Jump to content

Nahrawan

Daga wikishia
Nahrawan
ƘasaIraƙ
JihaBagdad
HarsheLarabci
Tsohon sunaBirnin Jisru Nahrawan
Shekara da aka kafa taZamanin Daular Sasaniyawa
Muhimman abubuwan da suka faruYaƙin Nahrawan


Nahrawan wani yanki ne a yake a gabashin Dajla a ƙasar Iraƙ wanda ya kasance tsakanin Bagdad da Wasiɗ.[1] An raba wannan yanki zuwa sasannin guda uku, na sama, na tsakiya da na ƙasa wanda ake kira Ƙatul, Tamarra da Jisru Nahrawan.[2]Yaƙin Nahrawan, shi ne ƴakin da Imam Ali (A.S) ya gwabza tare da Khawarijawa, da ya faru a shekara ta 83H, a kusa da Jisru Nahrawan[3]

Nahrawan yna da nisan farsaki huɗu (Kilomita 22) daga Bagdad.[4] Kuma yana daga masaukin matafiya daga hanyar Khurasan[5] Wasu malamai da masana masu tunani na Musulunci[6] kamar Abul Faraj Nahrawani an danganta su da wannan yanki.[7]

Nahrawan a asali suna ne na wata ƙorama da ya ware kansa daga kogin Dajla kuma yake shayar da sassan yanki ruwa.[8] samar da wannan ƙorama ana jingina shi da Iraniyawa a zamanin Sasaniyawa musamman zamanin Shapur na biyu.[9] an kuma gina gadoji da madatsun ruwa a kansa,[10] Birnin Jisru Nahrawan shima ya kasance kusa da ɗaya daga cikin waɗannan gadoji.[11]

An samu rahotanni daban-daban game tushen wannan kogi, daga ciki akwai masu cewa tushensa yana Azerbaijan, ko kuma kusa Tamarra da Halwan[12] Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sunansa na Farsi shi ne Jurawan amma bayan shiga harshen Larabci sai aka koma ana kiransa da Nahrawan[13] Cikin rarrabawar Iraƙ a wannan zamani, Nahrawan wani ɓangare ne na garin Mada'in da yake babban birnin Bagdad.[14]

Bayanin kula

  1. ↑ Ƙazwini, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, shafi na 472; Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
  2. ↑ Alawi Isfahani, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, shafi na 413.
  3. ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325; Muhammadi Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
  4. ↑ Isɗarkhi Karkhi, Al-Masalik Wal Mamalik, shafi na 86.
  5. ↑ Alawi Isfahani, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, shafi na 413.
  6. ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
  7. ↑ Ƙazwini, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, shafi na 472.
  8. ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 242-243.
  9. ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245.
  10. ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
  11. ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
  12. ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
  13. ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 244.
  14. ↑ «هیئة الاستثمار توجه باشغال المراکز الخدمیه فی محمع بسمایة السکنی»، gidan yanar gizo na Zagros News.

Nassoshi

  • Alawi Isfahani, Ibrahim Bin Nasir, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, binciken Muhammad Mahadi Khurasan, Qom, Al-Maktabatul Haidariyya, 1377Sh.
  • Hamawi, Yaƙut Bin Abdullah, Mu'ujam Al-Buldan, Beirut, Darus Sadir, bugu na biyu, 1995M.
  • Himyari, Muhammad Bin Abdullah, Ar-Raudul Mi'iɗar fi Khabaril Aƙɗar, binciken Ihsan Abbas, Beirut, Cibiyar Nasir lis-Saƙafa, bugu na biyu, 1980M.
  • Hududul Alam min al-Mashriƙ ilal Maghrib, fassarar Sayyid Yusuf al-Hadi, Alkahira, Darus Saƙafa lin Nashr, 1423M.
  • Isɗakhri Karkhi, Ibrahim Bin Muhammad, Al-Masalik Wal Mamalik, Beirut, Darus Sadir, 2004M.
  • Ƙazwini, Zakariyya Bin Muhammad, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, Beirut, Darus Sadir, 1380H.
  • Muhammadi Malayeri, Muhammad, Tarikh Wa Farhange Iran dar Daurane Intiƙal az Asre Sasani be Asre Islami, Tehran, Ɗus, bugun na biyu, 1379Sh.
  • «هیئة الاستثمار توجه باشغال المراکز الخدمیه فی محمع بسمایة السکنی»، (Mayar da hankali kan mamaye cibiyoyin hidima a rukunin gidajen zama na Bismaya), Gidan yanar gizon Zagros News, ranar da aka buga labari: 14 ga Agusta, 2022, ranar da aka duba: 22 ga Oktoba, 2026M.