Lauhul Mahfuz

Daga wikishia
Ka da ayi kuskuren ƙaddara shi da Lauhul Mahawi wa Isbat

Lauhul mahfuz (Larabci:اللوح المحفوظ ) shi ne mahallin Kur’ani na haƙiƙa wanda aka rubutu dukkanin abubuwan da za su faru a duniya da ba zasu taɓa canjawa, sanin lauhul mahfuz yana da matuƙar muhimmanci domin sani da fahimtar haƙiƙanin kur’ani, saboda kamar yadda ba’arin malaman tafsiri suke cewa shi lauhul mahfuz wani wuri na asali bakiɗayan litattafan sam, daga jumlarsu akwai kur’ani, suna ganin lauhul mahfuz wani abu da yake daidai da ilimin Allah da baya karɓar canji da canjawa, kuma bakiɗayan abubuwa da za su faru a duniya an rubuta su a cikinsa. shi lauhul mahfuz ya kasance saɓanin lauhul mahawi wa isbati wanda cikinsa a rubuta abubuwan da zaus faru a duniya da surar yankewa ba da rashin canji da canjawa. Lauhul mahfuz yana daga abubuwa da suke ɓoye bayan ɗabi’a waɗanda ba za a iya gano su da riskarsu da mariskai ba, mafi muhimmanin abubuwan da lauhul mahfuz ya keɓantu da su, kasancewarsa ya tattaro komai da komai, wasu gungun malaman tafsiri suna ganin lauhul mahfuz matsayin kinaya kan ilimin Alla, sai dai wasu gungu daga cikinsu tare da jingina da ayoyin kur’ani sun yti watsi da wannan magana, haka nan kuma wasu ba’ari daga masana falsafa suna gani daidai yake da matsayin Aƙlul Fa’al ko Jibrilu, sai dai cewa wannan magana ta saɓawa zahirin shari’a kuma babu dalili daga kur’ani da riwaya kanta. Wasu ba’ari masana muslunci tare da dogara da ayoyi daga kur’ani sun tafi kan cewa haƙiƙa ma’asumai sha huɗu suna da ilimi da tsinkaya daga lauhul mahfuz, kishiyar wannan magana an samu wasu ba’ari daga malaman tafsiri da suka tafi kan cewa ilimi da tsinkaya kan lauhul mahfuz ya keɓantu da Allah shi kaɗai, babu wani mahaluƙi da yake iya tsinkaye kansa, a cewar masu zurfafa bincike kan muslunci, rubuta ɗaukacin abubuwan da za su faru a duniya cikin lauhul mahfuz baya da ma’anar tilasta mutum, saboda su ayyukan mutum da wancan sura da suke afkuwa, (suna afkuwa bisa zaɓin mutum) a haka ne aka rubuta su a lauhul mahfuz, sannan shi ilimin Allah baya canja haƙiƙa.

Matsayin Lauhul Mahfuz Cikin Bahasosin Muslunci

Lauhul mahfuz wani isɗilahi ne na kur’ani da yake shiryarwa zuwa ga mahallin kur’ani na asali da haƙiƙa gabanin saukarsa daki-daki zuwa ga Annabi (S.A.W)[1] Allama ɗaba’ɗaba’i mawallafin tafsirul Almizan, ya yi imani kan cewa kur’anin da yake a lauhul mahfuz ya fi ƙarfin fahimtar mutane, da wannan dalili ne Allah sauke shi zuwa ga mutane da mafi sauƙaƙar martaba zuwa ga mutane,[2] a cewar Allama ɗabaɗaba’i ɗaukacin litattafan sama da aka saukar da su ga Annabawa an ciro kofinsu daga lauhul mahfuz, da wannan dalili ne kur’ani ya kira lauhul mahfuz da sunan Ummul Kitab (Littafi na Asali)[3] haka nan sanin lauhul mahfuz domin fahimtar ayoyi da suke da alaƙa da saukar kur’ani, katanguwar kur’ani daga jirkita da kasancewarsa wahayi, ana ƙaddara shi wani abu mai matuƙar muhimmanci.[4] Allama Majlisi mawallafin littafin Biharul Al-anwar cikin bayani game da lauhul mahfuz, ya bayyana shi wani abu da yake matsayin ilimin Allah wanda cikinsa aka rubuta ɗaukacin abubuwan da za su faru a duniya da babu canji cikinsu.[5] haka nan a cewar Jafar Subhani malamin tafsiri na shi’a, cikin wannan allo rubuta duk wasu da tabbas za su faru abubuwa da suke da dangantaka da mutum.[6] sakamakon rubuta abubuwa da tabbas za su faru cikin wannan littafi, shi ne dalili da yasa ake ganin lauhul mahfuz matsayin wani wuri na hukunce-hukuncen Allah.[7] kishiyar lauhul mahfuz akwai wani allo da ake kira da sunan lauhul mahawi wa isbati wanda shi cikinsa ba a rubuta abubuwa da za su faru a duniya cikin yanayin tabbaci da yankewa da rashin canji da canjawa ba.[8] Kalmar lauhul mahfuz ta zo sau ɗaya cikin kur’ani an ambace shi: فِي لَوْحٍ مَحْفُوظٍ[9] ba’arin Malaman tafsiri sun tafi kan cewa a wasu ayoyin daban an yi ishara zuwa ga laihul mahfuz cikin mabambanciyar jumla, daga jumlarsu akwai «كِتَابٍ مُبِينٍ» [10] ma’ana (littafi mabayyani) «كِتَابٍ مَكْنُونٍ» [11] (ɓoyayyen littafi) da kuma «أُمِّ الكِتَابِ» [12] (littafi na asali)[13]

Haƙiƙanin Lauhul Mahfuz

Lauhul mahfuz yana daga jinsin al’amura da suka ɓuya daga barin ɗabi’a, wani abu ne ba a a iya riskar da mariskai da tajaribar ɗan adam,[14] a cewar Muhammad Hadi Marifa da Nasir Makarim Shirazi daga malaman tafsiri na shi’a, shi lauhul mahfuz kinaya ce kan ilimin Allah kuma da haka nema a iya hukunta shi da wani abu daga mada ko ma’anawi (Misalin zarafi, shafi ko wani keɓantacce waje ba)[15] amma Muhammad Taƙi Yazdi marubucin littafin Kur’an shinasi ya na ganin rashin ingancin wannan magana, bisa la’akari da kalmomin da kuir’ani ya zo da su kan lauhul mahfuz misalin (Ummul Kitabi) da take da ma’anar asalin abu a wurinsa, ya tafi kan cewa shi lauhul mahfuz bai kasance ainahin zatin Allah ba, bari dai shi halitta ne daga halittun Allah,[16] wasu ba’arin masu bincike game da haƙiƙar lauhul mahfuz sun kawo ra’yoyi guda shida[17] an ce amfani da kalmar allo ko alƙalami sun zo daga babin kusanto da ma’ana zuwa ga kwakwale daga babin tashbihi ko tanzili, bai kamata a ƙiyasta shi tare da alƙalami da takarda ko litattafai da aka saba da su.[18]

Lauhul Mahfuz a Mahangar Falsafa da Irfani

Wasu ba’ari daga masana falsafa suna ɗora lauhul mahfuz kan Aƙlul Fa’al, Jibrilu[19] ko Naful Kulli (Gamammen rai), Falakul A’azam da dukkanin halittu ke kasancewa ƙarƙashinsu.[20] cikin duniyar ilimin irfani, an gabatar da alƙalami matsayin tushen lauhul mahfuz[21] Muhyiddini Ibn Arabi daga shahararrun Sufaye, ya yi imani kan cewa Allah yana samar da iliminsa dunƙule game da halittu da kuma alƙalami a faifaice cikin lauhul mahfuz,[22] tare da haka wasu ba’arin masu bincike suna ganin ɗora lauhul mahfuz kan wasu ma’anoni na falsafa misalin Jauharul mujarrad ki Aƙlul Fa’alul Awwal matsayin wani abu da ya saɓa da zahirin shari’a kuma babu dalili na kur’ani ko riwaya kansa.[23]

Hususiyar Lauhul Mahfuz

Mafi muhimmancin lauhul mahfuz shi ne kasancewarsa ya tattaro komai da komai.[24] kamar yanda ya zo cikin riwaya haƙiƙa ɗaukacin labarurruka da abubuwa da za su faru a duniya, an rubuta su tare da alƙalami a cikin lauhul mahfuz,[25] haka nan cikin riwaya, haƙiƙa an yi bayanin ba’arin hususiyoyinsa na zahiri misalin kasancewar kyawuntarsa kamar dutsen zumurrud.[26] wanda Allama ɗabaɗaba’i yake cewa wannan hususiya wani nau’i ne na misali da yake hakaito surar lauhul mahfuz daidai da yanda kwakwalen mutane za su iya ɗauka.[27]

Kaiwa zuwa ga Lauhul Mahfuz daga wanda ba Allah ba

Ba’arin masu bincike tare da dogara da ayoyin kur’ani sun tafi kan cewa haƙiƙa ba’arin keɓantattun mutane za su iya tsinkaye kan lauhul mahfuz,[28] waɗannan malamai tare da jingina da ayoyi 77-79 daga suratul waƙi’a [tsokaci 1] da kuma aya ta 33 daga suratul Ahzab [tsokaci 2] haƙiƙa Ma’sumai sha huɗu suna daga cikin mutane da yanke tabbas suna yin tsinkaye kan lauhul mahfuz,[29] Sayyid Ali Milani masanin ilmin kalam na shi’a shima ya tafi kan cewa wasu ba’arin riwayoyi ana iya dogara da su kan cewa kai tsaye A’imma suna tsinkaye kan lauhul mahfuz,[30] Allama ɗabaɗaba’i shima ya fassara ilimin gaibun Annabawa da Imamai matsayin tsinkaye daga kan lauhul mahfuz.[31] Tare da haka kan asasin ba’arin wasu riwayoyi, ya zo cewa babu wani mutum hatta Annabawa da Imamai da zai iya tsinkaye kan lauhul mahfuz, haƙiƙa ya keɓanta da Allah shi kaɗai.[32] Muhammad Hadi Marifa shima tare da jingina da riwayar Imam Sadiƙ (A.S) ya tafi kan cewa haƙiƙa Annabawa da Imamai basu da tsinkaye kan lauhul mahfuz.[33]

Rashin Cin Karon Lauhul Mahfuz Tare da Zaɓin Mutane

A cewar masu zurfafa bincike na muslunci, rubuta ɗaukacin abubuwa cikin lauhul mahfuz, bai da ma’ana tilastawa mutum,[34] Misbahu Yazdi cikin littafin Khodashinasi, ya yi bayani cewa rubutu ɗaukacin abubuwa daga jumlarsu ayyukan mutum cikin lauhul mahfuz baya cin karo da zaɓin mutum kan ayyukansa,[35] cikin amsar da ya bayar kan tambaya da aka yi masa, ya yi imani kan cewa rubuta ɗaukacin ayyukan mutum cikin lauhul mahfuz baya nufin tilasta mutum kan wannan ayyuka, saboda ayyukan mutum an rubuta su cikin wannan allo, suna faruwa ne da yanayin faruwarsu cikin zaɓinsa, kuma shi ilimin Allah baya canja haƙiƙa.[36] kamar dai misalin malami da yake da tsinkaye kan hazaƙar da kaifin basirar ɗaukacin ɗalibansa kuma ya san wanda zai nasara a jarrabawa da wanda zai faɗi tun gabanin jarrabawa.[37]

Bayanin kula

  1. Kalantari, "Loh Mahfouz", shafi na 119.
  2. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 10, shafi na 138
  3. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 18, shafi na 84.
  4. Dehghani, wa digaran, "Ma'ana shinas Loh Mahfouz a cikin Kur'ani", shafi na 6.
  5. Majlisi, Mir'ah al-Aqool, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 132
  6. Sobhani, Ma’al Shi’a al-Imamiyah fi Aqeedhim, 1440 AH, shafi na 144-145.
  7. Qolizadeh, wa Tavakoli, "barasi tadbiki cisti Loh Mahfuz's wa Wijegihaye an dar Al-Mizan wa Majmael Al-Bayan", shafi na 185.
  8. Majlisi, Mir'ah al-Aqool, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 132.
  9. Abdul Baqi, Al-Mu'jam al-Mufhars, 1364H, shafi na 653.
  10. Suratul An'am, aya ta 59.
  11. Suratul Waki'eh, aya ta:78.
  12. Suratul Zakharf, aya ta 4.
  13. Duba: Marafet,Al- Tamhid, 1428 AH, juzu'i na 3, shafi.34; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 26, shafi.354; Sobhani, Ma’al Shi’a al-Imamiyah fi Aqiedhim, 1440 AH, shafi 144.
  14. Kalantari, "Loh Mahfouz", shafi na 121.
  15. Marfat, Al-Tamhid, 1428 AH, juzu'i na 3, shafi na 34; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 26, shafi.354.
  16. Masbah Yazdi, Khodashinasi, 2016, shafi na 485. ↑
  17. Kalantari, "Loh Mahfouz", shafi na 122.
  18. Jafari, "Bahasi darbaraye Lauhul Mahfuz wa Lauhul mahawi wa isbat", shafi 85.
  19. Tahouni, Keshaf Istilahat al-Funun wa Uloom, 1996, juzu'i na 2, shafi na 1416.
  20. Mulla Sadra, Al-Hikma al-Mu’taaliyyah, 1981, juzu’i na 6, shafi na 295.
  21. Zamani, “Jayiga Lauhu wa qalam dar Jhan shinasi irfani Ibn Ibn Arabi wa Attar Neishaburi”, shafi na 119.
  22. Ibn Arabi, al-Tadbirat al-Ilahiya, 1424H, shafi na 108.
  23. Ansari, "Loh Mahfuz", shafi 1940.
  24. Qolizadeh, wa Tavakoli, "Barasi Tadbiki cisti lauhu wa wijagahye an dar Al-Mizan da Majmael Al-Bayan", shafi na 189.
  25. Sheikh Sadouq, Ilalul Ash-Shara'i, 1385, juzu’i na 1, shafi na 19.
  26. Sheikh Mufid, Al-IKhtissas, 1413H, shafi na 49.
  27. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi na 170.
  28. Ghoruyan, wa digaran,bahasi mabsut dar Amuzeshi Akayid , 1371, juzu'i 1, shafi na 255-256.
  29. Ghoruyan, wa digaran,bahasi mabsut dar Amuzeshi Akayid , 1371, juzu'i 1, shafi na 255-256.
  30. Hosseini Milani, tBa Pishwayan Hidayetgar 2009, juzu'i.4, shafi na 198.
  31. Tabatabai, Barasihaye Islami, 2008, juzu'i na 1, shafi 195.
  32. Safar, Basair al-Derajat, 1404 AH, shafi na 109-110.
  33. Ma'raft, al-Tafsir wa al-Mufassirun, 1425 AH, juzu'i na 1, shafi na 513.
  34. Mesbah Yazdi,Khodashinasi 1396, shafi na 487-488.
  35. Mesbah Yazdi,Khodashinasi 1396, shafi na 487
  36. Mesbah Yazdi,Khodashinasi 1396, shafi na 487-488.
  37. Tehmursi, "Loh Mahfouz", shafi na 533.

Nassoshi

  • Abdul Baqi, Muhammad Fouad, Al-Mu'aqim Al-Mufars na Al-Faz Al-Qur'an Al-Karim, Alkahira, Dar Al-Kitab al-Masriya, 1364H.
  • Ansari, Masoud, "Loh Mahfouz", a juzu'i na biyu na karatun Alqur'ani da Qur'ani, Tehran, Dostane da Nahid, 1377.
  • Ghoruyan, Mohsen, wa digaran, Bahasi mabust dar Amuzehsi Akayid, Qom, Darul Alam, 1371.
  • Hosseini Milani, Seyyed Ali: Ba Pishvayan Hedayatgar, Qom, Al-Haqaq, 2009.
  • Ibn Arabi, Al-Tadbirat al-Ilahiyyah fi Isharah al-Mulkama al-Husaniyyah, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1424H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir bin Mohammad Taqi, Mir'ah al-Aqool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul (AS), Tehran, Darul Katb al-Islamiyya, 1404H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1374.
  • Marafet, Mohammad Hadi, Al-Tafseer wa Al-Mufassirun Fi Thobha Al-Qashib, Mashhad, Razavi University of Islamic Sciences, 1425 AH.
  • Mesbah Yazdi, Mohammad Taqi, Khudashinasi, Kum, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (RA), 1396.
  • Mulla Sadra, Muhammad bin Ibrahim, Al-Hikmah al-Muttaaliyyah fi al-Asfar al-Uqliyyah al-Arabah, Sharhin: Muhammad Hossein Tabatabai, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1981.
  • Safar, Muhammad bin Hasan, Basair al-Darajat fi Fadael al-Muhammad (a.s), Kum, Laburare Ayatullah Murashi Najafi, 1404H.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-IKhtisas, Kum, Al-Khangir al-Alami na Alfiya Al-Sheikh Al-Mufid, 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ilalul Shara'i, Qum, Davari, 1385.
  • Sobhani, Jafar, Ma al-Shi’a al-Amamiyyah fi Aqeedham, Qum, Imam Sadiq Institute (AS), 1440H.
  • Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Qur'an, Qom, Islamic Publications Office, 1417 AH.
  • Tabatabai, Mohammad Hossein,Barasihaye Islami, edited by: Seyyed Hadi Khosrowshahi, Qom, Bostan Kitab, 2008.
  • Tahouni, Mohammad Ali, Keshaf Istilahat Al-Funun da Uloom, Beirut, Lebanon Publishers School, 1996.
  • Tehmursi, Ramin, "Loh Mahfouz", a Juzu'i na 14 na Encyclopaedia na Shi'i, Tehran, Hikmat, 2013.
  • جعفری، «بحثی درباره لوح محفوظ و لوح محو و اثبات»، در مجله کلام اسلامی، شماره ۳۴، تابستان ۱۳۷۹ش.
  • قلی‌زاده، رضا، و محمدجواد توکلی، «بررسی تطبیقی چیستی لوح محفوظ و ویژگی‌های آن در المیزان و مجمع البیان»، در مجله تفسیر پژوهی، شماره ۱۷، بهار و تابستان ۱۴۰۱ش.
  • کلانتری، ابراهیم، «لوح محفوظ»، در مجله مقالات و بررسی‌ها، شماره ۸۳، پاییز و زمستان ۱۳۸۳ش.
  • Mohammad Hadi, Talmhid fi Ulum al-Qur'an, Qum, Talmhid, 1428H.

دهقانی، فرزاد، و دیگران، «معناشناسی لوح محفوظ در قرآن»، در مجله ذهن، شماره ۷۳، بهار ۱۳۹۷ش.