Ranar Talaƙ

Daga wikishia

Ranar Talaƙ wato Alƙiyama (Larabci:يومُ التَّلاق) ko Ranar gamuwa tana daya daga cikin sunayen ranar ƙiyama, kuma an ambace ta a cikin Alkur’ani a aya ta 15 a cikin suratul Gafir. An ambaci ma’anoni guda biyar game da ranar Talaƙ, waɗanda su ne: 1 haduwar mutanen ƙasa da sama, 2 ko haduwar mahalicci da halittu, 3 ko taron al’ummomi tun daga farko da na ƙarshe, 4 ko haɗuwar mutum da aikinsa, 5 ko haduwar rayuka da jikkunansa.

Cikin Kuir'ani

An ambaci wannan kalma sau ɗaya a cikin Alƙur’ani, a aya ta 15 a cikin Suratul Ghafir

رَفِیعُ الدَّرَجَاتِ ذُو الْعَرْشِ یُلْقِى الرُّوحَ مِنْ أَمْرِهِ عَلىَ‏ مَن یَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ لِیُنذِرَ یَوْمَ التَّلَاق‏.
Maɗaukaki ne, Ma'abũcin Al'arshi, yana aika Rũhi da umurninsa a kan wanda yake so daga cikin bayinsa, domin Ya yi gargaɗi ga ranar gamuwa.



([1])


Ma'anar haɗuwa

Talak yana da bada ma'anar gamuwa da fuska da fuska da wani abu.[2] An ambaci ma'anoni da dama na haɗuwa a cikin ayar:

  • Kamar yadda aka ruwaito daga Imam Sadik (A.S) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Ranar haduwa ita ce ranar haduwar mutanen sama da mutanen kasa.[3]
  • Sheikh Mufid ya ce ranar taro ita ce ranar sakamako, inda rayuka da jikkuna suke haɗuwa.[4]
  • Ma'anar gamuwa ta zo a gamammiyar ma'ana d ata hado kowa da kowa daga halittun kasa da sama, wadanda suka gabata da wadanda za su zo, azzalumi da wanda aka zalunta, mahalicci da abin halitta, mutane da ayyukansa, gangar jiki da ruhi.[5] kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani cewa:
إِنَّ الأَوَّلینَ وَ الآخِرینَ لَمَجمُوعُونَ إِلى‏ میقاتِ یَومٍ مَعلُوم

“Hakika na farko da na karshe za a tara su ne a wani lokaci sanannen yini”.[6]

  • Gamuwa ta zo da ma'anar:[7] Mahalicci da halitta sun hadu (kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani Suratul Inshikak:
إِنَّکَ کادِحٌ إِلى‏ رَبِّکَ کَدحاً فَمُلاقیه

Lalle ne ya kai mutum kai mai fifutika ne zuwa ga Ubangijinka, kuma tabbas za ka hadu da shi”.[8]

  • Abin nufi daga gamuwa shi ne gamuwa da ayyuka.[9] da ya zo cikin suratul Alu Imran:
یَوْمَ تَجِدُ کُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ مِنْ خَیْرٍ مُّحْضَرًا

Mutum da aikinsa za su hadu (kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani: “Ranar da kowane rai zai gamu da ayyukan alheri da ya aikata.[10]

Bayanin kula

  1. سوره غافر،‌ آیه ۱۵.
  2. Rajeb Esfahani, Mufradat Alfaz Al-Qur'ani, 1412 Hijira, shafi na 745.
  3. Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403H, shafi na 156.
  4. Sheikh Mufid, Al-Masa'il Al-Akbariya, 1413 AH, shafi na 42
  5. Sheikh Baha'i, Miftah al-Falah, 1405H, shafi na 161.
  6. Suratul Waki'a, aya ta 49.
  7. Sheikh Baha'i, Miftah al-Falah, 1405H, shafi na 161.
  8. Suratul Inshiqaq, aya ta 6.
  9. Sheikh Baha'i, Miftah al-Falah, 1405H, shafi na 161.
  10. Suratul Alu-Imran, aya ta 30.

Nassoshi

  • Ragheb Esfahani, Hossein bin Mohammad, Mufradat Alfaz Al-Qur'an , Beirut, Dar al-Shamiya, 1412 AH.
  • Sheikh Baha'i, Muhammad bin Hossein, Miftah al-Falah fi amal al-ayum wa al-laila man al-wajibat wa al-mustahabat, Beirut, Dar al-Awatah publishing house, 1405 AH.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, Qom, Islamic Publications Office of Qom Teachers Society, 1403 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Masail al-Akbariya, Qom, Al-Tomar al-Alami Lalfiyyah al-Sheikh al-Mofid, 1413 AH.