Karatun Juzu'i-juzu'i
Karatun juzu'i-juzu'in Alkur'ani (Larabci: قراءة جُزء من القرآن) shi ne karatun kur'ani juzu-i-juzu'i, yawanci yana daukar nau'i na zama da gungun mutane ke halarta. Wannan hanya ta zama ruwan dare a cikin watan Ramadan da kuma zaman karatun kur'ani a gida, da ma tarukan Fatiha da tunawa da matattu. a ƙarshen ƙarni na ɗaya ne ko na biyu bayan hijira Aka raba Alkur'ani zuwa kashi 30.
Yadda Ake Karatun Juzi'i-juzu'i
A wajen taron karatun kur'ani mai tsarki ana karanta wani bangare ko fiye da haka, kuma wadanda suke wurin suna saurare ko karantawa tare da murya ƙasa-ƙasa[1] wannan hanya ta bazu sosai a watan ramadan.[2] A zaman karatun kur'ani a gida da ma tarukan Fatiha da tarukan tunawa da matattu, inda ake rarraba kur'ani mai kunshe da sassa talatin domin duk wanda ya halarta ya karanta wani bangare ko sashinsa, da kuma saboda haka ana karanta kur'ani sau daya ko fiye da haka.[3] haka nan ana yin karatun kur'ani ta hanyar dandalin sada zumunci na fasahar zamani. [4]
Saukar Alƙu'ani
- Tushen ƙasida: Saukar Kur'ani
daga cikin salo da ya yi matuƙar yaɗuwa cikin sauke bakiɗayan Alkur'ani akwai salon karanta juzu'i-juzu'i daga kur'ani, kuma a wasu majalisu da ake gudanarwa a gidaje ko masallatai, ko wane mutum ya na karanta kashi ɗaya ko fiye da haka a cikin ko wace rana a watan Ramadan idan ya zama ana karanta juzu'i ɗaya za a sauke kur'ani cikin kwanakin talatin.[5] A kudancin Iran ana kiran wannan hanya ta sauke kurani cikin kwanaki 30 da suna karatun muƙabala.[6] ana gudanar da tarukan karatun kur'ani a ƙasashe daban-daban a cikin watan Ramadan, kuma ana watsa wannan shiri kai tsaye a tashohin talabijin daga wurare masu tsarki, kamar makwancin Imam Husaini (A.S)[7] da kuma hubbaren Imam Rida (A.S).[8]
Rarraba Alƙur'ani Zuwa Juzi'i-juzi'i
An raba Alkur'ani zuwa juzi'i talatin a cikin ƙarni na farko ko na biyu bayan hijira, Wannan ya faru ne saboda sauƙaƙa karatunsa da haddace shi da koyan shi,[9] Ana jingina wannan rabawar zuwa ga Hajjaju ɗan Yusuf As-saƙafi,[10] Da kuma Mamun Abbasi.[11] Zarkashi, ɗaya daga cikin masu tafsiri a ƙarni na takwas bayan hijira, ya ambaci cewa kasa Kur'ani zuwa kashi 30 ya faru a makarantun addini.[12]
A wasu ƙasashen musulmi kamar Iran, an buga wasu kur'anai daban, waɗanda suka ƙunshi juzi'i talatin, ana amfani da su wajen taron majalisan Fatiha da sauransu.[13]
Bayanin kula
- ↑ «بهترین شیوه قرائت قرآن کریم در ماه رمضان»، باشگاه خبرنگاران جوان.
- ↑ Moini, "Juz", shafi na 836.
- ↑ موسوي آملي، «شناخت قرآن؛ قرآن در مراسم ختم». پایگاه اطلاعرسانی حوزه.
- ↑ "Katmul Kur'ani", mujallar Nasim Wahi, lamba 7.
- ↑ "Katmul Kur'ani", Mujallar Nasim Wahi, lamba 7.
- ↑ «مقابله آیین سنتی قرآن خوانی مردم بوشهر در ماه مبارک رمضان»، خبرگزاری شبستان.
- ↑ «نفحات القران الكريم تمتزج مع نسائم شهر رمضان عند مرقد الامام الحسين (ع).. اكثر من (1000) شخص يشاركون في الختمة القرآنية (يوميا)»، موقع العتبة الحسينية المقدسة.
- ↑ «زمان پخش ترتیل جزءخوانی قرآن کریم شبکههای سیما»
- ↑ Majmu'atu Min Al-Muhaqqin, Farhangenameh Ulumi qur'ani, shafi na 481-482
- ↑ Al-Faiz Al-Kashani, Al-Mahajja Al-Bayda, juzu'i na 2, shafi na 224.
- ↑ Marefati, At-tamhid, juzu'i na 1, shafi na 364.
- ↑ Al-Zarkashi, Al-Burhan, juzu'i na 1, shafi na 250.
- ↑ Dehkhoda, Lugatanameh Dehkhoda, zaile wajeh Sipareh.
Nassoshi
- Al-Zarkashi, Muhammad bin Abdullah bin Bahadur, "Al-Burhan Fi ulumi Kur'ani", Bincike: Muhammad Abol-Fazl Ibrahim, Beirut, Dar Al-Jil, 1408H/ 1988 Miladiyya.
- Alfiz al-Kashani, Muhammad bin Mortaza, "Al-Mahajja Al-Bayda fi Tahdeeb al-Hiyaa", Qom, Al-Nashar al-Islami, Juzu'i na 2, 1428H.
- «بهترین شیوه قرائت قرآن کریم در ماه رمضان»، باشگاه خبرنگاران جوان، تاريخ الإدراج: 07/ 02/ 1399 ش، تاريخ المشاهدة: 11/ 01/ 1403 ش
- "Katma Al-Qur'ani", "Mujallar Nasim Wahi", Qum, Jama'at al-Qur'an al-Karim, No. 7, 1386.
- Dehkhoda, Ali Akbar wa Akhroon, "Lugatnameh", Tehran, Jami'ar Tehran, 2019.
- "Katma Al-Qur'ani", "Mujallar Nasim Wahi", Qum, Jama'at al-Qur'an al-Karim, No. 7, 1386.
- Dehkhoda, Ali Akbar wa Akhroon, "Lugatnameh", Tehran, Jami'ar Tehran, 2019.
- Marafa, Mohammad Hadi, "Al-Tamehid", Qum, Al-Nashar Islamic Publishing House, Juzu'i na 1, 1412 AH.
- Moeini, Mohsen, ""Jaz", Daneshnameh Quran wa Quran Pajuhi, Tehran, Dostan Publishing and Nahid Publishing, 1377.
- «مقابله آیین سنتی قرآن خوانی مردم بوشهر در ماه مبارک رمضان»، خبرگزاری شبستان، تاريخ الإدراج: 30/ 03/ 1395 ش، تاريخ المشاهدة: 11/ 01/ 1403 ش.
- موسوي آملي، محسن، «شناخت قرآن؛ قرآن در مراسم ختم». پایگاه اطلاعرسانی حوزه، تاريخ الإدراج: 1390/08/08 ش، تاريخ المشاهدة: 11/ 01/ 1403 ش.
- «نفحات القران الكريم تمتزج مع نسائم شهر رمضان عند مرقد الامام الحسين (ع).. اكثر من (1000) شخص يشاركون في الختمة القرآنية (يوميا)»، موقع العتبة الحسينية المقدسة، تاريخ الإدراج: 05/ 04/ 2022 م، تاريخ المشاهدة: 02/ 04/ 2024 م.