Maganganun Imam Ali (A.S) Lokacin Binne Fatima (A.S)

Daga wikishia

Maganganun Imam Ali (A.S) lokacin Binne Fatima (S) (Larabci: خطبة الإمام علي(ع) عند دفن السيدة فاطمة(ع)) bayani ne da yake tattare da radadin da Imam Ali (A.S) tare da Manzon Allah (S.A.W) lokacin Makokin Fatima, wannan Bayanai sun zo cikin Nahjul Al-Balaga, wannan bayanai nasa sun kunshi raradi mai nauyi da dawwamuwar bakin cikinsa kan shahadar Hazrat Fatima (S) ya yi magana, sannan kuma yana son Annabi (S.A.W) a kan abubuwan da suka faru bayan wafatinsa ya tambayi Fatima (S). hakika Masu Sharhin littafin Nahjul Al-Balaga sun tafi kan cewa Imam Ali (A.S) ya yi amfani da jumla gamammiya kan Tambayar Fatima (S) kan abubuwan da suka afku bayan wafatin Annabi (S.A.W) kamar misalin Kwace Fadak, kai hari kan gidan Fatima, barin cikin Muhsin, duk ya yi ishara zuwa gare su cikin maganar da ya yi lokacin binneta, haka kuma cikin maganganun da ya yi cikin wannan Huduba an fahimci wasu abubuwan daban cikin harda misalin binneta kusa da Kabarin Annabi (S.A.W).

Wadannan Maganganu nasa an nakalto su cikin litattafan Shi’a misalin littafin Alkafi da Amali Shaik Tusi da kuma litattafan Ahlus-sunna misalin Tazkiratu Khawas.

Fagen Da Suka Fito Da Kuma Muhimmancinsu

lambobin Huɗubobi cikin mabambantan kwafin Nahjul Balaga
Kwafi Lambar Huɗuba
Al-Mujam Almufahris Li Al-Faz Nahjul Balaga 202
tashihu Nahju Balaga na Subhi Saleh 202
tarjameh wa Sharhu Nahjul Balaga Faizul Kashani 193
Misbahul As-Salikin na Ibn Maisam 193
Minhajul Al-Bara'a na Habibullahi Kuyi 201
Sharhu Nahjul Balaga na Mulla Salihu Ƙazwini 201
Sharhu Nahjul Balaga na Ibn ABil Al-Hadid 195
Sharhu Nahul Balaga na Muhammad Abduhu 195
Tanbihul Al-Gafilin na Mulla Fatahullahi Kashani 230
Fi Zilali Nahjul Balaga na Muhammad Jawad Mugniyya 200[1]

Maganganun da Imam Ali (A.S) ya yi zuwa ga Annabi (S.A.W) lokacin binne Fatima (S) suna nuni kan damuwar da ya yi dangane da rabuwa da Matarsa da sharhin irin girman da Hazrat Fatima (S) take da shi. [2] a cewar Ayatullahi Makarim Shirazi cikin Sharh Nahjul Al-Balaga, wadannan Maganganu wani sashe ne na tabbatatun abubuwa masu muhimmanci a tarihin farkon Muslunci ta sura wacce ba kai tsaye ba, sai dai cewa kuma tana bayyana a fili. [3] Masu Sharhin littafin Nahjul Al-Balaga a karshen wannan Huduba sun tsunduma cikin Bahasin mas’aloli misalin, waki’ar kwace Fadak, kwace Halifanci, dalilin boye Kabarin Fatima (A.S), lokacin shahadarta, [4] muddar rayuwarta, [5] Lakubban Fatima [6]

Abin da Hudubar Ta Tattaro

Maganganun Imam Ali (A.S) da suka kunshi radadin da ya yi tare da Annabi (S.A.W) da kuma musibar da ta same shi kan rabuwa da matarsa Fatima (A.S) [7] cikin wannan maganganu, ya bayyana irin nauyi da dawwamuwar bakin cikin shahadar Hazrat Fatima (S) ya yi Magana yana kuma rokon hakuri daga Allah, Imam Ali (A.S) ya nemi Annabi (S.A.W) ya tambayi Fatima (S) kan abubuwan da suka faru bayan wafatinsa, cikin wadannan maganganu nasa ya bayyana cewa hakika Fatima Amana ce a da aka bashi yanzu kuma ta koma wurin Mahaifinta. [8]

Abubuwan Da Aka Fito Dasu Daga Hudubar

Masu Sharhin Nahjul Albalaga a karshen wannan Huduba sun fito da wasu abubuwa wadanda ba’arin wasunsu sun kasance cikin sharhin da zai zo a kasa: Damfaruwa ta soyayya tsakanin Ali da Fatima: wasu ba’arin masu sharhi sun bayyana cewa jumlar

«أَمَّا حُزْنِی فَسَرْمَدٌ وَ أَمَّا لَیلِی فَمُسَهَّدٌ؛

Lallai bakin cikina kan rabuwa da ke Madawwami ne, amma Darena ido bude zai kasance. Ta kasance alama tsananin Bakin cikin da Imam Ali (A.S) ya yi kan rabuwa da Fatima kuma tana bayyana irin tsananin soyayya da damfaruwa ta ruhi da take a tsakaninsu, Ayatullahi Makarim Shirazi ya tafi kan cewa baitukan wakokin da za su zo a kasa wadanda aka danganta su zuwa ga Imam Ali (A.S) suna nuna da ishara kan wannan al’amarin ne. [9]

  • kasancewar Kabarin Fatima kusa da kabarin Mahaifinta: ba’arin masu Sharhi suna ganin cewa jamlar:
النَّازِلَةِ فِي جِوَارِكَ

Tana Sauka Kusa da kai. Hakika tana nunin kusancin Kabarinta dana Mahaifinta. [10] A cewar Ayatullahi Makarim Shirazi ya ce: wannan jumla tana karfafa ra’ayin wanda suke ganin an binne Fatima a gidanta. [11]

  • kasancewar Fatima wacce aka zalunta: a cewar Ibn Maisam Bahrani wanda ya mutu a shekara 679 ko 699 h kamari, jumlar
«فَأَحْفِهَا السُّؤَالَ؛

Ka Tambayeta a bude babu rufe-rufe. Tana ishara kan zaluncin da aka yi mata, kuma Ali (A.S) yana kai kara kan wannan zalunci. [12] Ayatullahi Makarim Shirazi shima ya ce wannan jumla tana ishara ne kan abubuwan da suka faru bayan Annabi (S.A.W) daga kai hari gidanta, barin cikin Muhsin, kai Imam Ali (A.S) Masallaci da karfin tuwo domin yi wa Abubakar Mubaya’a. [13] cikin Tarjamar Faizul Islam cikin sharhin wannan Jumla anyi ishara kan kwace Fadak, nuna rashin sanin matsayinta da karya Kashin Awazarta. [14]

  • Hannun dukkanin Mutane cikin zaluntarta: dangane da jumlar
«بِتَضَافُرِ أُمَّتِکَ عَلَی هَضْمِهَا؛

Tare da haduwar Al’ummarka kan zaluntarta. Malamai sun ce Kalmar (Tadhafur) tana bada ma’ana hade kai, sakamakon Aksarin al’umma a wancan lokaci sun yi shiru kan zaluntarta kuma shirinsu ya karfafi zaluncin, sai aka danganta aikata shi ga baki dayansu. [15]

  • Kusancin shahadarta da Wafatin Annabi (S.A.W): wasu ba’arin Masu sharhin Nahjul Al-Balaga sun bayyana cewa jumlar
«السَّرِيعَةِ اللَّحَاقِ بِكَ؛ به‌سرعت به تو ملحق شد»

Tana Gaggawar haduwa da kai. Tana ishara kan Kusancin shahadarta da wafatin Annabi (S.A.W). [16] na’am a ra’ayin wasu Malaman wannan jumla ishara ce zuwa ga Musibun Fatima wanda kan Kufansu ne ta yi shahada tana Matashiya. [17]

Isnadin Huduba

Hoton littafin Huznu Sarmad a bayanin hudubar Nahj al-Balagha ta 202.

Kan asasin binciken littafin Masadir Nahjul Al-Balaga wa Asanidihu, maganganun Imam Ali (A.S) cikin sakonsa zuwa ga Annabi (S.A.W) lokacin binne Fatima (S) akwai dan banbanci kadan da abin da litattafai suka kawo kamar misalin Alkafi talifin Muhammad Bn Yakub Kulaini wanda ya mutu shekara 329 h kamari, cikin nakali daga Imam Husaini (A.S), [18] da kuma littafin Dala’ilul Al’imama talifin Muhammad Bn Jarir Tabari Sagir da nakalin daga Imam Jafar Sadik (A.S) [19] da kuma littafin Amali Shaik Tusi talifin shekara ta 458 h kamari, da nakali daga Imam Husaini (A.S) [20] da littafin Tazkiratu Al-khawas talifin Sibt Ibn Jauzi Hanafi wanda ya mutu shekara ta 654 h kamari. [21] - [22] Haka kuma wannan maganganu sun zo cikin Nahjul Al-Balaga, [23] sai dai cewa lambobin hudubobi suna banbanta a Nahjul Al-Balaga bisa Banbanci Mabuga da Kofi. [24]

Nazari

Huzunu Sarmadi, taken wani littafi da Kamalud Addini Saruri ya wallafa shi kan sharhin huduba ta 202 cikin Nahjul AL-Balaga, hakika wannan littafi tare da unwanin Far’i Saugenameh Amirul Mumnin (A.S) bar Mazare Hazrat Fatimeh Zahra (S) aka buga shi da yada ta hannun cibiyar Nashar a shekara ta 1383 h shamsi.

Matani da Tarjama

Kai kuka wurin Annabi (S.A.W) bayan Shahadar Fatima (S)
الإمامُ عليٌّ عليه السلام ـ عِندَ دَفنِ فاطِمَةَ عليها السلام ـ : السَّلامُ عَلَيكَ يا رسولَ اللّه ِ عَنّي وَ عَن اِبنَتِكَ النّازِلَةِ في جِوارِكَ وَ السَّريعَةِ اللَّحاقِ بِكَ. قَلَّ يا رسولُ اللّه ِ عَن صَفيَّتِكَ صَبري، وَ رَقَّ عَنها تَجَلُّدي؛ إلاّ أنَّ لي في التَّأسّي بِعَظيمِ فُرقَتِكَ وَ فادِحِ مُصيبَتِكَ مَوضِعَ تَعَزٍّ ؛ فَلَقَد وَسَّدتُكَ في مَلحودَةِ قَبرِكَ، وَ فاضَت بَينَ نَحري وَ صَدري نَفسُكَ. فَإنّا للّه ِ وَ إنّا إلَيهِ راجِعونَ. فَلَقَد استُرجِعَتِ الوَديعَةُ، وَ أُخِذَتِ الرَّهينَةُ. أمّا حُزني فَسَرمَدٌ، وَ أمّا لَيلي فَمُسَهَّدٌ إلى أن يَختارَ اللّه ُ لي دارَكَ الَّتي أنتَ بِها مُقيمٌ. وَ سَتُنَبِّئُكَ ابنَتُكَ بِتَضافُرِ أُمَّتِكَ عَلى هَضمِها فَأحفِها السؤالَ وَ استَخبِرها الحالَ. هذا وَ لَم يَطُلِ العَهدُ وَ لَم يَخلُ مِنكَ الذِّكرُ. وَ السَّلامُ عَلَيكُما سَلامَ مُوَدِّعٍ لا قالٍ وَ لا سَئِمٍ.فَإن أنصَرِف فَلا عَن مَلالَةٍ، وَ إن أُقِم فَلا عَن سوءِ ظَنٍّ بِما وَعَدَ اللّه ُ الصّابِرين

daga cikin maganarsa da aka rawaito daga gare shi yayin binne shugabar matan aljanna Fatima (S) kamar misalin wanda Manzon Allah (s.a.w) yake ganawa da shi a kabarinsa, yana mai cewa Amincin Allah ya tabata a gareka ya manzon Allah da `yarka da sauka kusa da kai, mai gaggauta riskarka, hakurina ya karanta daga nisanci daga zababbiyar `yarka, juriya da dauriyata sun kare, sai dai cewa tunawa da babban rashinka da na yi yana saukaka mini radadin bakin ciki, saboda ba zan taba mantawa da lokacin da kanka yake kwance a kirjina ba, kuma ka bar duniya ne kana rungume da ni, inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, hakika na maido da ajiya, kuma an karbi jingina daga hannuna, amma bakin cikina bakin cikin na dindin, idona ba zai iya barci ba har zuwa lokacin da Allah zai zaba mini gidanka wanda kake zauna ciki a yanzu, lallai `yarka za ta baka labarin yanda al'ummarka suka hade kai cikin danne hakkinta, ka tambayeta dukkanin abin da ya faru bayan tafiyarka, wannan kenan daidai lokacin da baka jima da komawa ga Allah ba, ba a manta da kai ba kana na a cikin kwakwale, aminci ya tabbata a gareku sallama ta mai bankwana ba mai nuna kiyayya da kosawa ba, saboda haka idan na juya na tafi ba zan tafi ba sakamakon gajiya da kosawa ba, idan kuma na zauna ba zai kasance sakamakon munana zato daga abin da Allah ya yiwa masu hakuri alkawari ba

Bayanin kula

  1. Dashti wa Mohammadi, Al-Mu'jajm Al-Mufahris li Al-Faz Nahj al-Balagha, 1357, shafi na 513.
  2. Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, shafi na 32.
  3. Makarem Shirazi, Payama Imam Amir al-Momenin, 2006, juzu'i na 8, shafi na 56-40.
  4. Makarem Shirazi, Payama Imam Amir al-Momenin, 2006, juzu'i na 8, shafi na 40-56
  5. Khoei, Minhaj al-Baraa', 1358, juzu'i na 13, shafi na 10-11.
  6. Khoei, Minhaj al-Baraa', 1358, juzu'i na 13, shafi na 8-4.
  7. Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, shafi na 30.
  8. Duba Sobhi Saleh, Nahj al-Balagha, 1414 AH, shafi na 319.
  9. Makarem Shirazi, Payam Imam Amir al-Momenin, 2006, juzu'i na 8, shafi na 37.
  10. Khoei, Minhaj al-Baraa', 1358, juzu'i na 13, shafi na 8-9.
  11. Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, shafi na 32.
  12. Ibn Maitham, Iktiyaru Misbah al-Salkin , 1366, shafi na 393.
  13. Makarem Shirazi, Sakon Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, 37-38.
  14. Faiz al-Islam, Tarjameh wa Sharh Nahj al-Balagha, 1371, shafi na 653.
  15. Makarem Shirazi, Payam Imam Amir al-Momenin, 2006, juzu'i na 8, shafi na 38.
  16. Khoei, Minhaj al-Baraa', 1358, juzu'i na 13, shafi na 9-10.
  17. Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, shafi na 33.
  18. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 458.
  19. Tabari, Dala'il Al-Imamah, 1413 AH, shafi na 137.
  20. Tusi, Al-Amali, 1414 AH, shafi na 109.
  21. Ibn Jozi, Tazkira Al-Khwas, 1426 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 361.
  22. Hosseini Khatib, Masadir Nahj al-Balagha wa Asanideh, 1985, juzu'i na 3, shafi na 85-87.
  23. Sobhi Saleh, Nahj al-Balagha, 1414 AH, shafi na 319; Faiz al-Islam, tarjameh wa Sharh Nahj al-Balagha, 1371
  24. Dashti da Mohammadi, Al-Mu'jajm Al-Mufars na Al-Faz Nahj al-Balagha, 1357, shafi na 513.

Nassoshi

  • Nahj al-Balagha, Sobhi Saleh, Qum, Dar al-Hijrah, 1414 H.
  • Diwan al-Imam Ali, bincike na Abdul Moneim Khafaji, Diwan al-Imam Ali, Dar Ibn Zaidoon, B.
  • Ibn Abi al-Hadid, IzzulDin Abu Hamid, Sharhi Nahj al-Balagha, Qum, Ayatullah Murashi Najafi Public Library, 1404H.
  • Ibn Jozi, Yusuf bin Ghazaughli, Tazkira al-Khawas min umma, da ambaton sifofin Imamai, Qum, Al-Majjam al-Alami, Lahlul-Bait, amincin Allah ya tabbata a gare su, 1426H.
  • Ibn Maitham Bahrani, Maitham bin Ali, Ikhtiayr Misbah al-Salkin; Sharhin Nahj al-Balagha al-Wasit, bincike na Mohammad Hadi Amini, Mashhad, Astan Quds Razavi Islamic Research Foundation, 1366.
  • Hosseini Khatib, Seyyed Abdul Zahra, Masadir Nahj al-Balagha wa Asanideh, Beirut, Dar al-Azwa, 1985.
  • Khoi, Abolqasem, Minhaj al-Baraa', Tehran, Islamic School, 1358.
  • Dashti, Mohammad, da Kazem Mohammadi, Al-Mujajm Al-Mufars na Al-Faz Nahj al-Balaghah, Kum, Amirul Mominin Cultural Research Institute, 1375.
  • Tabari Amoli Saghir, Muhammad bin Jarir bin Rostam, Dala'il Al-Imamah, Qum, Ba'ath, 1413H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Mali, Qum, Dar al-Thaqaft, 1414H.
  • Abdo, Muhammad, Sharh Nahj al-Balagha, Alkahira, Al-Istiqama Press, Beta.
  • Faizul-Islam, Ali Naqi, Tarjameh wa Sharhn Nahjul-Balagha, Tehran, Faizul-Islam Publications, 1371.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Payam Imam Amir al-Mominin, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1386.