Jump to content

Imani Da Mau'ud

Daga wikishia

Imani da Mau'ud (Larabci: الإيمان بالموعود) yana nufin Imani da bayyanar mai ceto wanda zai bayyana a ƙarshan zamani domin ceton mutane daga zalinci da ƙara tabbatar da musluncida adalci. Wannan aƙida ta zuwan mai ceto, wanda aka yi alƙawarin zuwanshi, wannan ba sabuwar magana bace, tuntuni akwaita a gun mutane daban-daban da kuma addinai mabanbanta, da kuma yanayi dabana-daban cikin mabambantan al'adu, kamar yadda akwai tarayya tsakanin dukkan mutane cewa sun yi ittifaƙi kan wani abu guda ɗaya shi ne cewa wata mai ceton da aka yi alƙawarin zuwanshi zai bayyana domin ya `yantar da mutane daga mulkin kama-karya da zalinci, bayan haka mutane za su rayu cikin adalci da gaskiya, kamar yadda a addini `yan Hindu za ka ga cewa suma suna da aƙidar jiran mai ceto, suna kiran shi da "Fishinu" ko "Kaliki" kuma a gun su shi ne mutum na goma mai bayyana Allah. Kazalika abin yake a addini `yan Buda suma suna kiran shi da mai ceton da aka yi alƙawari sunan shi "Bunisatafa", amma a gurin Yahudawa suna jiran "Almashihu", su kuma Kiristoci suna jiran "Faraƙalid" wannan suna yana nuni ga Annabi Isa (A.S) wanda shi ne ya yi Bushara da dawowarshi, amma su musulmi sun yi Imani ne da bayyanar Mahadi (A.S).

Bayani kan Imani da wanda aka yi Albishir Da Zuwanshi

Imani da Mahadi yana nufin Imani da wani mutum mai ceto da zai zo a ƙarshan zamani, wanda zai zo domin ceton mutane da `yanto su tare kuma da tabbatar da muslunci da adalci a tsakanin mutane,[1] wannan aƙida ta bayyanar Imam Mahadi aƙida ce wacce mutane da addinai suka yi Imani da ita ta fuska daban-daban, tare wannan bambance-bambance duk sun yi ittifaƙi da wannan mutum mai ceto mutane daga mulkin kama karya da zalinci kuma shi ne wanda zai tabbatar da adalci a tsakanin mutane.[2]

Imani Da Mau'ud A Tsakanin Makarantun Addinai

Imani da wanda ak ayi alƙawarin zuwanshi haƙiƙa ce wacce addinai duk da bambancinsu sun yi magana a kanshi, kuma Imani da wanda ake jira yana cikin aƙida ta asali cikin addinai, kamar yadda wasu masu bincike suka ce zai wahala ka sami wani addini ko mazahaba ko wasu mutane, ba tare da Imani da zuwan wani mai ceto ba.[3]

Aƙidar Imani Da Mau'ud A Cikin Addinan Gabashin Duniya

A mahangar Addinin Hindu: mai ceto a gurinsu ana kiran shi da "Kalili" shi Kaliki shi ne wannan mutumi da zai bayyana a ƙarshan daura daga daurori guda huɗu da duniya za ta yi,[4] Bisa abin da masu addini Hindu suke gani cewa ita duniya za ta yi zamani na ɓarna da rashin ci gaba, cikin daurori guda huɗu, amma a ƙarshan daura ta huɗu zalinci da barna zai mamaye duniya gaba ɗaya, kuma wannan lokacin shi ake kira da Kali Yuga, kuma a wannan lokacin ne abubuwa za su yi muni sosai. Lokacin da duniya za ta shiga wannan hali, zai zama wannan yanayi ya haifar da wani yanayi na fita daga zalinci.[5]

  • Bisa aƙidar Mabiya addinin Hindu: wannan lokaci zamani ne na duhu da zalinci (Kaliki Yuga) ya fara tin daga shekara ta 3102 daidai da ranar 17 ko 18 ga wata Fabrairu shekarar Miladiyya a tsakiyar dare, mu a yanzu muna rayuwa ne a cikinshi, ba a yin aiki da addini da aƙida sai gwargwadon rubu'i, sannan kashi uku cikin huɗu na aƙida an manta da shi, kuma daga cikin abubuwan da wannan daura ta huɗu ta keɓantasu akwai yawan yin saɓo da tawaye, saboda mutane a wannan lokacin duk talakawa ne, kuma suna shan azaba, kuma hakan shi ne ya sabbaba musu rashin samun damar aikata wani abu, sai bibiyar abin da bashi da muhimmaci, idan za su ci wani abu sai su yi haɗama, ɓarayi sun cika garuruwan da suke rayuwa cikinsu,[6] bisa ra'ayin addinai da falsafa na indiya,[7] a ƙarshan lokacin duhu da zalinci shi ne lokacin bayyanar mutum na goma kuma na ƙarshe wanda ake kira (Autara) da ubangiji mai suna (Fishinu) ko Kaliki wanda zai zo a yanayin mutum kan wani farin doki a hannunshi a kwai Takobi tana kyalli kuma zai kawar da duhu, za a samu lafiya ko'ina, zai mayar da komai dai-dai kamar yadda ya kamata ya kasance.[8]
  • A mahangar addinin Buda: aƙidar mai ceto an gina ta kan wannan kalma (مايتريا) wacce take nufin abin so da ƙauna kuma shi(Mayitiriya) shi ne Buda na biyar a aƙidar `yan Buda,[9] kuma shi ne Buda na ƙarshe a duniya kuma har yanzu bai bayyana ba, a nan gaba zai bayyana domin ya ceci mutane daga zalincin da ake yi musu, ana yin hotan Buda na biyar a matsayin wani mutum a zaune wanda yake yunƙurin tashi, shi wannan hoto yana nuna matsayin wanda yake shirye tsaf domin tashi don ya ceci al'umma!

Akwai baMbanci cikin maganar `yan addinin Buda kan bayanin mutumin da zai ceci a'lumma da kuma yanayin bayyanarshi, ko mutum na ƙarshe wanda zai zo da bushara ta ceton da mabiya addinin Buda, wanda zai ceci al'umma daga wannan rayuwar da ake ciki, amma shi wannan saɓani ya samu ne ta sanadiyar babban saɓani da suka samu kan mutuwar Buda, cikin addini Buda akwai mahanga guda biyu ta farko ita ce Hainayana ta biyu kuma ita ce Mahiyana, a mahangar farko tana bawa wannan mutuman muhimmanci (Mayitariya) amma a wannan mahanga akwai ruwayoyi da suka zo da suna wani mutum mai suna (Shakiya Muni) ko shi ne dai mai suna Gontama Buda kuma ya shahara da wannan sunan, kuma shi ne Buda, amma shi Miyatarya na huɗu shi ne, wanda daga bayanshi Buda na biyar zai zo kuma shi ne mai ceton mutane, anfi sanin shi da Buda na biyar. Amma a wasu riwayoyi a gunsu shi Gontama shi ne Buda na bakwai ba na huɗu ba, shi Budisatafa zai bayyana a gaba a matsayin Buda na ƙarshe domin `yantar da mutane. Akwai saɓani kan tarihin rayuwar Miyatariya wanda shi ne Buda na ƙarshe a doran ƙasa, a (littafin Shari'atul Bali) wanda shi ne littafin da muke samu bayanai kan addinn Buda, za muga shi wannan littafi baya bawa rayuwar Miyatariya muhimmanci sai kaɗan a wasu gurare, kamar inda suka ambaci sunanshi, amma a wasu litattafai da basu da muhimmanci da yawa, a gun `yan Buda akwai abin da ya keɓanta da magana kan imani da Miyatarya mai ceto. A cikin Mahafanasa, shi wannan littafi ne na tarihin ƙasar Sirilanka ta da, a cikin wannan littafi ne aka yi bayani dalla-dalla kan gwagwarmayar Miyatariya, ga abin da ya zo a cikinshi: Koma baya da rashin ci gaba ga ɗan Adam abu ne da yake ci gaba tare da rayuwarshi a cikin addinin Buda kamar yadda Diganikaya ya faɗa, a lokacin Buda Fiyabasi wanda ya bayyana kan shi kafin Kaba na 91 ɗan adam ya kasance yana rayuwa zuwa shekara 80000, amma a lokacin Buda Siki na biyu (kafin Kaba 231) ɗan adam ya kasance yana shekara 70000, amma Buda na bakwai mai suna Gotama ya bayyana kanshi a lokacin da mutum baya rayuwa fiye da shekara 100, wannan yana nuna cewa shekarun ɗan Adam sun kai ƙarshan miƙidarinsu, amma duk da haka su shekaru ba a ƙayyade su ba a addinin Buda, kuma wannan ya dace da abin da yake cikin ra'ayin Hindu wanda yake ganin cewa Buda Satuwa zai narke cikin jikin ɗan Adam domin shelanta zaman lafiya a rayuwar na dindin ɗan Adam na har abada.[10]

  • Mahangar Konafishiyosaya: An sanya wani take na komawa zamanin farkon lokacin `ya`yan sarakunan farko, wannan shi ne tinaninsu na farko domin kawo gyara, kuma ana alaƙanta ɗaukaka da hikimar sarakuna da tinanin mabiya Konafishiyosa.[11]
  • Mahangar Tawiyya: a al'adu da addini a ƙasar Sin akwai abin da ya yi kama da tinani da ra'ayi na Konafishiyosaya da wasu mazahabobi na tinani, amma banbanci da yake a tsakaninsu shi ne cewa imani da mai ceto a tawiyya ya fi fitowa fili kan sauran mazahabobi, misali idan ka duba cikin littafin (Shang-Ch'ing Too. Chon Lieh-Chi) zaka sami cewa Li Hung a mastayin mai ceto wanda zai bayyana a shekara ta (392 Miladiyya).[12]
  • Mahangar Shantuwiyya: ƙasar tana kamanceceniya da Jafan cikin abin ya yi kama da addinai da al'adu na ƙasar Sin, a nan ya kamata mu lura da wani abu cewa ra'ayin Shabtuwiyya da na Buda ya haɗu anan, kuma wannan shi ne ya zama wani fata ga al'ummar ƙasar Jafan, kuma wannan shi ne ya zama mahaɗa da matattara ta ƙarshe ga dukan mazahabobi waɗanda sukayi imani da mai ceto, daga cikin mazahabobin akwai mazahabin Kurizu Miku wanda wani mutum mai suna Kafata Bunjiru ya kafa a shekara ta (1814-1883) da mazahabin Tanrikuyo wanda shugabanshi shi ne Nakayama a shekara ta (1798-1878).[13]

Imani Da Mai Ceton Da Aka Yi Alƙawarin Zuwanshi A Addinan Ibrahimiyya

Addinin Zartashtiyya

Saɓanin sauran addinai shi addinin Zartashtiyya suna jiran masu ceto mutum uku ne, ba guda ɗaya ba, kuma ɗaya daga cikinsu shi ne mai ceto, kuma tsakanin bayyanar kowane ɗaya daga cikinsu akwai shekara dubu,[14] A Karshen duniya bisa ruwayoyin Zartashtiyya da Yushit na goma shatara daga cikin Yushit da suke da su, a cikin Zardashit za a haifi yara guda uku sunansu na gamagari shi ne Sushiyasa, amma shi wannan sunan ana kiran mutum na ƙarshansu ne kuma shi ne wanda ake jira kuma shi ne wanda Allah zai naɗa a matsayin Khalifa. Sushiyanit kalma ce wadda asalinta shi ne Sabsu, tana nufin shugaba da mai amfani, amma idan aka duba Kalmar a cikin littafin sa sun ana Usta, za a sami kalmarakamar haka; (Saoshyant) ana rubutata ta hanya daban-daban, kamar Sushiyansa da Sushans da Susiyush da Siyusush.[15]

Waɗannan `ya`yan guda uku su ne masu ceto a addinin Zartashit kuma su ne za su ceci duniya daga zalinci da lalacewa, za su bayyana ne a ƙarshan duniya kuma akwai shekara dubu a tsakanin kowane ɗaya daga cikinsu, ga su kamar haka:

  1. . Ukshit Irita (Ukhsyat ereta) shi wannan suna yana nufin mai kare dokoki masu tsarki (Hakan yana nufin ba shi ƙarfi da tabbatar da addini da adalci),[16] A wannan zamani ana kiran ɗa na farko da Hushidar ko Ushidar a wasu litattafan kamar Bahlawi ana kiran shi da Kurshitadar ko Ushitir, a wasu lokuta kuma ana ƙarawa sunan wannan Kalmar Bami sai ta zama Hushidar Bami shi wannan ƙari yana nufin Hushidar mai haske.
  2. . Sunan mutum na uku shi ne Ukshit Nima ko Ukshit Nimanƙa, ma'anar suna shi ne wanda yake raya ibada da yin addu'a, amma a yanzu ana kiranshi da (Hushidar Mah) amma a littafin Bahlawi ana kiranshi da Kurshit-Mah ko Ushitir Mah.
  3. . Ɗa na uku sunanshi (Astafat Irta) shi wanda zai bayyana dokoki masu tsarki, kuma shi ne dai mai suna Soshiyanit wanda aka yi alƙawarin zuwanshi domin ceton mutane a ƙarshan zamani, kuma shi ne ɗa na ƙarshe mai ceto da aka yi alƙawarin zuwanshi a mahanga irin ta Mazdisina ko Zadashtiyya.

Kuma su waɗannan `ya`ya guda uku an halicce su ne daga maniyin Zartashit, bisa abin da ya zo a al'adar Zartashtiyya cewa ubangiji Izid Nairusanƙ ya karɓi ruwan maniyi daga Zartashit sai ya aje shi a gurin sarkin ruwa, sai shi sarkin ruwa ya ci gaba da ajiyar wannan ruwa maniyi a ƙaramin Tabki na Hamun.

A ƙarshan Alfiya ta sha biyu ya zo cewa wata budurwa daga iyalin Bahruz ta je wannan ƙaramin tafki na Hamun ta yi wanka, bayan haka sai ta ɗauki ciki ta haifi Soshiyanit, kuma shi ne ƙarshan abin da ubangijin Ahura-Mazad ya halitta, kuma shi wannan ubangiji zai wakilta Soshiyanit ɗaukan nauyin saƙo na tsawan shekara 30 a wannan lokacin ne rana zat a tsaya sama, kuma wannan wata alama ce da mutane zasu san wannan lokaaci ne na bayyanar Soshiyanet wanda aka yi alƙawarin cetonshi, zai wa mutane albishirin sabuwar duniya, bayan bayyanar Soshiyanet ba za a sami Ahraman Wiladiyu na ƙarya ba, saboda dukkansu za su yi rashin nasara a hannun Soshiyanet, a lokacin Soshiyanet mabiyanshi za su kasance tare da shi kuma za su yi juyin-juya-hali tare da shi kuma za su zama sojojinshi, to a lokacin ne mamata za su dawo, kuma duniya za ta rayu cikin addini da lafiya.[17]

A Addini Yahudawa

A wurare da daman gaske akwai nuni da ishara a littafi mai tsarki (tsohon alƙawari) na Yahudawa kan mai ceto wanda zai zo a ƙarshan zamani,[18] Shi wannan mutumin da zai zo a ƙarshan zamani zai zo ne domin gina sabuwar rayuwa wadda mutane suke fatanta gaba ɗaya, duniya za ta zama mai tsafta daga zalinci kuma mutum zai zama yana iya isa ga hadafinshi da kuma ci gaba.

Wurare masu yawa a cikin littafin Mazamir akwai nuni da ishara kan bayyanar mai ceto a ƙarshan zamani, kuma daga cikin nassosin akwai nassi da yake nuna cewa akwai alƙawarin Allah na yin nasarar mutanan kirki kan mutanan banza, bayan haka ne sai a kafa gwamnati guda ɗaya a duniya gaba ɗaya, mutane za su zama Mabiyan addini guda ɗaya.

A lokacin wannan gwamnati ne mutane za su ɗabbaƙa adalci da gaskiya kuma mutane za su kasance cikin aminci, mutane za su bi malamai kuma zai yi wa talakawa adalci da ceton masu Rauni kuma zai gama da azzalumai, azzalumai za su ji tsoranshi, zai yayyanka azzalimai, ya yi kama da mamakon ruwan sama, a lokacin ne aboki na gaskiya zai bayyana, kuma a lokacinshi ne addini zai yaɗu har ƙarshan gwamnatinshi, duk duniya za ta zama a ƙarƙashin mulkinshi, duk mutane za su yi biyayya ga gwamnatinshi, su kuma makiyanshi za su yi da nasani da nadama, sarakuna za su yi rige-rige wajan yin bai'a, ƙasashe za su yi shelar mubaya'a kafin ya kai gare su, masu Mulki za su yi ta bada kyauta, kuma duk za su yi biyayya, duk mutane za su bishi, saboda zai ceci talakan da ya nemi taimakwanshi yayin da babu mai taimako sai shi, zai zama rahama ga talakawa da masu rauni kuma zai cece su daga zalinci da yin garkuwa da su da girmama su kuma zai ba da kyautar zinare, za a tsaida ibada saboda shi, albarka zata yawaita a doran ƙasa, ambatonshi zai dauwama a faɗin duniya za ayi ta neman albarkarshi, duk mutane za su ji daɗin gwamnatinshi, Allah ya yi mishi albarka kuma mutum ne mai ban mamaki.[19]

Yahudawa sun yi imani cewa mai ceto a ƙarshan zamani shi ne Masihu, kuma ana kiranshi da Almashihu, ana nufin wanda aka shafa daga Allah kuma shi ne zai mayar da duniya kamar yadda mutane suke so, kuma akwai rayuwa mai kyau a gaba.

Mafi yawancin malaman Yahudawa suna riƙo da wannan aƙida da take cewa mai ceton da aka yi alƙawarin zuwanshi shi ne Masihu wanda zai kyautata rayuwar al'umma kuma zai kyawunta yanayi a tsakanin dukkan mutane da biya musu buƙatunsu, duk wannan zai faru ne sakamakon tsari na Allah tin farkon abin da Allah ya fara halitta, bisa wannan zai zamo tilascin samuwar aƙidar mai ceto a gurin Allah tin kafin ya ƙirƙiri halitta.[20]

Mai ceto (Masihu) bisa aƙidar dukkan Yahudawa, wani mutum ne da ya yi kama da sauran mutane, amma ya bambanta da su ta hanyar bayyanar ƙudurar Allah a tare da shi, kuma zai haskaka duniya da haskenshi wanda ya samo daga Allah.

Amma akwai waɗanda suka yi imani cewa shi Masihu shi ne Annabi Dauda ba Yesu ba (Annabi Isah)[21] Wasu Yahudawa suna ganin cewa ba dole bane shi Mashihu ya kasance Annabi Dauda, bari dai shi wani mutum ne a daga gidan Annabi Dauda,[22] Wasu kuma a cikinsu sun yi imani cewa Allah a ƙarshan zamani zai turo da Annabi Dauda domin ya ceci mutane.[23]

Aƙidar Mai ceto A Addinin Kiristanci

Mai ceto bisa aƙidar Kiristanci sunanshi Farƙaliɗ, wannan suna yana nufin mai ɗaukaka da mai ceto da mai taimako, amma bisa abin da ya zo a sabon alƙawari mai ceto shi ne Annabi Isa (A.S) a gurinsu annabi Isa zai dawo kuma idan ya dawo zai ceci mutane daga dukkan fasadi da fitina.

Magana kan dawowar Annabi Isa ta gabata, cewa shi Annabi Isa ba zai barkanshi cikin azaba ba kuma baya ganin kanshi cikin masu ɓarna, kuma mu shedun ne kan haka.[24]

Bayan Annabi Isa ya sadaukar da kanshi fansa ga zunuban mutane kuma zai bayyana karo na biyu domin ceton mutanen da suke jiranshi.[25]

Akwai wani abu da yake da muhimmanci shi ne cewa a sabo alƙawari an yi nuni cewa mai ceto a ƙarshan zamani zai zo bayan Annabi Isa, kuma shi Annabi Isa da kanshi shi ne ya yi alƙawarin zuwanshi, shi wannan mai ceto mai girma annabi Isa (A.S) zai buƙata daga Allah mahaifi bisa aƙidar kiristanci domin ceton al'umma, kuma Allah zai ba da shi ga annabi Isa da duniya gaba ɗaya kuma koda yaushe Annabi Isa zai kasance tare da shi, shi wannan mai ceto babu wanda zai ganshi ko ya san shi sai wanda ya yi imani da shi.

Shi wannan mai ceto shi wannan Ruhi ne wanda duniya ba za ta iya karbarshi ba, saboda ba sa ganinshi kuma basu san shi ba, amma ku kuna ganinshi domin yana ruyuwa a cikin ku yana tare da ku.[26] amma shi wannan annabi Isah da ake Magana kanshi bashi bane wanda alumar annabi Musa da Yahudawa suke jira, shi wanda ake jira zai bayyana ne bayan tafiyar annabi Isa (A.S) bayan haka zai shiriyar da mutanan duniya zuwa gaskiya kuma zai taimaka wajan tabbatar da adalci da gwamnatin adalci a duniya, saboda idan ya yi Magana baza kaga yana Magana kanshi ba, koda yaushe yana Magana ne kan annabi Isah da Allah mahaifi.

Sai dai na faɗa muku gaskiya cewa alherin ne na tafi, saboda idan ban tafi ba, to fa mai ceto ba zai zo muku ba, amma idan na tafi za a turo muku mai ceto, duk lokacin da mai ceto ya zo, zai saita duniya kan tsari da abu mai kyau, zai ɗora ta kan tsari saboda ba su yi imani da shi ba, amma zai ɗora duniya kan abu mai kyau da biyayya saboda shi zai koma zuwa ga mahaifinshi bazaku ƙara ganina ba, amma kan bashi, saboda shugaban wannan duniya ya ɗorata kan bashi, cewa ni ina da abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ku bazaku fahimci abin da zan faɗa ba yanzu, amma duk lokacin da mai ceto ya zo wanda shi ne rai na gaskiya, to shi ne wanda zai shiryar da ku zuwa gaskiya, saboda shi yana Magana ne da yawun Allah, duk abin da zai ji da maganarshi da labarin da zai baku na abubuwan da za su zo, wannan kuma yana burgeni kuma yana farantamin rai, saboda yana samuwa ne daga inda nake samuwa kuma ya baku labari…..[27]

Aƙidar Mai ceto A Musulinci

Dukkan mazahabobi na muslunci sun yi imani da zuwan mai ceto a ƙarshan zamani, duk da suna da saɓani kan abubuwan da suka keɓanta da shi, da yadda zai bayyana. Ahlus-Sunna sun yi imani da cewa mai ceto za a haife shi a nan gaba, kuma zai fito ne daga cikin zuriyar Annabi (S.A.W). Amma shi'a daga cikin aƙidarsu shi ne cewa mai ceto wanda ake jira yana nan a raye kuma yana cikin mu, kuma wasu daga cikin malaman Ahlus-sunna sun yi imani da haka, maganar gaskiya ita ce `yan shia da Ahhlus-sunna sun yi ittifaƙi kan aƙidar mai ceton da aka yi alƙawarin zuwanshi, sakamakon wasu ingantatun hadisai da aka rawaito daga Annabi (S.AW) kuma sun yi imani da haka imani mai ƙarfi, idan ya zo zai cikin duniya da adalci kamr yadda ta ciki da zalinci.

Zai yiwu a tattauna wannan imani na mai ceto a muslunci a wasu ayoyi na Kur'ani mai girma, ayoyin sun kasu gida biyu:

  1. . Kashi na farko; ayoyin da suka nuna cewa akwai ceto na musamman a ƙarshan duniya, to anan zai yiwu Maudu'i Imam Mahadi ya zama ɗaya daga cikin abin da waɗannan ayoyi suke nufii, ko kuma ya zama wannan maudu'i na Imam Mahadi (A.S) shi ne mafi dacewa daga cikin ma'anonin wannan ayoyi, ayoyin sune kamar haka; aya ta 33 a suratul Tauba, aya ta 28 a suratul Fatah, aya ta 9 a saratul Saf, aya ta 105 a sauratul Anbiya, aya ta 55 a suratul Nur, ayoyi guda biyu a suratul ƙasas, kamar yadda ayoyin wannan kasan basu da yawa.
  2. . Kashi na biyu; ayoyin da suke nuni kan mai ceto da aka yi alƙawarin zuwanshi, waɗanda aka fassara su da bayyanar mai ceton da aka yi alƙawarin zuwanshi ko aka fassara su da bayyanar Imam Mahadi (A.S) da hanyar amfani da ruwayoyi, kuma waɗannan ayoyin sun fi kashi na farko yawa, kuma ruwayoyin da suka fassara wannan ayoyin sun zo a cikin litattafan tafsiri daban-daban.

Bayan ayoyin kur'ani akwai wani dalilin da ya yi Magana kan bayyanar mai ceto, wannan dalili shi ne hadisan Annabi, wannan hadisai suna ɗauke da duk abin da ake buƙata domin yin imani da zuwan mai ceto koda a kowane addini ne, kuma wannan hadisai suna da yawa, sun faɗa mana sunan mai ceto da laƙabinshi da ƙarin bayanai kanshi a ƙarshan zamani, da abubuwan da za su faro kan zuwanshi da lokacin zuwanshi, da sakamakon da zai biyu bayan kafa gwamnatinshi, kuma musulmi sun rawaito wannan ruwayoyi gungu-gungu har aka kiyaye su cikin litattafai kuma aka rawaito su cikin litattafai na hadisi.[28]

A ruwayoyin Shi'a za mu ga yadda suka rawaito siffofin wannan mai ceto na Zahiri da baɗini a ƙarshan zamani, ba tare da wata wahalar fahimta ba, daga ciki akwai wannan ruwayar da aka rawaito daga Imam Muhammad Baƙir (A.S)

فأنا بقية من آدم وذخيرة من نوح، ومصطفى من إبراهيم، وصفوة من محمد صلى الله عليهم أجمعين. ألا فمن حاجني في كتاب الله فأنا أولى الناس بكتاب الله، ألا ومن حاجني في سنة رسول الله فأنا أولى الناس بسنة رسول الله صلى الله عليه وآله

"Ni ne ragowar Adamu, ajiyar Nuhu, zababbe daga Ibrahim, kuma zababben Muhammad, amincin Allah ya tabbata a gares su baki daya. Duk wanda ya yi min gardama a kan littafin Allah, ni ne mafi cancantar littafin Allah. Duk wanda ya yi min gardama akan sunnar Manzon Allah, ni ne mafi cancantar Sunnar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa..[29]

Bayanin kula

  1. Duba: Tuni'ei, Maudu'uNameh, shafi na 706
  2. Duba: Tuni'ei, Maudu'uNameh, shafuka na 707 da 708; wasu marubuta, Guneh shinasi andusge Munji Mau'ud Dar Adyan, shafi na 19
  3. wasu marubuta, Guneh shinasi andusge Munji Mau'ud Dar Adyan, shafi na 19
  4. Shaygan, Dariush, Adyan wa Maktabehaye Falsafi Hindu, 1: 281-284; Jalali Naeini, Mahabharat, vol. 1, shafi na 20-22, 139, 353 da sauran su.; Juzu'i na 3, shafi na 55, 126-127, 257, 305; Evans, Vernica, Asatir Hindu, Bajlan Farrokhi ya fassara, shafi na 39-43.
  5. Shaygan, Dariush, Adyan wa Maktabehaye Falsafi Hindu, 1: 282
  6. Evans, Veronica, Asatir Hindu, shafi na 41
  7. Evans, Veronica, Asatir Hindu, shafi na 274
  8. Littafin Hindu Mai Tsarki, Alhindusi Al-ubanishad, Vol. 2, ku. 637
  9. Wolfgang Schumann, Hans, Ayineh Buddah, wanda A. Pashaei ya fassara, shafi na. 121.
  10. Eliade, Mercia, Ak-audil abadi, shafi na 204-205; Kuma lura: Movahdian Attar, "Goneshnasi Andisheh Ma'oud dar-i-Dyan-i-Akhtar," shafi. 118.
  11. Al-Mawahid Attar,Guneshinasi Andishe Mau'ud dar Adyan Mukhtalif, shafi na. 132.
  12. Al-Mawahid Attar,Guneshinasi Andishe Mau'ud dar Adyan Mukhtalif, shafi na. 154.
  13. Al-Mawahid Attar,Guneshinasi Andishe Mau'ud dar Adyan Mukhtalif, shafi na. 126.
  14. Mary Boyce, Tarikhu Zoroashtush, Sanati Zadeh ya fassara, p. 391.
  15. Pourdaoud, Risalaeh Sochians, p. 8; Farhange Namhaye Avesta, Vol. 2, ku. 769; A cikin Farvardin Yasht, abu na 129.
  16. Vendidad, vol. 4, ku. 1757.
  17. Yashta, 101:2; Vendidad, vol. 4, 1757-1758.
  18. Game da: Ishaya, 1:11-10 da 65:9-13 da 18-20; Daniyel, 12:1-5 da 10-13; Habakkuk, 2:3-5.
  19. Zabura 72:2-18; duba Safrur Mazamir 37:9-12, 17-18 da 96:10-13.
  20. Kohn, Ibrahim, Gunjineh Talmud, p. 352.
  21. Yusha'u 3:5
  22. Zabura 18:49-50; Greenstone, Julius, Intizar masiha dar Ayineh Yahud, shafi na 65-66; Don ƙarin bayani, duba: Kohn, Ibrahim, Gunjinehh Az Talmud, shafi na 352-3.
  23. Urmiya, 9:30
  24. Aamalul Rusuli 2:31-32.
  25. Risala Bolis Rasul Ilal Abraniyin 9:28.
  26. Linjil Yohanna, 17:14.
  27. Linjil Yohanna, 16:7-14.
  28. Ƙungiyar mawallafa, Guneshiansi Andishe Munji Mau'ud dar Adyan, shafi na. 227.
  29. Boruni, Ali, Mashihu, Masihu, Mahdi Dar Adyan Ibrahim, Morgh Suleiman Publications, shafi. 72

Nassoshi

  • Al-kutubul mukaddasatul Hindusiyya: A;-Ubanishad.
  • Iliad, Mercia, Astura Al-Awd al-Abdi, fassara daga Faransanci: Nihad Shitah, Damascus - Al-Mazzah Highway, Talasdar, bugun farko, 1987.
  • Oshidari, Jahangir, Daneshnameh Mazdasina, Markaz Publishing House, 1992.
  • Evans, Veronica, Asatirf Hindu, Bajlan Farrokhi ya fassara, Ɗabi'un Tatsuniyoyi, 1994.
  • Boruni, Ali, Masihu, Mahdi dar adyane Ibrahim, Morgh Sulayman Publications, bugun farko, 2010.
  • Tunei, Mojtaba, Sunan Alkawari: Kamus na Harafi na Mahdism, Qum, Jigon Gado, Bugu na 10, 2009.
  • Jalali Naeini, Mahabharat, Mawallafin Laburare na Tahouri, 1970.
  • Ƙungiyar masu bincike, Guneshiansi Andishe Munji Mau'ud dar Adyan, Qum, Jami'ar Addinai da Ƙungiyoyin Jama'a, Buga na Farko, 2010.
  • Shaygan, Dariush, Adyane wa Maktabhaye Falsafai Hindu, Amir Kabir Publications, 1977.
  • Littafi Mai Tsarki.
  • Kohn, Abraham, Gujineh Az Talmud, wanda Amir Fereydoun Gorgani ya fassara, bugun Ziba, 1350.
  • Greenstone, Julius, Intizar Almasihu dar Ayine Yahud, wanda Hossein Towighi ya fassara, Jami'ar Addinai da Ɗabi'un Darika, Bugu na Biyu, 2008.
  • Labulen Taghizadeh, karkashin kulawar Iraj Afshar, Vol. 9 (Mani da Addininsa), Shokofan Publications, 1977.
  • موحدیان عطار، علی، «گونه‌شناسی اندیشه موعود در ادیان مختلف»، فصلنامه هفت آسمان، ش 12، شتاء 1380ش.
  • Wolfgang Schumann, Hans, Ayineh Buddah, wanda A. Pasha ya fassara.