Khula ɗiyar Manzur

Daga wikishia
domin gujewa dimauta ku duba: Khaula

Khula ɗiyar Manzur bin Zabban Fazari,(Larabci:خولة بنت منظور بن زبّان الفزارية) matar Imam Hassan Mujtaba (a.s) kuma mahaifiyar Hassan Musanna, Ita ce matar farko ga Muhammad bin ɗalha, wanda aka kashe a yaƙin Jamal, sannan ta zama matar Imam Hasan Mujtaba (a.s)[1] Mahaifiyar Khaula ita ce Malikah diyar Ibn Sinan.[2] Rahoton ya ce, bayan kashe mijin Khola na farko Muhammad BN ɗalha, Abdullahi ɗan Zubair, mijin ‘yar uwar Khola, ya nemi aurenta ga Imam Hassan (a.s) a yayin da mahaifin Khola ba ya nan, sai Imam ya amince. An ce, lokacin da mahaifinsa ya gane haka, sai ya ji haushi da farko, amma daga ƙarshe ya yarda, .[3] amma masanin tarihin nan Baƙir Sharif ƙarshi (ya rasu: 1433H) ya yi tardidi kan ingancin wannan labari, yana ganin hakan ba ana sone a ragewa imam matsayi a jingina masa wani abu da ba haka ba ,kuma ya kawo saidun wajan ƙaryata labarin.[4] wasu suna ganin bayan wafatin imam Khula ta karɓi saki kafin nan ko ita ta mutu kafin shahadar tasa.[5] wasu na ganin tayi auren da Abdullahi bin Zubair bayan shahadar Imam.[6]

Amma a cewar Baƙir Sharif ƙurashi, Khula matar Imam ce har zuwa ƙarshen rayuwarsa, kuma ba ta yi aure ba bayan shahadar Imam.[7] A cikin littafin Al-Amali fil-Mushiklat al-ƙur'aniyya wal-Hukm wal-ahadis al-Nabawiyya na Abdul Rahman Bin Ƙasim (ya rasu: 339 bayan hijira), an bayyana cewa Khula ta kasance cikin tsananin damuwa a lokacin shahadar Imam Hasan. har mahaifinta Manzur ya rubuta mata waƙoƙi don kwantar mata da hankali .

Jiya na gano cewa Khula tana kuka da musibar zamani da ta hau mata, Ya ke Khula! Kada ki yi baƙin ciki kuma ki yi haƙuri domin ma'abuta daraja sun dogara da haƙuri. Haka kuma Khula ta haifi ‘ya’ya uku da Muhammad bin ɗalha(mijinta na farko) , mai suna Ibrahim, da Dawud da Ummu ƙasim.[8]

Bayanin kula

  1. Abolfaraj Esfahani, Al-Aghani, 1415 Hijira, juzu'i na 12, shafi na 408.
  2. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1397 AH, juz.3, shafi na 72.
  3. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1397 AH, juz 3, shafi na 24-25.
  4. ƙureshi, Hayat al-Imam al-Hasan, Dar al-Balagha, juzu'i na 2, shafi na 457.
  5. Duba Abul Faraj Isfahani, Al-Aghani, 1415H, Mujalladi na 12, shafi na 409.
  6. Duba ƙurashi, Hayat al-Imam al-Hasan, Dar al-Balaghah, juzu'i na 2, shafi na 457.
  7. ƙureshi, Hayat al-Imam al-Hasan, Dar al-Balagha, juzu'i na 2, shafi na 457.
  8. Abolfaraj Esfahani, Al-Aghani, 1415 Hijira, juzu'i na 12, shafi na 408.

Nassoshi

  • Abul Faraj Isfahani, Ali bin Hossein, Al-Aghani, Beirut, Dar Ahya Al-Trath Al-Arabi, 1415H/1994 Miladiyya.
  • Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf (Juzu'i na 3), Bincike: Mohammad Baƙer Mahmoudi, Beirut, Dar al-Taraif na Jarida, 1977/1397.
  • ƙurashi, Baƙer Sharif, Hayat Imam al-Hasan bin Ali (a.s), nazari da nazari, Dar al-Balagha, Beta.
  • Zajj, Abdul Rahman bin ƙasim, al-Amali fi al-Mashkilat al-ƙur'an da al-Hukm da hadisin annabci, Sharhin: Ahmad bin Amin Shenƙiti, Egypt, al-Maktab al-Mahmoudi al-Tajjariyah, bugu na biyu, 1354 AH/1935 AD.