Najma Mahaifiyar Imam Rida (A.S)
Kabari da ake danganta shi ga Najma khatun a mashrabe Ummu Ibrahim a garin Madina Kabari da ake danganta shi ga Najma khatun a mashrabe Ummu Ibrahim a garin Madina | |
Cikakken Suna | Najma Mahaifiyar Imam Rida (A.S) |
---|---|
Laƙabi | Shaƙra'u |
Mahallin Haihuwa | Garin Nauba (Arewacin afrika) ko jazirar Marsi (Kudancin faransa) |
Ƙabari | Kusa da kabarin Hamida matar Imam Sadik (A.S), Mashraba Ummu Ibrahim, yankin awalia Maida, gabashin makabartar baƙi'i |
Daga Sahabbai | Na Imam Sadik (A.S). Imam Kazim (A.S). Imam Rida (A.S) |
Najama Khatun (Larabci: نجمة أم الإمام الرضا (ع)) matar Imam Kazim (A.S) ita ce mahaifiyar Imam Rida (A.S) da Fatima Ma'asuma (A.S) hakika Najama Khatun ta kasance baiwa wacce Malama Hamida Matar Imam Sadiƙ (A.S) Asalin wacce ta sayo ta kuma ta yi kyautar ta ga Imam Kazim (A.S) wasu riwayoyi sun bayyana cewa Hamidatu ta yi wani mafarki wanda cikinsa Annabi (S.A.W) ya umarceta da ta yi kyautar wannan baiwa ga Imam Kazima (A.S) kabarinta yana Masharabatu Ummu Ibrahim[Tsokaci 1] a garin Madina.
Nasaba Da Kabila
Najama wata baiwa ce da Hamidatu matar Imam Sadiƙ (A.S) saye ta sannan ta yi kyautar ta ga Imam Kazim (A.S) wacce itace ta Haifa masa Imam Rida (A.S) da kanwarsa Fatima Ma'asuma (A.S)[1] wasu malamai sun tafi kan cewa Asalinta daga garin Nauba a arewacin Afrika wasu kuma sun tafi kan cewa ta fito ne daga tsibirin Marsiyya kudancin kasar Faransa[2] da wannan ne wasu ke kiranta da furen Marsiyya ko kuma kyakkyawar Naubiyya.[3]
Suna Da Lakabi
Mafi shaharar sunanta shi ne Najma Khatun,[4] sannan ana kiranta kuma da sunayen garin da ta fito misali:[5] Samanatu,[6] Aruye, Tuktam, Kaizuran,[7], Sakar da Khaizuranil Mursiyya[8] Ya zo a riwayar Shaik Saduk cewa lokacin da akayi kyautar ta ga Imam Kazim (A.S) an kirata da Tuktam 5 amma kuma yayinda ta Haifi Imam Rida (A.S)[9] sai aka kirata da Dahira[10] ana mata lakabi da Shakara'u sannan ana mata Alkunya da Ummu Banin.[11]
Mukami Da Matsayi
An nakalto wata Magana da Hamida matar Imam Sadiƙ (A.S) da ta gayawa Imam Kazim (A.S) cewa ni ban taba ganin baiwa mai falala kamar Najama Katun ba[12] wasu riwayoyi daga Shaik Saduk cewa Hamidatu ta yi mafarki da Hazrat Muhammad (S.A.W) ya umarceta tayi kyautar baiwarta Najama ga Imam Kazim (A.S) saboda ita zata haifi mafi darajar halittu a doran kasa, da wannan dalili ne Hamidatu tayi kyautar Najama wacce ta kasance budurwa a wannan lokaci.[13] Musa Bn Jafar (A.S) ya yi bayanin yanda aka sayo Najama Katun bisa umarnin Annabi.[14] An nakalto daga Najama tana cewa lokacin da na dauki ciki daga Imam Rida (A.S) ban kasance ina jin nauyayar ciki ba, sannan na kanji sautin tasbihi da hailala daga cikina a lokacin da nake barci idan na farka sai na ji babu komai.[15]
Wurin Da aka Bizne ta
Kamar yanda Shaik Muhammad Baƙir Husaini Jalali yake fada hakika kabarin Najama Katun ya kasance yana kusa da Kabarin Hamida matar Imam Sadiƙ (A.S) a garin Masharabatu Ummu Ibrahim a yankin Awali Madina gabashin Makabartar Baki'i.[16]
Bayanin kula
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 14.
- ↑ Ghaemi, a Maktabatu Alame Alu Muhammad, 1378, shafi na 30.
- ↑ Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 2, shafi na 259.
- ↑ "Kamal al-Din, juzu'i na 1, shafi na 305; Uyoon al-Akhbar, juzu'i na 1, shafi na 16."
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1367, juzu'i na 1, shafi na 486; Majama'al al-Tawarikh wa al-Qasas, Tehran, shafi na 457.
- ↑ "Uyoon al-Akhbar, juzu'i na 1, shafi na 16."
- ↑ Majamal Al-Tawarikh wa al-Qasas, Tehran, shafi na 457.
- ↑ "Manakib Al Abi Talib, juzu'i na 4, shafi na 367."
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 14.
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 15.
- ↑ Qomi, Tarikh Qum, 1361, shafi na 199
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 15.
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 17.
- ↑ Masoudi, Esbatul Wasiyya, 1426 AH, shafi na 202.
- ↑ Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 20.
- ↑ Hosseini Jalali, Fadak wa-Al-Awali, 1426H, shafi na 55.
Tsokaci
- ↑ "Mashraba Ummu Ibrahim tana nufin lambu ko ƙasa mai laushi inda tsire-tsire ke girma cikin sauƙi. Ana kuma amfani da wannan kalma don ƙasa da ke da tudu a tsakiyarta ko kuma gini a cikinta. Mashraba tana cikin lambu da ke da tsakar gida ko kuma ɗakin da aka haifi Ibrahim, ɗan Manzon Allah (SAW), a cikinsa. Wannan Mashraba tana arewacin Banu Qurayza a Harra ta Gabas, wanda ake kira 'Daji'. Littafin Wafa' al-Wafa' bi Akhbar Dar al-Mustafa (SAW), juzu'i na 3, shafi na 825."
Nassoshi
- Erbali, Ali Ibn Essi, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-Imam, Musahh Rasuli Mahalati, Tabriz, Bani Hashemi Publications, bugu na farko, 1381H.
- «تصاویری از مزار مادر امام رضا(ع) در مدینه»، همشهری آنلاین، Shigar da labarin ranar 7 ga Oktoba, 1391, duba ranar 18 ga Oktoba, 1400.
- Hosseini Jalali, Mohammad Baqir, Fadak and Al-Awali O Al-Hawait al-Sabah fi al-Katab wa Sunnah wa al-Tarikh wa Al-Adab, Mashhad, Sakatariyar Majalisar Tarihi ta Kimiyya da Ruhaniya ta Sayyida Fatima Zahra, 1426 AH.
- Sadouq, Mohammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza, Mehdi Lajordi, Tehran, Nash Jahan, 1378 H.
- Ghaemi, Ali, a makarantar Alam Al Mohammad, Tehran, Amiri Publications, 1378.
- Qomi, Hossein bin Muhammad bin Hassan, Tarihin Qum, wanda Hassan bin Ali bin Hasan Abd al-Mulk Qomi ya fassara, Seyyed Jalaluddin Tehrani ya yi bincike, Tehran, Tos Publications, 1361.
- Kulaini, Mohammad bin Yaqub, Al-Kafi, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiya, bugu na uku, 1367.
- Majamal al-Tawarikh wa-Al-Qasas, marubucin da ba a san shi ba, Malik al-Shaara Bahar bincike, Tehran, Kalala Khavar, Bita.
- Masoudi, Ali bin Hossein, Esbatu Wasiyya, Qum, Wallafar Ansar, bugu na uku, 1426H.