; Rawandi, ƙasas Al-Anbiya, 1409 AH, shafi na 136.
  8. Fakhr Razi, Mufatih Al-Ghaib, 1420H, juzu'i na 18, shafi na 435.
  9. Dilmi, Elamul Al-Din, 1408H, shafi na 429.
  10. Misali, Suratu Yusuf, aya ta 23-32; Attaura, Sefer Fedayesh, Babi na 39, Ayoyi 7-20.
  11. Sadeghi, “Negahi beh Dastane Yusuf wa Zuleikha dar Alƙur’an wa Attaura”, 101-103.
  12. Suratu Yusuf, aya ta 23-25.
  13. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 9, shafi na 374.
  14. Suratul Yusuf, aya ta 25.
  15. Suratul Yusuf, aya ta 25.
  16. Suratul Yusuf, aya ta 25-26
  17. Suratul Yusuf, aya ta 26-27
  18. Suratul Yusuf, aya ta 28-29
  19. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 347.
  20. ƙommi, Tafsir ƙummi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 343.
  21. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 347.
  22. Ɗabarasi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi.354; Beidawi, Anwar Al-Tanzil, 1418 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 163.
  23. Suratul Yusuf, aya ta:51.
  24. ƙommi, Tafsir ƙummi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 357.
  25. Sheikh Sadouƙ, Ayoun Akhbar al-Reza, (A.S), 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 45.
  26. Kashani, Tafsiri Manhaj al-Sadiƙin fi Zaam al-Makhalifin, 1336, juzu'i na 5, shafi na 28.
  27. Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 52.
  28. ƙortubi, Al-Jame Al-Ahkam Al-ƙur'an, 1364, juzu'i na 9, shafi na 214.
  29. Ma’arif waDigaran, “barasi riwayat tafsiri fariƙaini dar mas'aleh izdiwaji Hazrat Yusuf wa Zuleekha”, shafi na 26.
  30. Pakmehr, "Zulikha dar Andishe Sha'iran wa Arifan ƙarne Panjom ta Haftom", shafi na 149.
  31. Pakmehr, "Zulikha dar Andishe Sha'iran wa Arifan ƙarne Panjom ta Haftom", shafi na 149.
  32. Khosravi, “Fajuhsehi Dastane Yusuf wa Zulaikha dar Adabiyat Islami” shafi na 71.

Nassoshi

  • Ibn Jozi, Abd al-Rahman bin Ali, al-Muntazem fi Tarikh al-Umm da al-Muluk, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1412 AH.
  • Ibn Khaldun, Abd al-Rahman bin Muhammad, Tarikh Ibn Khaldun, Beirut, Darul Fikr, 1408H.
  • Asadi, Ali, “Zulikha”, daR Dayiratul Almarif ƙur\ani Kareem , juzu’i na 14, ƙum, Bostan Kitab, 1395.
  • Baidawi, Abdullah bin Omar, Anwar al-Tanzil da Asrar al-Tawil, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1418H.
  • پاکمهر، علی، «زلیخا در اندیشه شاعران و عارفان قرن پنجم تا هفتم»، در فصلنامه تخصصی ادبیات فارسی (دانشگاه آزاد مشهد)، شماره ۴۶، پاییز ۱۳۹۴ش.
  • خزاز رازی، علی بن محمد، کفایة الاثر فی النص علی الائمة الاثنی‌عشر، قم، بیدار، ۱۴۰۱ق.
  • خسروی، زهرا، «پژوهش تطبیقی داستان یوسف و زلیخا در ادبیات اسلامی»، در مجله دانشنامه (واحد علوم و تحقیقات)، شماره ۲، ۱۳۸۸ش.
  • دیلمی، حسن بن محمد، اعلام الدین فی صفات المؤمنین، قم، مؤسسة آل‌البیت(ع) لاِحیاء التراث، ۱۴۰۸ق.
  • Daylami, Hasan bin Muhammad, Elamul Al-Din Fi Sifat Al-Mu'minin, ƙum, Al-Bait (A.S.) Foundation, 1408 AH.
  • Ravandi, ƙutbuddin Saeed bin Hebatullah, ƙasses al-Anbiya (a.s.), Mashhad, Islamic Research Center, 1409 AH.
  • Saadi, Mosleh bin Abdullah, Bostan Saadi, Mohammed Ali Foroughi ya gyara, Tehran, Phoenix, 1372.
  • Saadi, Mosleh bin Abdullah, Ghazliat Saadi, editan Muhammad Ali Foroughi, Tehran, Iƙbal, 1342.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), Mehdi Lajurdi, Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378 Hijira, ya yi bincike kuma ya gyara shi.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ilalul Shara'i, Kum, Davari, 2005.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, 1420H.
  • Faiz Kashani, Mhilamasan, Tafsir al-Safi, bincike na Hossein Alami, Sadr Publishing House, Tehran, bugu na biyu, 1415H.
  • ƙortubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamei Ahkam Al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosrow, 1364.
  • ƙommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsir al-ƙummi, malami, mai gyara, Musawi Jazaeri, Seyyed Tayyeb, Darul Katab, ƙum, bugu na uku, 1404H.
  • Kashani, Mulla Fethullah, Tafsir Manhaj al-Sadeghin fi Zazam al-Makhalifin, Mohammad Hasan Elmi kantin sayar da littattafai, Tehran, 1336.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir namuneh, Dar al-Katb al-Islamiya, Tehran, 1374.Muƙatil, Ibn Suleiman, Tafsir Muƙatil bin Suleiman, Beirut, Dar Ihya al-Trath, 1423H.
  • Moghadsi, Motaher bin Taher, Albada'u wa al-Tarikh, Bija, Al-Taƙaba Al-Diniyeh School, Bita.