Kashe Habila
Kisan Habila (Larabci:مقتل هابيل) yana ɗaya daga cikin ƙissosin Alƙur'ani da suke nuni da kashe ɗaya daga cikin 'ya'yan Annabi Adam guda biyu da ya faru a hannun ɗan uwansa, a majiyoyin addini, ana ɗaukar wannan lamarin a matsayin ƙisa na farko da aka yi wa dan Adam a doron ƙasa. An ce Ƙabilu ya yi adawa da maye gurbin Habila a matsayin halifan Adam, kuma domin a kawo ƙarshen wannan rikici, wahayi ya zo daga Allah cewa kowannensu ya yi hadaya wato ya yi yanka domin neman yardar Allah, sai dai kuma bayan wannan hadaya da suka bayar, sai ya zamana Allah bai karɓi hadayar Ƙabilu ba, saboda haka ƙabilu ya yi hassada ga ɗan'uwansa Habila game da batun naɗa magajin Adam, kuma ya kashe shi, Kamar yadda aya ta 31 a cikin suratul ma'ida ta bada labari, Allah ya koyawa Ƙabilu yadda zai binne Habila ta hanyar turo da hankaka domin ya koyar da shi.
Mutum Na Farko Da Aka Fara Kashewa A Doran Ƙasa
Habila ya kasance mutum na farko da aka fara kashewa a doran ƙasa,[1] Aya ta 27 zuwa ta 31 a cikin suratul ma'ida ta yi bayani game da labarin kashe Habila, kamar yadda Allah ya faɗa a cikin waɗannan ayoyin cewa ƴaƴan Annabi Adam guda biyu sun yi wani abu don neman kusanci zuwa ga Allah, kuma hakan ya samu karɓuwa a wajen Allah. ɗaya daga cikinsu kuma bai yarda da ɗayan ba. Don haka ɗan uwan da ba a karɓi aikin shi da sadakarshi ba ya yi wa ɗayan barazana cewa zai kashe shi, ya kuma rantse zai kashe shi, kuma ya kashe shi[2] Bisa maganar malaman tafsiri wanda ya yi kisan shi ne Ƙabilu, wanda kuma aka kashe shi ne Habilu.[3]
Abin da Ya Sanya Ƙabila Kashe Habila
Ya zo a riwaya cewa hassada ce babban dalili da ta angiza Ƙabilu ya kashe Habila lokacin da aka naɗa shi magajin Annabi Adam.[4] Bisa abin da wasu masu bincike suka faɗa, a lokacin da Allah ya yi wahayi ga Adam domin ya sanar da Habilu Ismul A'azam a matsayin shi na Halifa bayan Annabi Adam, sai Ƙabila ya nuna rashin jin daɗinsa kan haka, a matsayin shi na babban ɗa ga Annabi Adam wanda haka ya sa yake ganin shi ne wanda yafi kowa cancanta ya zama magajin babansa, kuma a hannu ɗaya Ƙabilu yana ganin cewa Adam ya zaɓi Habila a matsayin halifanshi kawai saboda alaƙar shi ta masamman da Habila ba Allah ba ne ya umarce shi da hakan ba, domin ƙoƙarin kawo ƙarshan wannan danbarwa sai Allah ya saukar da wahayi cewa dole ne kowa a cikin su ya yi yanka na sadaka domin neman yardar Allah.[5]
Yadda Kashe Habila Ya Gudana
Daidai da abin da ya zo a ruwayoyi, haƙiƙa Ƙabilu ya kasance manomi, kuma ya yi hadaya da mafi munin amfanin gonakinshi, shi kuma Habila ya kasance makiyayi, sai ya sadukar da ɗaya daga cikin mafi kyawun abin da yake kiwatawa domin hadaya, idan hadaya taƙone alama ce ta amincewar Allah, sai Allah ya karɓi hadayar Habila, bai karɓi hadayar Ƙabilu ba.[6]
Hasssada Ita ce Dalilin Da Ya Sanya Ƙabilu Kashe Habila
Kamar yadda ruwayoyin musulunci suka yi bayani, bayan Allah ya karɓi hadayar Habila, sai hassadar Ƙabilu ta motsa, ya yi rantsuwa da Allah sai ya kashe Habila.[7] bisa abin da ya zo a ayoyin ƙur'ani haƙiƙa Habila ya tattauna tare da Ƙabilu yana ishara zuwa ga taƙawa ya ce mashi haƙiƙa Allah yana karɓar abu ne daga masu tsoranshi, Idan kana son kashe ni, ba zan yi yunkurin kashe ka ba, kuma ba zan aikata hakan ba. Ya kuma gargaɗi Ƙabilu da cewa idan ya aikata laifin kisan kai, zai yi zalunci kuma ya cancanci shiga wutar jahimu.[8] Bisa abin da ya zo cikin Littafin Tarikhu Ɗabari wanda aka rubuta a shekara ta 303 bayan hijira, a lokacin da Habilu ya tafi dutse domin kiwon dabbobi kawai sai Ƙabilu ya kai mishi hari dai-dai lokacin da yake hutawa, ya buga mishi dutse a kan shi ya kashe shi.[9]
Wasu sun ce dalilin da ya kawo haifar da hassada da ta kai ga yanka shi ya samo asali ne daga batun zaɓar mata da ƴan uwan biyun za su yi, kuma sun ce an umurci Habila da ya auri ƴar uwar Ƙabilu wanda suke tagwaye ne domin aiwatar da umurnin da Allah ta'ala da ya yi wa Adam, kazalika an umurci Ƙabilu da ya auri ƴar tagwayen Habila, sai Ƙabilu ya ce bai yarda da umarnin da mahaifinsu ya bashi, saboda ƴar uwarshi tafi ƴar uwar Habilu kyau, Sai Allah ya umurci ƴan uwan biyu da su yi hadaya, kuma duk wanda aka karɓi hadayarshi, to shi ne zai auri ƴar uwar Ƙabilu, sai aka karɓi hadayar Habila, sai Ƙabilu ya yiwa Habilu hassada, ya buga mishi dutse, nan take ya kasheshi.[10] A cikin Attaura an anbaci ƙissar Habilu ta sadaukarwarsa da Ƙabilu da yadda ya kashe Habila.[11]
Binne Gawar Habilu
Bisa abin da Muhammad ɗan Jarir Ɗabari malamin tarihi a ƙarni na uku ya anbata, gawar Habila ta kasance a cikin haɗari sakamakon dabbobi masu cin naman mutane, saboda Ƙabilu bai san yadda ake wa gawa sutura ba, bai san yadda zai binne gawar mutumin da ya mutu ba.[12] Bisa abin da ya zo a aya ta 31 cikin suratul ma'ida, Allah ya tura Hankaka domin ya koyawa Ƙabilu yadda ake binne gawar mamaci, sai Hankaka ya nemi inda ƙasa take ya haƙa rami ya binne wani Hankaka da ya mutu, a wani labarin an ce ya haƙa rami ya ɓoye wani sashi na abincinshi, tab haka ne Ƙabilu ya fahimci yanda zai binne gawar ɗanu wanshi da ya kashe.[13]
Bayanin kula
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 3, shafi na 669.
- ↑ Imzar: Suratul Ma’idah, aya ta 27-31.
- ↑ Sheikh Al-Tusi, Al-Tibyan, juzu'i na 3, shafi na 492; Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 5, shafi na 315; Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 3, shafi na 672.
- ↑ Al-Ayyashi, Tafsirin Al-Ayyashi, juzu'i na 1, shafi na 312.
- ↑ Sadiƙi Fadaki, Irtidad; Bazgasht Beh Tariki, shafi na 270.
- ↑ Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 113.
- ↑ Al-Ayyashi, Tafsirin Al-Ayyashi, juzu'i na 1, shafi na 312.
- ↑ Suratul Ma'idah, aya ta:29.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh Al’umam wa al-muluk. juzu’i na 1, shafi na 138
- ↑ Sheikh Al-Tusi, Al-Tibyan, juzu'i na 3, shafi na 493; Al-Tabari, Tarikh Al’umam wa Al-muluk, juzu’i na 1, shafi na 138.
- ↑ Attaura, Sifrul Takwin, Babi na 4, ayoyi 3-8.
- ↑ Tabari, Tarikh Al'umam wa Al-muluk, juzu'i na 1, shafi na 86.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 3, shafi na 675.
Nassoshi
- Al-Ayyashi, Muhammad bin Mas'ud, Al-Tafsir (Tafsir Al-Ayyashi), edited by: Hashim Rasouli, bugun farko, Tehran, Islamic Scientific Library, 1380 AH.
- Al-Kulayni, Muhammad bin Yaƙoub, Al-Kafi, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
- Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al'umam wa al-muluk, bugun: Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, bugun na biyu, Beirut, Darul-Turath, 1387H.
- Al-Tabatabai, Al-Sayyid Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir Al-ƙur’an, bugu na biyu, Beirut, Al-Alami Publications Foundation, 1390 AH.
- Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, Al-Tibyan fi Tafsir Al-ƙur’an, Beirut, Dar Ihya Al-Tarath Al-Arabi, (ed.).
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsiri kitabillahil al-munazzal i, ƙum, Madrasatul Imam Ali bin Abi Talib, bugun farko, 1379H.
- Sadiƙi Fadaki, Jaafar, Irtidad, Bazgasht Bih Tariki; negareshi be maudu'i irtidad az negahe kur'an kareem, bugu na farko, ƙum, Babbar Cibiyar Kimiyya da Al’adun Musulunci, 1388H.