Rayuwa Imani ce Da Gwagwarmaya

Daga wikishia

Haƙiƙa rayuwa faɗi tashi ce da kuma aƙida (larabci:إن الحياة عقيدة وإجتهاد), magana ce da ake jingina ta ga Imam Husaini (A.S), kuma an yi saɓani a kan ingancin jingina wannan magana ga Husaini bin Ali (a.s). akwai waɗanda suke jinginata zuwa ga Imam ba tare da ambaton sanadi ba, amma Murtada Muɗahhari yana ganin cewa wannan magana sakamakon rashin isnadi da sanadi da kuma rashin dacewarta da sauran maganganun Imam Husaini, da kuma rashin ingancin ma’anarta dalili ne da yake nuna cewa ba maganar Imam Husaini ba ce, kuma mai binciken tarihi Inayatullah Majidi ya yi aƙidan cewa wannan magana ɓarayin baitukan waƙar mawaƙin ƙasar misra na karni na sha hudu Ahmed Shawƙi.

Matsayi

Rayuwa aƙida ce da kuma jihadi, magana ce da ta shahara bisa ga abin da mai bincike na Iran Inayatullah majidi ya yi aƙida da shi saboda jingina ta ga Imam Husaini (a.s), kuma akwai irinsu Murtada Muɗahhari, malami mufakkiri ɗan Shi'a. waɗanda suka yi aƙida cewa jinginawa wannan magana ga Imam Husaini ba ta inganta ba,[1] kuma akwai waɗanda suka karɓa suka yarda da wannan magana, kuma suka ɗauke ta a matsayin shi'ari ne mai kayau ga mutumin da ya yi aƙida da Allah,[2] wasu kuma suna ganin ta a matsayin magana da dace domin isar da saƙo na aƙidar shi. gwargwadan yadda zai yiwu.[3]

Tattaunawa Game da Danganta Wannan Magana Ga Imam Husaini (A.S)

An samu saɓani a kan jingina wannan magana ga Imam husaini (a.s). Akwai masu bincike irin su Mahdi Bazargan da Yahya Nuri da suka yi aƙida da cewa tana daga cikin maganganun Imam.[4] kuma ba su kawo tushen da suka samo maganar ba.[5] Marubuci kuma mai bincike na Iran Zainu Abidina Ranama a cikin littafi mai suna rayuwar Imam Husaini ya yi aƙidan cewa, Rahnama ya rubuta a cikin littafin rayuwar Imam Husaini (a.s). wannann magana tana ɗaya daga cikin waƙoƙin Imam.[6]

Sabanin wannann mahangar, akwai masu bincike kan al'amuran Imam Husaini, kamar su Murtada Muɗahhari da Muhammad Sahati Sardarudi,[7] wadanda ba su dauketa a cikin maganganun Imam Husaini (a.s) da kuma malaminna dan Shi'a mai tinani Muhammad Taƙi Jaafari ya ruwaito ta a cikin littafin Taragum da Tafsirin Nahj al-Balagha a matsayin sashe na waƙa, ba tare da ya ce ya danganata ga kowa ba,[8] amma Muhammad Sihati Sardarudi ya karkare daga mahangar Jaafari cewa bai yi la'akari cewa wannann jumlar magana ce wacce aka rawaito daga Imam Husaini ba.[9]

kishiyar wannan ra'ayi, akwai masu bincike cikin kaziyoyi d asuka shafi Imam husaini (a.s), misalin murtda muɗahhari, da muhammad sihhati sardarudi.[10] basa ganin wannan magana daga maganganun imam husaini (a.s) ta fito, mufakiri ɗan shi'a muhammad taƙiyyu jafari ya naƙalto wannan magana cikin littafin tarjama wa tafsir nahjul balaga, ya naƙalto ta matsayin wani ɓarayi daga waƙa ba tare da dangantata ga wani mutum ba.[11] sai dai kuma muhammad sardarudi sihhati yafitar da natija daga siyaƙi da koro zancen jafar balagi cewa bai ɗauki wannan magana matsayin hadisi da aka rawaito shi daga imam husaini (a.s) ba.[12]

A cikin ƙasida mai suna “Nazari a kan Shahararriyar Magana; "Rayuwa aƙida ce kuma Jihadi ce" (ƙasidar Farisanci ce), Inayatullah Majidi ya yi aƙidan cewa wannann magana ba ta daga cikin zantukan Imam Husaini (a.s). a maimakon haka, ta samo asali ne daga waƙoƙin Mawaƙin ƙasar misra na ƙarni na goma sha huɗu Ahmad shauƙi,[13] baitin ya kasance kamar haka.

قف دون رأيك في الحياة مجاهدا إن الحياة عقيدة وجهاد

Ka tsaya kan ra'ayinka a rayuwa kana mai gwagwarmaya domin ita rayuwa aƙida ce da kuma ko faɗi tashi.[14]

Matasla kan Jingina wannan Magana Zuwa ga Imam Husaini (A.S)

Allama Almuɗahari ya tafi kan cewa wannan magana (rayuwa aƙida ce da kuma gwagwarmaya ba maganar Imam Husaini bace, kuma ya kafa hujja a kan haka.[15] daga cikin dalilin shi akwai:

  • Bata da Sanadi, kuma wannann jumla ba a sameta daga Imam Husaini (a.s) ba a cikin litattafan Musulunci.[16] haka nan Allama muɗahhari yana ganin cewa wannan magana asalinta yana komawa zuwa ga shekara arba'in ko haamsin da suka wuce a baya.[17]
  • A ɗaya ɓangaren kuma yana ganin cewa dole ne jihadi ya kasance saboda gaskiya, kuma jihadi don aƙida bai dace ba. Kamar yadda kur'ani ya jaddada jihadi don gaskiya, ba don aƙida ba,[18] haka nan kuma Muɗahhari ya bayyana cewa wannann magana ba ta dace da maganar Imam Husaini (a.s) da sauran maganganunsa ba. kalmomi, misali abin da aka rawaito daga gare shi yana cewa;

1. "Mutuwa a cikin izza da ɗaukaka ta fi rayuwa a cikin kaskanci, mutuwa ita ce mafi alheri daga wulaƙanta, haka kunyata ya fi alheri daga ya shiga wuta".[19]

2. Ku sani mazinaci ɗan mazinaci ya tilasta mana mu zaɓi ɗaya a tsakanin abubuwa guda biyu: tsakanin mutuwa cikin karamci da kuma rayuwa a wulaƙanci, mu ba zamu taɓa wulaƙanta ba, wato Imam Husaini ya zaɓi ya yi shahada kan ya rayu a ƙarƙashin bai'ar Yazidu ɗan Ma'awiya Allah ya la'ance shi.[20]

Bayanin kula

  1. Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 51; Motahari, majmu asar 23, 1389, shafi na 243.
  2. Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 51.
  3. Alaei, Mujahideen wa Shahidai . Rahe Azadi, 1358, shafi na 528.
  4. Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 53-54
  5. Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 53-54
  6. Rahnama, Zindigani Imam Husaini (AS), 1349, juzu'i na 1, shafi na 189.
  7. Saheti Sardroudi, Bazkoni cand hadis darbaraye Ashura, 2013, shafi na 122.
  8. Jafari,Tajameh wa tafsir Nahj al-Balagha, 1360, juzu'i na 8, shafi na 118.
  9. Saheti Sardroudi, Bazkoni cand hadis darbaraye Ashura, 2013, shafi na 122.
  10. Saheti Sardroudi, bazkhoni cande hadis mashhur darbaraye ashura, 2013, shafi na 122.
  11. Jafari, Tarjama wa tafsirin Nahj al-Balagha, 1360, juzu'i na 8, shafi na 118.
  12. Saheti Sardroudi,Bazkhoni candi hadis mashhur darbaraye ashura , 2013, shafi na 122.
  13. Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 5
  14. مجیدی‏، «پ‍ژوهشی درباره یک شعار معروف؛ ان الحیوة عقیدة و جهاد»، ص51؛ «قف دون رأيك في الحياة مجاهدا»، موقع الدیوان.
  15. Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 243.
  16. Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 243.
  17. Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 171.
  18. Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 244.
  19. Ibn Shahr Ashub, al-Manaƙib, bugun Allamah, juzu'i na 4, shafi na 68.
  20. Al-Sayed bin Taɓus, Allahouf, 1348, shafi na 95.

Nassoshi

  • Al-Sayyid bin Taɓus, Ali bin Musa, Allahouf Ali ƙatali al-Tofuf, bincike: Ahmad Fahr al-Zanjani, Tehran, Jahan, 1348.
  • Jagora, Zainul-Abdin,Zindigani Imam Husaini (AS), Bija, Littafan hadiye, bugu na 6, 1349.
  • Sahti Sardroudi, Muhammad, Bazkoni can hadis Mashhur darbaraye ashura, Kum, Kimiyyar Hadisi, bugun farko, 1381.
  • Alai, Amir, Mujahideen wa Shahidan 'Yanci, B.M., Tehran, Dehkhoda, bugun farko, 1358.
  • Majidi, Inayatullah, "Fajuheshi darbaraye yek shia'ar maruf innal hayata jihadun wa akida" a cikin tarin kasidu na taron kasa da kasa na Imam Khumaini (a.s) da al'adun Ashura. , Littafin Rubutu na Farko, Tehran, Mu’assasa Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (ra) 1374H.
  • «قف دون رأيك في الحياة مجاهدا»، موقع الدیوان، آخر مراجعة: ٨ أكتوبر/ أكتوبر ٢٠٢٢م.
  • مطهری، مرتضی، مجموعة أعمال ج23، تهران، صدرا، 1389ش.