Jump to content

Husainiyyar Imam Khomaini (Tehran)

Daga wikishia
Husainiyyar Imam Khomaini
Wanda ya kafaMuhsin Rafiƙ Dusti
Kafawa1989 miladiyya
Mai amfaniAyyukan da'awa da koyarwa
WuriTehran. Iran
Sauran sunayeHusainiyyar gidan jagora
HaliTana kan aiki
FaɗiMurabba'in mita 2000


Husainiyyar Imam Khomaini, (Larabci: حسينية الإمام الخميني تهران) ɗaya ce daga cikin Husainiyyoyin babban birnin Tehran, wace ake yin tarurrukan addini da hukuma da jalsosin darasussukan Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran. An kafa wannan Husainiyya a shekarar 1989m, wace shekara ta farko da fara jagorancin Sayyid Ali Khamna'i.

Amfani

Darasin kharij na Ayatullah Khamna'i a Husainiyyyar Imam Khomaini 23 Oktoba 2019m.

Husainiyyar Imam Khomaini, wani gini a babban birnin Tehran wace galibi a wannan wuri ne ake yin tarurrukan hukuma da Sayyid Ali Khamna'I yake halarta, daga jumlar tarurrukan akwai ganawa da gayyar mutane,[1] da tarurrukan addini[2] da ajujuwan darasin kharijul fiƙhi na Sayyid Khamna'i.[3] Mafi shaharar taron addini da ake yi a wannan Husainiya shi ne makokin Muharram da kwanakin tunawa da shahada Fatima. Tun daga farkon watan Ramadan zuwa ƙarshe, a ko wace rana a na yin sallar jam'i na azuhur da la'asar. A wasu ranaku na musamman, Sayyid Ali Khamna'i yana yin limancin sallah a wannan Husainiyya.[4]

Ginin Husainiyya

Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci aikin ginin Husainiyar Imam Khomaini

A shekarar 1989m, bayan zaɓar Ayatullahi Khamna'i matsayin jagoran juyin juya halin Muslunci Na Iran, bisa shawarar Muhisin Rafiƙ Dusti, an sayi wani gida da ya kasance mallakar iyalan tsohuwar gwamnati, aka gina Husainiyyar Imam Khomaini a wannan wuri.[5]

An yi gina wannann Husainiyya a fili mai girman mita dubu biyu. A cewar Muhsin Rafiƙ, an kammala gina wannan Husainiyya cikin kwanaki 62 da kuɗaɗen da mutane suka bayar da taimako domin gina ta, bayan kammala gini, bisa shawarar Ayatullahi Khamna'i, an shimfiɗe wannan Husainiya da tabarma saƙar hannu.[6]Kafet-Kafet na wannan Husainiyya ya kasance daga ƙasar hannu na garin Yazdi[7] Ginin Husainiyya, an ƙawata Husainiyyar da bulo mai girman senti mita uku.[8]

Bayanin kula

  1. "Masallacin Imam Khumaini Husainiyyah ya dauki nauyin ajujuwa," in ji kamfanin dillancin labarai na IMNA.
  2. "Daren karshe na zaman makokin Sayyida Fatima Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) a Husainiyyar Imam Khumaini (R)" a shafin yanar gizon ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei.
  3. "Kafa Husainiyya na Imam Khumaini", gidan yanar gizon Parsa.
  4. "Husaini's Imam Khomeini", Iran Fanzi website.
  5. "Yaya aka yi shugabancin?/Me ya sa "Agha" bai je Jamaran ba?!", Jahannews.
  6. "Rafiq Doost:Man Misle Camaq mi monam," Kamfanin Dillancin Labarai na Tabnak.
  7. "Zayulhaye Husainiyye Imam Khumaini?", Cibiyar Watsa Labarai ta Hawza.
  8. "Rafiq Doost:Man Misle Camaq mi monam," Kamfanin Dillancin Labarai na Tabnak.

Nassoshi

«بیت رهبری چگونه ساخته شد؟/ چرا "آقا" به جماران نرفت؟!»،Jahan News, an wallafa labarin a ranar 20 ga watan Khordad shekara ta 1395 ta Hijira Shamsiyya (daidai da kimanin 9 ga Yuni 2016), kuma an ziyarta a ranar 18 ga Khordad 1403 SH (kimanin 7 ga Yuni 2024).