Rayuwa Imani ce Da Gwagwarmaya
Rayuwa faɗi tashi ce da kuma aƙida (larabci:إن الحياة عقيدة وإجتهاد), magana ce da ake jingina ta ga Imam Husaini (A.S). An yi saɓani a kan ingancin jingina wannan magana ga Husaini bin Ali (A.S). akwai waɗanda suke jinginata zuwa gare shi ba tare da kawo sanadi ba,Murtada Muɗahhari yana ganin cewa wannan magana sakamakon rashin isnadi da kuma rashin dacewar ta da sauran maganganun Imam Husaini, da rashin ingancin ma'anarta dalili ne da yake tabbatar da cewa ba maganar Imam Husaini ba ce. Mai binciken tarihi Inayatullah Majidi ya yi imani cewa wannan magana gutsire ce daga baitukan waƙar mawaƙin ƙasar Misra a ƙarni na sha huɗu Ahmad Shauƙi.
Matsayi
Rayuwa aƙida ce da jihadi, magana ce da ta shahara bisa ga abin da mai bincike ɗan ƙasar Iran Inayatullah Majidi ya yi imani da shi saboda jingina ta ga Imam Husaini (A.S), Murtada Muɗahhari, malami mufakkiri ɗan Shi'a. waɗanda shi ma ya yi amanna da cewa jinginawa wannan magana ga Imam Husaini bai inganta ba,[1] Akwai waɗanda suka karɓa suka ɗauke ta a matsayin take ne mai kyau ga mutumin da ya yi imani da Allah,[2] Wasu kuma suna ganin ta a matsayin magana da ta dace domin isar da saƙo na aƙidarshi. gwargwadan yadda zai yi wu.[3]
Tattaunawa Game da Danganta Wannan Magana Ga Imam Husaini (A.S)
An samu saɓani dangane da jingina wannan magana ga Imam husaini (A.S). Masu bincike irin su Mahdi Bazargan da Yahaya Nuri da sun yi imani da cewa tana daga cikin maganganun Imam.[4] sai dai kuma ba su kawo tushen da suka samo maganar ba.[5] Marubuci kuma mai bincike ɗan ƙasar Iran Zainul Abidina Rahnama a cikin littafi mai suna "Rayuwar Imam Husaini" ya yi imani cewa ita wannann magana tana ɗaya daga cikin waƙoƙin Imam Husaini.[6]
saɓanin wannann mahangar, akwai masu bincike kan abubuwa da suka shafi Imam Husaini, misalin Murtada Muɗahhari da Muhammad Sahati Sardarudi,[7] waɗanda ba su ɗauke a a cikin maganganun Imam Husaini (A.S) da kuma malamin nan ɗanShi'a mai tinani Muhammad Taƙiyyu Jafari ya ruwaito ta a cikin littafin "Tarjama Wa Tafsiri Nahj al-Balagha" a matsayin sashe na waƙa, ba tare ya danganta ta ga kowa ba,[8] Sai dai kuma Muhammad Sihati Sardarudi ya ƙarƙare da cewa Jafari bai yi la'akari da wannann jumla a matsayin magana da aka rawaito daga Imam Husaini ba.[9]
A cikin ƙasida mai suna "Dirasa Haulal Alp-ƙaulil Shahir" Rayuwa aƙida ce Jihadi (Maƙala ce ta Farisanci), Inayatullah Majidi ya yi imani da cewa wannann magana ba ta daga cikin zantukan Imam Husaini (A.S). magana ce da ta samo asali daga waƙoƙin mawaƙin ƙasar Misra na ƙarni na goma sha huɗu Ahmad shauƙi,[10] baitin ya kasance kamar haka: }}
Tarjama: Ka tsaya kan ra'ayinka a rayuwa kana mai gwagwarmaya domin ita rayuwa aƙida ce da kuma ko faɗi tashi.[11]
Tambayoyi Da Aka Yi Kan Jingina Maganar Ga Imam Husaini (A.S)
Allama Muɗahari ya tafi kan cewa wannan magana ta (Rayuwa aƙida ce da gwagwarmaya) ba maganar Imam Husaini ba ce, kuma ya kafa hujja a kan haka.[12] daga cikin dalilin shi akwai:
- Bata da Sanadi, kuma wannann jumla ba a same ta daga Imam Husaini (A.S) ba a cikin litattafan Musulunci.[13] haka nan Allama Muɗahhari yana ganin cewa wannan magana asalinta yana komawa zuwa ga shekara arba'in ko hamsin da suka wuce a baya.[14]
- A ɗaya ɓangaren kuma yana ganin cewa dole ne jihadi ya kasance saboda gaskiya, jihadi don aƙida bai dace ba. Kamar yadda kur'ani ya jaddada jihadi don gaskiya, ba don aƙida ba.[15] Haka nan kuma Muɗahhari ya bayyana cewa wannann magana ba ta dace da maganar Imam Husaini (A.S) da sauran maganganunsa da kalmomi, misali abin da aka rawaito daga gare shi yana cewa:
- "Mutuwa a cikin izza da ɗaukaka ta fi rayuwa a cikin ƙasƙanci, mutuwa ita ce mafi alheri daga wulaƙanta, haka kunyata ya fi alheri daga ya shiga wuta".[16]
- Ku sani ɗan zina kuma ɗan ɗan zina ya tilasta mana mu zaɓi ɗaya a tsakanin abubuwa guda biyu: tsakanin mutuwa cikin karamci da kuma rayuwa a wulaƙanci, mu ba zamu taɓa yadda da wulaƙanta ba.[17]
Bayanin kula
- ↑ Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 51; Motahari, majmu asar 23, 1389, shafi na 243.
- ↑ Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 51.
- ↑ Alaei, Mujahideen wa Shahidai . Rahe Azadi, 1358, shafi na 528.
- ↑ Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 53-54
- ↑ Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 53-54
- ↑ Rahnama, Zindigani Imam Husaini (AS), 1349, juzu'i na 1, shafi na 189.
- ↑ Saheti Sardroudi, Bazkoni cand hadis darbaraye Ashura, 2013, shafi na 122.
- ↑ Jafari,Tajameh wa tafsir Nahj al-Balagha, 1360, juzu'i na 8, shafi na 118.
- ↑ Saheti Sardroudi, Bazkoni cand hadis darbaraye Ashura, 2013, shafi na 122.
- ↑ Majidi, “Barasi darbaraye yek shi'ar maruf; inna Al-Hayata Aƙeedah wa Jihadi”, shafi na 5
- ↑ Majidi, "Fajuheshi Darbaraye Yek Shi'ar Maruf: Innal hayata Akidatan wa Jihadan", shafi na 51. «قف دون رأيك في الحياة مجاهدا»، Shafin yanar gizo na Al-diwan
- ↑ Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 243.
- ↑ Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 243.
- ↑ Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 171.
- ↑ Motahari, MaJmu asare 23, 1389, shafi na 244.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, al-Manaƙib, bugun Allamah, juzu'i na 4, shafi na 68.
- ↑ Al-Sayed bin Taɓus, Allahouf, 1348, shafi na 95.
Nassoshi
- Al-Sayyid bin Taɓus, Ali bin Musa, Allahouf Ali ƙatali al-Tofuf, bincike: Ahmad Fahr al-Zanjani, Tehran, Jahan, 1348.
- Jagora, Zainul-Abdin,Zindigani Imam Husaini (AS), Bija, Littafan hadiye, bugu na 6, 1349.
- Sahti Sardroudi, Muhammad, Bazkoni can hadis Mashhur darbaraye ashura, Kum, Kimiyyar Hadisi, bugun farko, 1381.
- Alai, Amir, Mujahideen wa Shahidan 'Yanci, B.M., Tehran, Dehkhoda, bugun farko, 1358.
- Majidi, Inayatullah, "Fajuheshi darbaraye yek shia'ar maruf innal hayata jihadun wa akida" a cikin tarin kasidu na taron kasa da kasa na Imam Khumaini (a.s) da al'adun Ashura. , Littafin Rubutu na Farko, Tehran, Mu’assasa Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (ra) 1374H.
- «قف دون رأيك في الحياة مجاهدا»، Shafin diwan, ƙarshe da aka duba: 8 ga Oktoba/ Oktoba 2022.
- Murtada Mutahhari مجموعة أعمال ج23، Tehran, Sadra, 1389 sh.