Sarjun Bn Mansur Rumi

Daga wikishia

Sarjun bin Mansur Rumi(Larabci:سَرْجُون بن منصور الرومي) (ya rasu a shekara ta 86 bayan hijira) yana ɗaya daga cikin mashawartan Mu'awiya ɗan Abi Sufyan da Yazid ɗan Mu'awiya. A lokacin da Kufawa suka yi mubaya’a ga Muslim ɗan Aƙeel, sai Yazid ya naɗa Ubaidullahi ɗan Ziyad ya yi mulkin Kufa don murƙushe su.

Sarjun ɗan Mansour ɗaya ne daga cikin Kiristocin Sham,[1] kuma bawan Mu’awiya.[2] Ya kasance marubuci a gwamnatin Mu'awiya,[3] kuma mai ba shi shawara kan al'amuran gwamnati.[4] kuma ya kasance mai kula da Akwatin haraji.[5] Bayan wafatin Mu’awiya, sarjun ya taka rawa a gwamnatin Yazid bin Mu’awiya,[6] Wasu suna ganin cewa shi da Akhɗal su kasance Kiristoci.

Suna cikin bayin Yazid a lokacin da yake kan giyar mulki,[7] A lokacin da ‘yan Shi’ar Kufa suka yi mubaya’a ga Muslim bin Aƙil, sai Yazid ya yi shawara da Sarjun, da ra’ayinsa, ya sanya Ibn Ziyad ga gwamnatin Kufa domin ya murƙushe mutanan da sukaiwa yazid tawaye a Kufa.[8] Sarjun ya bawa yazid wata takardar yarjejeniya, wai daga babansa Mu’awiya ya ce: “Muawiyah ya rubuta wannan wasiƙa lokacin da yazo mutuwa, cewa idan anyi tawaye a Kufa, a nada Ubaidullahi ɗan Ziyad a matsayin gwamnan garin.[9]

A zamanin Marwan bin Hakam da ɗansa Abdul--Malik, Sarjun ya kasance marubucinsu, amma Abdul-Malik ya cire shi daga wannan matsayi saboda yana ganin baya bada himma a aikinsa.[10] Wasu sun ce an bashi matsayin marubuci a Baitul Mal a zamanin Abdul-Malik,[11] Ya mutu a shekara ta 86 bayan hijra.[12]

Bayanin kula

  1. Masoudi, al-Tanbih wa al-Ashraf, Dar al-Sawi, shafi na. 265.
  2. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400 AH, juz.5, sahfi na 159, 288; Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1967, juz 5, shafi na356; Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, juz .2, shafi na 42.
  3. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400H, juzu'i na 5, shafi na 159.
  4. Ibn Kathir, Al-Bidayah wa Al-Nihayah, 1986, juzu'i na 8, shafi na 146.
  5. Khalifa bin Khayyat, Tarikh, 1995, shafi na 141; Masoudi, al-Tanbihi wa al-Ashraf, Dar al-Sawi, shafi na 261.
  6. Tabari, Tarikh al-Umm wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 348; Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400H, juzu'i na 5, shafi na 354, 379.
  7. Abolfaraj Esfahani, Al-Aghani, 1415 Hijira, juzu'i na 17, shafi na 4.
  8. Tabari, Tarikh al-Umm wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi.356; Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi.42; Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400 AH, juzu'i na 5, shafi na 379.
  9. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400 AH, juzu'i na 5, shafi na 379; Tabari, Tarikh al-Umm wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 356.
  10. Ibn Abd Rabbah, Al-Iƙdul Al-Farid, 1407H, juzu'i na 4, shafi na 252.
  11. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400 AH, juzu'i na 7, shafi na 222.
  12. Khalifa bin Khayyat, Tarikh, 1995, shafi na 189.

Nassoshi

  • Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Bincike na Ehsan Abbas, Beirut, Jamus Oriental Society, 1400/1400/1979.
  • Ibn Abd Rabbah, Ahmad Ibn Muhammad, al-Iƙd ul al-Farid, bincike: Mufid Muhammad ƙomiha, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Ulamiya, bugu na uku, 1407 AH/1987 Miladiyya.
  • Ibn Kathir Damaschi, Ismail Ibn Umar, al-Bidaya wa Al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407 AH/1986 Miladiyya.
  • Khalifa bin Khayyat, tarihi, bincike: Fawaz, Beirut, Darul Kutb al-Alamiya, 1415 AH/1995 miladiyya.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, al-Tanbiyyah wa al-Ishraf, gyara daga: Abdullah Ismail al-Sawi, Cairo, Dar al-Sawi, Beta (ƙom offset: Al-Manaba Al-Tulfaƙa al-Islamiya Publishing House).
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Ma'rifa Hajjullah Ali Al-Abad, ƙum, Publications of the World Congress of Sheikh Mofid, 14
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin Al'ummai da Al-Muluk, bincike: Muhammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, Dar al-Trath, 1967/1387 AD.
  • Abulfaraj Esfahani, Ali bin Hossein, Al-Aghani, Beirut, Dar Ahya Al-Trath

13 AH. Al-Arabi, 1994.