Nuƙaba Bani Isra'ila

Daga wikishia

Nuƙaba ko Wakilan Bani Isra’ilaa, (Larabci: نقباء بني إسرائيل) magana ce kan Wakilai goma sha biyu da suke wakilcin ƙabilun Bani Isra’ilaa (ƴaƴan Annabi Yaƙub) Annabi Musa (A.S) ya zaɓe su bayan Allah ya ba shi umarni yin hakan, wazifarsu ta kasance kula da alƙawarin Allah da yake kan wuyan Bani Isra’ila, haka kuma akwai wazifar tattara rahoton Azzaluman mutane a lokacin tafiyar Baitul-Almuƙaddas, Musa ne ya buƙace su da tattaro rahotanni kuma kada su gayawa mutanesu rahotannin da aka samu, sai dai cewa aksarinsu sun saɓawa umarnin da ya ba su. A cikin masadir ɗin Shi’a da Ahlus-sunna akwai wata riwaya daga Annabi (S.A.W) da cikinta yake bayyana cewa adadin Halifofinsa daidai yake da adadin wakilan Bani Isra’i, shi ne hadisi da ya shahara da riwayar Halifofi goma sha biyu, Malaman Shi’a suna dogara da wannan hadisi kan tabbatar da Imamanci.

Nuƙaba Wakilan Hazrat Musa (A.S)

Nuƙaba Bani Isra’ila sun kasance Manzannin Annabi Musa (A.S) tsakaninsa da mutanensa[1] kan asasin riwayoyi, ƙarƙashin umarnin Ubangiji ta hannun Annabi (A.S) aka zaɓe su Wakilai da Jakadu,[2] a cewar Malaman tafsiri, Nuƙaba Bani Isra’ila sun fito ne daga ƙabilu goma sha biyu daga Bani Isra’ila (ƴaƴan Annabi Yaƙub).[3] daga kowace ƙabila an zaɓi wakili guda ɗaya.[4]

Nuƙaba su ne Manyan mutane[5] da hukuncinsu yake aiki da suka kasance mutane masu matsayi da ƙima ta musammam cikin Bani Isra’ila,[6] cikin ba’arin litattafan tafsiri an bayyana Nuƙaba matsayin Shugabannin mutanen Annabi Musa (A.S).[7] kwamandoji[8] Sarakuna,[9] wasu jama’a sun yi imani kan cewa daga baya Allah ya zaɓe su Annabawa,[10] wasu ba’ari kuma sun tafi kan cewa Nuƙaba sun kai ga cimma mafi girmama muƙami, suna ganinsu matsayin Annabawa da aka aikowa da litattafai, sun wuce gamagarin Annabawa amma kuma ba su kai muƙamin Annabawa Ulul Azmi ba.[11] Cikin aya ta 12 suratul Ma’ida wacce a cikin ta ne Allah ya zaɓi Wakilai goma sha biyu daga Bani Isra’ila, cikin Alkur’ani ba ayi bayani ƙarara ba kan wanne matsayi suke da shi,[12] Malaman tafsiri suna da mabambanta ra’ayoyi batunsu.[13]

Kamanta Halifofin Annabi Da Nuƙaba Bani Isra’ila

Cikin wata riwaya da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) an yi bayani cewa adadin halifofinsa misalin adadin Nuƙaba Bani Isra’ila ne.[14] waɗannan gungun riwaya sun shahara da sunan hadisan halifofi goma sha biyu waɗanda cikinsu aka yi bayani cewa adadin halifofinsa sun kasance mutane goma sha biyu kuma baki ɗayansu za su fito daga ƙuraishawa,[15] Malaman Shi’a suna amfani da waɗannan riwayoyi kan tabbatar da Imamanci,[16]

Kan asasin wani hadisi daban, Annabi (S.A.W) ya nuna cewa Makomar al’ummarsa misalin Bani Isra’ila ne,[17] haka zalika cikin mubaya’ar Aƙbatu Annabi (S.A.W) ya zaɓi wakilai goma sha biyu daga mutanen Madina domin su zama wakilansa a Madina.[18]

Sayyid Muhammad Husaini ɗabaɗaba’i, cikin tafsirul Almizan, ya kamanta Nuƙaba’u Bani Isra’ila da misalin Ulul Amri a addinin muslunci, ya bayyana cewa sun kasance Maraji’ai kan al’amuran addini dana duniya ga Bani Isra’ila.[19]

Wazifar Nuƙabar Bani Isra’ila

Bisa ayoyin Alkur’ani, an ɗora wazifar kula da alƙawarin da Allah ya karɓa daga hannun Bani Isra’ila kan wuyan Nuƙaba,[20] haka kuma daga ɓangaren Musa (A.S) an ɗora masa nauyin ya jagoranci tafiya zuwa Baitul-Almuƙaddas,[21] ya je ya tatataro bayanai da rahotanni dangane da Azzaluman mutane,[22] a ƙasar Kan’an,[23] Shamat,[24] ko yankin Ariha [yadash 1] da suke rayuwa cikin ƙasar Sham,[25] Bayan sun gama rubuta abin da suka gani, sai suka koma wajen Musa (A.S).[26] suka yi magana kan girman mazauna wadannan yankuna.[27] sai dai cewa babu wanda ya girmama umarnin Musa (A.S) in banda mutum biyu,[28] zuwa biyar[29]

Sunayen Nuƙaba Bani Isra’ila

Sa’alabi daga Malaman tafsiri na Ahlus-Sunna a cikin tafsirinsa ya kawo sunayen Nuƙaba Bani Isra’ila, sun kasance kamar yadda bayaninsu zai zo a ƙasa: 1. Shamel Bn Ran 2. Shaƙat Bn Houri 3. Kaleb Bn Yoƙna 4. Maƙail Bn Yusuf 5. Yoshua Bn Nun 6. ƙantam Bn Argun 7. Madi Bn Udi 8. Jedi Bn ƙaman 9. Bayanun Bn Malikiya 10. Naftali Mohr Bn Waƙsi 11. Hamael Bn Hamal 12. Sabur Bn Malkiya.[30] A wasu wuraren kuma an ambaci sunayen Naƙba da dan bambanci.[31]

Bayanin kula

  1. Dinouri, Al-Wadihu, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 190.
  2. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 265.
  3. Ibn Hamush, Al-Hudaiya ili Balogh al-Nahiya, 1429 AH, Juzu'i na 3, shafi na 1639; Meibodi, Kashf al-Asrar, 1371, juzu'i na 3, shafi na 57.
  4. Thaalabi, Tafsir al-Thalabi, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi.362; Siyuti, dattijo al-Manthor, juzu'i na 2, shafi na 267.
  5. Thaalabi, Tafsir Thalabi, 1418 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 362.
  6. Jurjani, Darj Al-Duarr, 1430 AH, juzu'i na 1, shafi na 552.
  7. Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1369, juzu'i na 4, shafi na 319.
  8. Deobandi, Tafsir Kabuli, 1385, juzu'i na 2, shafi na 52.
  9. Samarkandi, Bahr al-Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375; Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 265.
  10. Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 260
  11. Sadeghi Tehrani, Tajeman Fargan, 2008, juzu'i na 2, shafi na 41.
  12. Mughniyeh, Al-Tafsir Al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 3, shafi na 30.
  13. Duba Aamili, Tafsir Aamili, 1360, juzu'i na 3, shafi na 239.
  14. Khazaz Razi, Kefayat Athar, 1401 AH, shafi na 27; Sheikh Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 468; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi 118; Ibn Hanbal, Masnad na Ahmad Ibn Hanbal, 1416 AH, Juzu'i na 6, shafi na 321, 406; Tabarani, al-Mu'jam al-Kabir, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 157; Abi Ya’ali, Musnad Abi Ya’ali, 1404 AH, juzu’i na 8, shafi:444; Bezar, Musnad Bezar, 1993, juzu'i na 5, shafi na 320.
  15. Muassaseh Marif Islami, Al-Ahadith Al-Imam al-Mahdi, 1428 AH, juzu'i na 3, shafi na 501.
  16. Duba Samadi, “Imamat isana ashriyya”, shafi na 430.
  17. Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 203.
  18. Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Erbali, Kashf al-Ghamma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 55.
  19. Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 5, shafi na 240.
  20. Ibn Suleiman, Tafsirin Muqatil bin Suleiman, 1423 AH, juzu'i na 1, shafi:460; Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 6, shafi na 95.
  21. Ibn Hamush, Al-Hudaiya ili Balogh al-Nahiya, 1429 AH, Juzu'i na 3, shafi na 1639; Samarkandi, Bahr al-Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375.
  22. Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 6, shafi na 96; Samarkandi, Bahrul Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375; Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Ibn Hamoush, Al-Hudaiya ili Balogh al-Nahiya, 1429H, juzu'i na 3, shafi na 1640.
  23. Thaalbi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 36; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 615; Beidawi, Anwar al-Tanzil, 1418 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 118.
  24. Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 6, shafi na 96; Meibodi, Kashf al-Asrar, 1371, juzu'i na 3, shafi na 58.
  25. Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 615; Beidawi, Anwar al-Tanzil, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 118; Tabarsi, Tafsir Jameem Al Jame, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 317.
  26. Samarkandi, Bahr al-Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375; Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Shearani, Binciken Al-Qur'ani na Allameh Shearani, 2006, juzu'i na 1, shafi.420.
  27. Zamakhshari, al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 615.
  28. Samarkandi, Bahr al-Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375; Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Jurjani, Darj al-Darr, 1430 AH, juzu'i na 1, shafi na 552; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 265.
  29. Samarkandi, Bahr al-Uloom, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 375; Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu'i na 2, shafi.369; Jurjani, Darj al-Darr, 1430 AH, juzu'i na 1, shafi na 552; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 265.
  30. Thaalbi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422H, juzu'i na 4, shafi na 36.
  31. Duba Shearani, Pajuheshhaye Kur'ani na Allameh Shearani, 2006, juzu'i na 1, shafi na 419.

Nassoshi

  • Alousi, Seyyed Mahmoud, Ruh al-Ma'ani fi Tafsir al-Qur'an al-'Azeem, research by Ali Abd al-Bari Attiyah, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1415 AH.
  • Abulfatuh Razi, Hossein bin Ali, Ruz al-Jinnan and Ruh al-Jinnan fi Tafsir al-Qur'an, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1408 AH.
  • Ibn Abi Zainab, Muhammad Ibn Ibrahim, Al-Ghaibah, research by Ali Akbar Ghafari, Tehran, Sadouq Publishing, 1397 AH.
  • Ibn Hamoush, Makki bin Abi Talib, Al-Hudaiya Ili Bologh Al-Nahiya, Sharjah, Al-Sharqa University, 1429 AH.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Masnad Ahmad Ibn Hanbal, Beirut, Al-Rasalah Institute, 1416 AH.
  • Ibn Suleiman, Muqatil, Tafsir Muqatil Bin Sulaiman, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1423 AH.
  • Abi Ya'ali Mosuli, Ahmed Bin Ali, Musnad Abi Ya'ali, Damascus, Dar al-Ma'mun for Heritage, Hossein Salim Asad's research, 1404 AH.
  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, research by Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tabriz, Bani Hashemi, 1381 AH.
  • Bazar, Ahmed bin Amr, Musnad al-Bazar, Mahfouz Rahman Zainullah's research, Medina, Al-Uloom and Al-Hakim School, 1993.
  • Beidawi, Abdullah bin Omar, Anwar al-Tanzil and Asrar al-Taawil, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1418 AH.
  • Thaalabi, Abd al-Rahman bin Muhammad, Tafsir al-Thaa'albi known as Al-Jawahir al-Hasan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1418 AH.
  • Thaalbi, Ahmad bin Muhammad, Al-Kashf and al-Bayan al-Ma'roof Tafsir al-Thalabi, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1422 AH.
  • Jurjani, Abd al-Qahir bin Abd al-Rahman, Darj al-Darr fi Tafsir al-Qur'an al-Azeem, Amman, Jordan, Dar al-Fikr, 1430 AH.
  • Khazaz Razi, Ali bin Muhammad, the adequacy of athar in the text of Ali Imams of the twelfth century, research by Abdul Latif Hosseini Koh Kamri, Qom, Bidar, 1401 AH.
  • Dinouri, Abdallah bin Muhammad, al-Hashar fi Tafsir al-Qur'an al-Karim, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1424 AH.
  • Deobandi, Mahmoud Hassan, Tafsir Kabuli, Tehran, Ehsan Publishing House, 11th edition, 1385.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Al-Kashaf on the facts of Ghawamaz Al-Tanzil and Ayun Al-Aghawil in the ways of Ta’awil, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, third edition, 1407 AH.
  • Samarkandi, Nasr bin Muhammad, Tafsir of Samarkandi known as Bahr al-Uloom, Beirut, Dar al-Fikr, 1416 AH.
  • Siyuti, Al-Dar Al-Manthur Fi al-Tafsir Balmathur, Qom, School of Ayatollah al-Marashi Najafi, 1404 AH.
  • Shearani, Abul Hasan, Quranic researches of Allameh Shearani in Majmam al-Bayan commentaries, Qom, Bostan Kitab, 2006.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Khisal, revised by Ali Akbar Ghafari, Qom, Jamia Modaresin, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Laihdara al-Faqih, Research by Ali Akbar Ghafari, Qom, Islamic Publications Office, 1413 AH.
  • Sadeghi Tehrani, Mohammad, Farqan interpreter: A brief interpretation of the Holy Qur'an, Qom, Shokarane, 2008.
  • Samadi, Qanbar Ali, "Twelfth Imamat", in Encyclopedia of Islamic Kalam, Volume 1, Qom, Imam Sadiq Institute (AS), 1387.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, second edition, 1390 AH.
  • Tabarani, Suleiman bin Ahmad, Al-Tafseer al-Kabeer: Tafsir al-Qur'an al-Azeem, Irbid, Jordan, Dar al-Kitab al-Thaqafi, 2008.
  • Tabarani, Suleiman bin Ahmad, Al-Mu'jam al-Kabir, researched by Hamdi bin Abdul Majid al-Salfi, Mosul, School of Science and Law, second edition, 1404 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Tafsir al-Jameed al-Jame, Qom, Qom Seminary, Management Center, 1412 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow, third edition, 1372.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Daral al-Marefa, 1412 AH.
  • Tayeb, Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam Publications, second edition, 1369.
  • Aamili, Ebrahim, Tafsir Aamili, Tehran, Sadouq Bookstore, 1360.
  • Institute of Islamic Education, Al-Imam al-Mahdi, Qom, Jamkaran Holy Mosque Publications, 1428 AH.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, al-Tafsir al-Kashif, Qom, Dar al-Katab al-Islami, 1424 AH.
  • Meybodi, Ahmad bin Mohammad, Kashf al-Asrar and Kitah al-Abrar, Tehran, Amir Kabir, 5th edition, 1371.