Sa'id Ɗan Abdullahi Hanafi
Sa'id Ɗan Abdullahi Hanafi (Larabci: سعید بن عبدالله حنفی) ya yi shahada shekara 61 hijira ƙamari, ya kasance cikin shahidan karabala. Kuma daga ƴan shi'ar garin kufa waɗanda suka kaiwa Imam Husaini (A.S) wasiƙu. Bugu da ƙari Sa'id shi ne wanda ya kaiwa Imam Husaini (A.S) wasiƙar Muslim Ɗan Aƙilu, bayan nan ya dawo ya shiga cikin ayarin Imam. A daren Ashura ya yi huɗubar nuna goyan baya ga Imam Husaini (A.S) cikin wannan huɗuba ya yi rantsuwa da za a ƙona shi a yana raye har sau saba'in a sake raya shi lallai ba zai ta ɓa janyewa daga goyan bayan Imam Husaini ba.
Isar Da Wasiƙa A Waƙi'ar Karbala
Sa'id Ɗan Abdullahi ya fito daga dangin bani hanifa Ɗan Lajim, dangin Abubakar Ɗan Wa'il daga rassan ƙabilar Adnan[1] mutumin gari kufa ne a cewa war Muhammad Samawi cikin littafin Absarul Al-aini Sa'id Ɗan Abdullahi ya shahara da jarumta da ibada.[2] a cikin ziyaratul Al-shuhada an ambace da Sa'ad,[3] a cikin ziyaratul Al-rajabiyya Imam Husaini (A.S) ya masa sallama da sunansa Sa'id.[4]
Sa'id ɗa Abdullahi da Hani Subai'i su ne mutanen da suka isar da wasiƙa mutanen kufa ta uku zuwa ga Imam Husaini (A.S).[5] marubuta sun tabbatar da cewa wasiƙa ce daga Shabas Ɗan Rib'i, Hajjar Ɗan Abjar Yazid Ɗan Haris, Yazid Ɗan Ruwayam, Azratu Ɗan ƙaisu, Amru Ɗan Hajjaj da Muhammad Ɗan Umairu.[6] wasu ba'ari sun yi amanna wannan aiki isar da wasiƙu ta hannun Sa'id Ɗan Abdullahi ya faru ne sakamakon alfarma da girman da yake da shi, ana fata da sarai ya yi amfani da wannan alfarma cikin gamsar da Imam Husaini (A.S) tafiya kufa.[7]
Imam Husaini (A.S) ya ba da amsa wasiƙun mutanen kufa ta hannun Sa'id Ɗan Abdullahi, ya rubuta cewa ya aiko Muslim Ɗan Aƙilu zuwa kufa matsayin jakadansa. A rahotan Tarikh Ɗabari (Talifi: 303 hijira ƙamari), lokacin da Muslim ya shiga garin kufa ya yi huɗuba a taron mutane, Abbas Ɗan Abi Shabib Shakiri, Habib Ɗan Mazahir da Sa'id Ɗan Abdullahi cikin wata huɗuba sun shelanta goyan bayansu ga Imam Husaini (A.S).[8] cikin wannan taro Muslim ya umarci Sa'id Ɗan Abdullahi ya je ya gaya Imam (A.S) zai iya tahowa garin kufa, sai Sa'id ya tashi ya koma garin makka ya kaiwa Imam Husaini (A.s) wasiƙar da Muslim Ɗan Aƙilu ya rubuto masa, bayan suka tahowa tare da Imam Husaini (A.s) zuwa kufa.[9]
Shelanta Cika Alƙawari Tare da Imam Husaini A Daren Ashura
Sa'id Ɗan Abdullahi a daren ashura ya yi huɗuba, ya yi rantsuwa da Allah cewa da za ƙona shi yana raye har karo saba'in sannan a sake raya shi ba zai ta ɓa janyewa daga goyan bayan Imam Husaini ba. Ya yi wannan maganar ne martani ga magana da Imam Husaini ya yi cikin maganar da yake yi ga sahabbansa tare da bada dama ga duk wanda yake son janyewa ya koma gida.[10]
Bada Kariya Ga Masu Sallar Azuhur A Ranar Ashura
A rahotan Maƙtale Nuwiyan, a azuhur ɗin ranar ashura yayin da Imam Husaini (A.S) yake yin salatul kaufi kaufi, Sa'id Ɗan Abdullahi da Zuhairu Ɗan ƙainu sun tsaya a gabansa suna masu sanya fusake da ƙirazansu matsayin garkuwa da saukar kibbai da masu kan Imam Husaini (A.S),[11] an naƙalto cewa lokacin da Imam ya yi shahada an samu adadin kibbai guda goma sha uku kan jikinsa ƙari kan saran takubba da aka yi masa.[12] da wannan dalili ake kiran Imam Husaini (A.S) da sunan shahidin sallah.[13] an naƙalto cewa lokacin da Sa'ad ya faɗi a ƙasa yayin fitar ransa ya dinga karanta wannan addu'a: Ya Allah! Kamar yadda ka tsinewa adawa da samudawa ka tsinewa waɗannan mutane (Sojojin kufa). Ya Allah! Ka yi daɗin tsira da aminci ga Annabi, kuma raɗaɗin ciwon da na jurewa a jikina ka sanar da shi gare shi; saboda haƙiƙa na kasance ina kwaɗayi da burin samun ladanka ya Allah cikin taimakon Annabinka.[14]
Sai ya juya ya kalli Imam Husaini (A.S) ya ce: ya Ɗan Manzon Allah! Shin na cika alƙawari? Imam (A.S) ya ce: za ka shiga aljanna tun kafin shiga ta.[15] an dangata waƙen jarumta da zai zo a ƙasa ga Sa'id Ɗan Abdullahi: Ya Husaini! Ka taho yau za ka haɗu da kakan za ɓa ɓ ɓen Allah kuma za ka ga babanka ma'abocin kyauta da karamci.[16]
Bayanin Kula
- ↑ Shamsuddin, Ansar al-Hussein, 1407H, shafi na 76.
- ↑ Samavi, Absar al-Ain, 2004, shafi na 187.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 70, juzu'i na 98, shafi na 272.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 340.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Dar al-Tarath, juzu'i na 5, shafi na 353.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Dar al-Tarath, juzu'i na 5, shafi na 353.
- ↑ Kamrahay, Unsurul Shujaat, 1389 AH, juzu'i na 1, shafi na 158.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, Dar al-Tarath, juzu'i na 5, shafi na 355.
- ↑ Samavi, Absar al-Ain, 2004, shafi na 188
- ↑ Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Dar al-Tarath, juzu'i na 5, shafi na 419.
- ↑ Ibn Tawoos, al-Malhouf Ali Qatali al-Tafouf, Anwar al-Hadi, shafi na 66.
- ↑ Ibn Tawoos, al-Malhouf Ali Qatali al-Tafouf, Anwar al-Hadi, shafi na 66.
- ↑ Muhaddi, Farhang Ashura, 1376, shafi na 263.
- ↑ Ibn Tawoos, al-Malhouf Ali Qatali al-Tafouf, Anwar al-Hadi, shafi na 66.
- ↑ Samavi, Absar al-Ain, 2004, shafi na 189.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Manaqib Ale Abi Talib, 1421, Juzu'i na 4, shafi na 112.
Nassoshi
- Ibnshahr Ashub, Muhammad Bin Ali, Manaqib Al Abi Talib, tlatemolistli uan lista tlen Yusuf al-Baqa'i, Dar al-Azwa, 1421 AH.
- Kamreei, Khalil, Unsurul Shujat ya Haftedo do ton wa yek ton, As'habul Seyyed al-Shahada, Dar al-Irfan, Qom, 1389.
- Majlesi, Mohammad Bagher, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Institute, 1403 AH.
- Muhaddi, Javad, Farhang Ashura, Qom, tlajkuiloli tlen tlauel ixmatij, 1376/1417 AH.
- Samawi, Muhammad bin Taher, Absar al-Ain fi Ansar al-Hussein tlaseuilistli ma eli ika ya, tlatemolistli tlen Muhammad Jaafar Tabasi, Qom, Zamzam Hedayat, 2004.
- Shams al-Din, Mohammad Mehdi, Ansar al-Hossein, Al-Baath Institute, Teherán, 1407 AH.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-umam wa Al-Muluk, Dar al-Tarath, B.
- Ibn Tawoos, Ali Ibn Musa, Allahoof fi Qatali al-Touf, Qom, Anwar al-Hadi, Bita.