Ummu Dawud

Daga wikishia

Ummu Dawud,(Larabaci:أم داوود) matar Hassan musanna babar Imam Sadiƙ (A.S) cikin shayarwa, ta samu wannan alkunya ta Ummu Dawud ne daga sunan ɗanta da ake kira Dawud ɗan Hassan, sunanta Habiba, ayyukan ibada da ya zo da sunan A'amal Ummu Dawud da Du'a'u Istifta (Du'a'u Ummu Dawud) ta naƙalto su ne daga Imam Sadiƙ (A.S). Ummu Dawud ta koyi waɗannan ayyukan ibada da addu'a ne domin roƙon Allah ya fitoi da ɗanta daga kurkuku, a cewarta bayan yin wannan ayyukan ibada da addu'a haƙiƙa an samu nasara an sako mata ɗanta daga kurkuku ya dawo gida.

Suna da Alkunya

Habiba, amma akwai waɗanda suke ganin cewa sunanta Fatima, ta shahara da Ummu Dawud ɗiyar Abdullahi ɗan Ibrahim kuma matar Hassan musanna.[1] ta samu wannan alkunya ne daga sunan ɗanta Dawud ɗan Hassan.[2] cikin littafin A'ayanul shi'a an kawo cewa ana mata alkunya da Ummu Khalid.[3] Ummu Dawud itace ta shayar da Imam Sadiƙ (A.S),[4] haka nan ɗanta Dawud ya kasance cikin sahabban Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S).[5]

Ayyukan Ibada da Du'a'u Ummu Dawud

Tushen ƙasida: A'amal Ummu Dawud da Du'a'u Ummu Dawud

Cikin madogaran riwaya, akwai wani hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) a cikinsa ya umarci Ummu Dawud ta yi wasu ayyukan ibada a fararen ranaku (Ranakun 13.14.15 ga watan Rajab), waɗannan ayyuka sun shahara da sunan A'amal Ummu Dawud, haka nan an naƙalto addu'a da sunan du'a'u istiftah ko du'a'u Ummu Dawud, waɗanda a ƙarshe ana kiransu da ayyukan ummu dawud.[6]marawaicin wannan hadisi ba wani bane sai ita kanta ummu dawud ɗin.[7] Du'a'u ummu dawud ta zo cikin littafin fada'ilu shahri rajab na Hakim hasakani daga malaman ahlus-sunna ƙarni na biyar bayan hijira.[8]

Addu'ar ummu dawud ana yinta cikin wannan tsari kamar haka ana farawa da ɗaukar azumi a ranar farko cikin fararen ranaku (Ranakun 13.14.15 ga watan Rajab), a rana ta 15 ga rajab sai a yi wanka daidai lokacin zawalin rana, bayan yin sallar azuhur da la'asar za a karanta wasu surorin kur'ani, daga ƙarshe sai a karanta du'a'u ummu dawud ko istiftahi.[9] malaman shi'a misalin shaik ɗusi, sayyid ibn ɗawus da allama majlisi, suna cewa haƙiƙa du'a'u ummu dawud wata addu'a mai tasiri cikin kawar musibu da samun biyan buƙata.[10]

labarin A'amal Ummu Dawud

labarin A'amal ummu ya zo daga Imam Sadiƙ (A.S) da zirin ƙissa mai faɗin gaske cikin littafan fada'ilu ash'huril salasa na shaik saduƙ da kuma iƙbalul a'amal na sayyid ibn ɗawus.[11] a rahotan waɗanann littafai biyu, dawud ɗan ummu dawud an jefa shi a kurkuku a zaman halifancin mansur dawaniƙi, bayan aka ɗauke aka kaishi ƙasar iraƙi, tsawon lokaci mahaifiyarsa bata samu labarinsa ba, ta yi addu'a mai yawan domin fitowar ɗanta, amma shiru babu wani canji da ta gani babu labarinsa, ta yi tawassali da ma'abota ibada, amma tare da addu'o'insu na su matsakar ta dai bata warware ba.[12] har ta kai ga ta fara cire sa rai da ƙara ganin ɗanta.[13]

wata rana sai ta je duba Imam Sadiƙ (A.S) a wata rashin lafiya da ya yi, sai ya tambayeta game da ɗanta dawud, sai ummu dawud ta gaya masa abin da yake faruwa, Imam Sadiƙ (A.S) ya ce mata me yasa baki karanta du'a'u istiftahi ba? Saia ya nemi da ta ɗauki azumi a fararen ranaku sannan a rana ta ƙarshe watau 15 ga watan rajab ta yi a'amal ummu dawud tare da karanta wannan addu'a.[14] a cewar ummu dawud, bayan ta yi wannan ayyuka sai ta yi mafarki da Annabi (s.a.w) ya yi mata busharar fitowar ya ce mata bayan wani lokaci zai dawo gida, kamar yadda ta faɗa a wannan dare ne kuwa dawud ya dawo gida.[15]

Bayanin kula

  1. Amin, A'yan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 3, shafi 476.
  2. Amin, A'yan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 3, shafi 476.
  3. Amin, A'yan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 3, shafi 476.
  4. Amin, A'yan al-Shia, 1406 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 368.
  5. Amin, A'yan al-Shia, 1406 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 368.
  6. Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 530-535; Kafami, Balad al-Amin, 1418 AH, 180-183; Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 812-807; Seyed Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 242-248.
  7. Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 530-535; Kafami, Balad al-Amin, 1418 AH, 180-183; Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 812-807; Seyed Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 242-248.
  8. Akbari da Rabi Netaj, “Kaweshi dar Du'aye Ummu Dawood” shafi na 88-91.
  9. Qomi, Mufatih al-Jinan, karkashin "Amaal Um Dawood".
  10. Akbari da Rabi Netaj, “Kaweshi dar Du'aye Ummu Dawud” shafi na 82.
  11. Duba Sadouq, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396 AH, shafi na 33 da 34; Sayyed bin Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 241 da 242.
  12. Duba Sadouq, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396 AH, shafi na 33 da 34; Sayyed bin Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 241 da 242.
  13. Duba Sadouq, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396 AH, shafi na 33 da 34; Sayyed bin Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 241 da 242.
  14. Duba Sadouq, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396 AH, shafi na 33 da 34; Sayyed bin Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 241 da 242.
  15. Duba Sadouq, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396 AH, shafi na 33 da 34; Seyed bin Tavus, Iqbal al-Amal, 1376, juzu'i na 3, shafi na 250 da 251

Nassoshi

  • Amin, Seyyed Mohsen, Ayan-al-Shia, bincike: Hasan al-Amin, Beirut: Dar al-Taarif, 1406 AH.
  • Kafaami, Ibrahim bin Ali Ameli, Al-Balad al-Amin da al-Dara al-Hussein, Beirut: Al-Alami Press Institute, bugu na farko, 1418H.
  • Kafami, Ibrahim bin Ali Ameli, Masbah al-Kafami, Qum: Dar al-Razi, bugu na biyu, 1405H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamiu liduraril Akhbar al-Imath al-Athar, bincike: ƙungiyar masu bincike, Beirut: Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403 H.H.
  • Qomi, Abbas, Mofatih al-Jinan, Kum: Aswah, [Bita].
  • Seyyed Bin Tawoos, Ali Bin Musi, Al-Iqbal al-Amal al-Hasaneh, bincike: Javad Qayyumi Esfahani, Qom: Ofishin farfagandar Musulunci, bugu na farko, 1376.
  • Tousi, Muhammad bn al-Hassan, Misbah al-Mutahjad da Selah al-Mutabbad, Beirut: Institute of Fiqh al-Shia, 1411 A.H.
  • Akbari, Zahra, da Seyyed Ali Akbar Rabienetaj, "Kaweshi duaye Umm Dawood", a cikin Mujallar Safina, Tehran: Cibiyar Al'adun Naba Mobin, No. 36, Fall 2013.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Fada'ilu ash'hur salasa, Bincike da Gyara: Gholamreza Irfanian Yazdi, Qom: kantin sayar da littattafai na Douri, bugun farko, 1396 Hijira.