Tattaunawa:Abdullahi Ɗan Abi Hosain Al-Azdi
- A banbance shi da Abdullahi ɗan Abil Husaini Al-azdi Al-bajali.
Abdullahi ɗan Abil Husaini Al-azdi (Larabci: عبد الله بن أبي الحُصين الأَزدي) ya yi wafati a shekara ta 37 hijirar manzon Allah (S.A.W) kuma ya kasance yana daga cikin sahabban Imam Ali (A.S) kuma yana cikin shahidan yaƙin Siffin.. Lokacin da rundunar Imam Ali (A.S) suka isa Raƙƙa, a kan hanyar su ta zuwa Siffin, a lokacin da suke tsallaka wata gada, sai hular Abdullahi ɗan Abi Al-Husain Al-az-di ta faɗo saboda cunkuson dawakai a kan gadar. sai ya sauka ya ɗaukota, sai hular Abdullahi ɗan Hajjaj Al-azdi ta faɗo, sai shi ma ya sauko ya ɗaukota, sannan ya ce wa Abdullahi ɗan Abi Hosain Al-bajali:
"Idan zatan Azzajiri Aɗɗayyar ya kasance gaskiya, kamar yadda suka yi tinani, to za a kashe ni da wuri, kuma kai ma za a kashe ka."
Sai ya ba shi amsa yana mai cewa; ba bu abin da na ke so kamar abin da ka ambata.[2] Abdullahi ɗan Abi Hosain yana daga cikin masu karatun kur'ani, wadanda suka raka Ammar ɗan Yasir zuwa fagen daga, kuma aka kashe shi tare da Ammar[3] Kafin ya tafi fagen daga, Mukhnaf ɗan Salim Al-azdi ya ce ma shi: Mu munfi buƙatar ka fiye da Ammar, amma ya ƙi ya tsaya tare da mu, sai ya raka Ammar aka kashe shi tare da Ammar [4].