Huɗuba Ashbahu

Daga wikishia

Huɗuba Ashbahu (Larabci: خطبةالأشباح) ɗaya ce daga jerin huɗubobin cikin nahajul balaga da suke Magana game da batun sanin Allah, Ibn Abil Al-hadid cikin bayaninsa game da irin ƙima da muhimmancin da wannan huɗuba take da shi yana cewa: misalin bambancin da yake tsakanin wannan huɗuba da misalin zancen laraba mai cike da fasaha kamar misalin bambancin da yake tsakanin ƙasa da zinare ne, Sayyid Ibn Ɗawus bisa lura da ƙimar matanin wannan huɗuba, ya ce babu kokwanto ko kaɗan game da ingancin wannan huɗuba.

wannan huɗuba baya ga nahajul balaga ta zo cikin sauran madogaran shi'a da ahlus-sunna, ba'ari daga cikin bahasosi da aka bijiro da su a wannan huɗuba su ne kamar haka: siffofin Allah, kasancewar kur'ani ma'auni cikin sanin sunayen Allah da siffofinsa, rashin tsinkayen mutum kan zatin Allah da siffofinsa, halittar mala'iku, siffofi da halayensu, tsinkayen ubangiji kan bakiɗayan sirrikan ɗan Adam.

An rubuta litattafai daban-daban game da wannan huɗuba, daga jumlarsu: Ali (A.S) Wa Salikin Rahe Shaiɗan (Faujul Muƙtaham), talifin Abdul-Ali Guyasti.

Gabatarwa

Huɗuba Ashbahu ɗaya ce daga jerin huɗubobin cikin nahajul balaga da suke cike da maɗaukakan ma'anoni.[1] Ibn Abil Al-hadid ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta sharhi kan nahajul balaga, cikin bayanin balaga da fasahar wannan huɗuba ya ƙiyastata da zancen larabawa da yake cike da fasaha , ya ce misalin wannan huɗuba da misalin zancen larabawa da yake cike da fasaha kamar misalin ƙasa da zallan zinare ne.[2]

Bisa naƙalin Sayyid Radiyu wanda ya haɗa littafin nahajul balaga, Imam Ali (A.S) ya yi bayanin wannan huɗuba ne lokacin da wani mutum ya buƙaci ya siffanta masa Allah, an ce yana so Imam ya siffanta masa Allah kamar yana ganinsa a gaban idanunsa, kan asasin wannan naƙali Imam Ali (A.S) wannan buƙata da wannan mutumi ya yi daga gare shi ta fusata shi matuƙa, ya tara mutane yah au mimbarin masallacin kufa ya yi wannan huɗuba.[3] game da mene ne ya fusata shi daga roƙonsa da wannan mutumi ya yi, an bijiro da uzurori daban-daban, daga jumlarsu akwai tsammanin cewa wannan mutumi yana jira Imam ya yi siffanta masa Allah da siffofin halittu domin ya samu damar ganin Allah ko suranta shi a kwakwalwarsa[4] da kuma cewa ta yiwu duk da cewa musulmi sun ɗau dogon lokaci suna rayuwa kan fahimtar addinin muslunci amma tare da haka har zuwa yanzu ba su fahimci siffofin Allah ba.[5]

Lambobin jerin wannan huɗuba cikin mabambantan kwafi-kwafin na nahajul balaga:[6]

Sunan Kwafi Lambar Huduba
Al-mujam Al-mufahras, Subhi salihu 91
Faizul Al-islam, Sharhu Khuui, Mulla Salihu Mazandarani, Ibn Abil Al-hadid 90
Ibn Maisam 88
Abduhu 87
Mulla Fatahullahi 97
Fi Zilal 89

Sanya Suna

An ambaci bayanan da za su a ƙasa game da dalilin sanyawa huɗubar suna Ashbahu:

  • ”Ashbahu” kinaya ce kan mala'iku kuma wani sashi daga huɗubar ya ƙunshi wannan batu;[7]
  • Kalmar “Ashbahu” da aka yi amfani da ita cikin wannan huɗuba ta zo daga ba'arin naƙali [8] ba daga nahajul balaga ba,[9]
  • Ashbahu ma'ana duk wani da ake hango inuwarsa daga nesa ba tare da tantance haƙiƙaninsa ba; sakamakon cikin wannan huɗuba an kawo abubuwa da ba su bayyanu ba sosai ga mai sauraro aka kirata da suna Ashbahu.[10]

Abin da Yake Ciki

Ba'arin bahasosi da aka yi bayaninsu cikin wannan huɗuba, sun kasance kamar haka:

  • Ambato ba'arin siffofin Allah,
  • Kasancewar kur'ani ma'auni cikin sanin sunaye da siffofin Allah,
  • Rashin tsinkaye ɗan Adam kan haƙiƙanin zati da siffofin Allah,
  • Halittar sammai tare da ɗaukaka,
  • Halittar mala'iku da ke ɓantattun siffofinsu,
  • Halittar ƙasa, halittar Annabi Adam (A.S) da aiko da Annabawa;
  • Tsinkayen Allah kan bakiɗayan sirrikan ɗan Adam.[11]

Inganci

A imanin Sayyid Ib Ɗawus marubucin Farajul Al-mahmum, cikin auna ingancin wannan huɗuba babu buƙatar bahasi da bincike game da isnadinta, saboda matanin wannan huɗuba ya girmama da babu wanda zai iya bayanin waɗannan lafuzza sai wanda ya kasance ma'asumi.[12] huɗuba ashbahu tana cikin shahararrun huɗubobin Imam Ali (A.S) da suka shahara tun kafin Sayyid Radiyu ya haɗa littafin nahajul balaga.[13] wannan huɗuba ƙari kan naƙalto ta cikin madogaran shi'a misalin Kitabul At-tauhid na Shaik Saduƙ[14] da Taisiru Al-maɗalib na Yahaya ɗan Husaini Haruni daga malaman zaidiyya[15] an naƙalto a litattafan ahlus-sunna misalin Al-iƙdul Al-farid [16] da Rabi'ul Al-abrar.[17]

A cewar Sayyid Abdul-Zahra Al-husaini Al-khaɗib marubucin littafin Masadir Nahji Al-balaga, Sayyid Radiyu ya naƙalto wannan huɗaba ne daga littafin “Khuɗab Amiril Al-muminin (A.S), talifin Mas'adatu ɗan Sadaƙa; saboda a wani ɓangare, Sayyid Radiyu a farkon wannan ya yi bayani ƙarara a fili cewa ya naƙalto ta ne daga Mas'adatu ɗan Sadaƙa daga Imam Sadiƙ (A.S), a wani ɓangare daban kuma Mas'adatu an ce Mas'adatu yana littafi mai suna “Khuɗab Amiril Al-muminin, wannan littafi yana nan har zuwa zamanin Sayyid Hashim Bahrani marubucin Kitabul Al-burhan.[18]

Nazari

Littafin Tabi'at Dar Kutbe Ashba, Na Muh'sin Sitaregi

An rubuta litattafai daban-daban game da huɗuba Ashbahu, daga jumlarsu za a iya ishara da sunaye wanda za su a ƙasa:

  • Ali (A.S) Wa Salikine Rahe Shaiɗan (Fauju Muƙtaham), talifin Abdul-Ali Guya: kamfanin Dalilima suka buga shi a shekara ta 2007 m, littafi ne da yake ɗauke da shafuka 424.[19]
  • Ɗabi'at Dar Khuɗbeh Ashbahu Nahje Al-balaga, na Muhsin Sataregi, kamfanin Intisharat Desara a garin Rashti suka buga wannan littafi mai ɗauke da shafi 160.[20]