Hamimu

Daga wikishia

Hamimu, (arabic: حميم) ma’ana zafi mai tsanani, cikin Alkur’ani ishara ta zo kan wannan kalma da ma’anar tafashashen ruwa da ake shayar da ƴan Jahannama da shi, haka kuma wannan kalma wani lokaci tana bada ma’anar mutum mai kusanci da kai, wannan kalma ta zo sau ashirin cikin Alkur’ani. [1] Malaman Tafsiri da Masu nazarin Alkur’ani sun tafi kan cewa kalmar “Hamimu” tana da ma’ana guda biyu: Tafashashen ruwan zafi, [2] da ake shayar da ƴan Jahannama da shi, 3 Hamimu cikin aya ta 57 Suratul Sad.

(هَذَا فَلْیذُوقُوهُ حَمِیمٌ وَ غَساقٌ)

Wannan kenan to su ɗanɗane shi ruwan zafi da ruɓaɓɓen jini. [3] Da kuma cikin suratul Yunus aya ta. [4]

(وَ الَّذِینَ کفَرُوا لَهُمْ شَرَابٌ مِنْ حَمِیمٍ وَ عَذَابٌ أَلِیمٌ بِمَا کانُوا یکفُرُونَ)

Kuma waɗanda suka kafirce suna da abin sha daga ruwan zafi da kuma azaba mai raɗaɗi sakamakon abin da suka kasance suna daga kafirci. [5] Kan wannan ma’ana ne take shiryarwa, Fakhrur razi cikin littafin tafsirinsa mai suna Mafatihul Al-Gaibi ya naƙalto cewa abin da ake nufi da Hamimu a wannan aya shi ne narkakkiyar tagulla. [6] Mutumin da yake da kusanci da mutum, kamar yanda ya zo a aya ta 101 suratul Shu’ara

(وَ لَا صَدِیقٍ حَمِیمٍ)

Kuma bamu da Aboki Masoyi. [7] Cikin aya ta 10 suratul Ma’arij

(وَ لَا یسْأَلُ حَمِیمٌ حَمِیمًا)

Kuma Aboki Masoyi baya tambayar inda Abokinsa Masoyi yake. [8] tana shiryar kan wannan ma’ana, Malaman tafsiri cikin wannan aya sun fassara Hamimu da makusanci [9] masoyi mai tausayawa [10] makusanci da yake bibiyar mas’aloli da matsalolinka ya warware su, [11] makusanci da yake baka goyan baya, [12] Hassan Musɗafawi wanda ya rasu shekara ya 1384 h shamsi, marubucin littafin Al-Tahƙiƙu fi Kalimati Alkur’ani Al-karim, ya tafi kan cewa kalmar Hamimu tana da wasu adadin ma’anoni, daga cikinsu: zafi mai tsanani, kusanci da hallara, wani nau’in murya da niyya da dukkaninsu suke komawa ga wannan ma’ana ta zafi mai tsanani, idan ka samu ana kiran wata idaniyar ruwa da sunan Hamimu an kirata ne da haka sakamakon ruwa mai zafi da take tare da shi, idan ka samu wani yana amfani da kalmar Hamimu kan mutumin da yake da kusanci da shi, ya faɗi hakan sakamakon soyayya da alaƙarsa da shi. Haka kuma idan an yi amfani da Hamimu game da gawayi, to domin itacen ya yi baki ya koma garwashi saboda tsananin zafi da wuta, [13] Saboda haka, Hamimuu yana nufin wani abu mai zafi da zafi; Ko zafi na zahiri kamar ruwan zafi ko zafin ma'anawi a cikin misalin aboki da waliyin mutum. [14]

Bayanin kula

  1. Qureshi, Kamus na Alqur’ani, 1371, juzu’i na 2, shafi na 184.
  2. Rajeb Esfahani, Al-Mufradat, 1412 AH, shafi na 254; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 643, juzu'i na 4, shafi na 492; Sheikh Tusi, al-Tabayan, Beta, juzu'i na 10, shafi na 244; Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 30, shafi na 9; Maraghi, Tafsir al-Maraghi, Beta, juzu'i na 30, shafi na 13; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 150.
  3. Jurjani, Jala al-Azhan, 1377, juzu'i na 8, shafi na 154.
  4. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 320.
  5. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 8, shafi na 221.
  6. Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420H, juzu'i na 31, shafi na 17.
  7. Ibn Jozi, Zad al-Masir, 1422H, juzu'i na 3, shafi na 343.
  8. Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 29, shafi na 46.
  9. Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 19, shafi na 56; Ibn Haim, al-Tabayan, 1423 AH, shafi na 322; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 10, shafi na 37; Shabbar, tafsirin al-kur'an al-Azeem, 1412 AH, shafi na 532.
  10. Rajeb Esfahani, Al-Mufradat, 1412 AH, shafi na 255; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 531; Siyuti, Al-Durrul Al-Manthor, 1404 AH, juzu'i na 5, shafi na 91; Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 Hijira, juzu'i na 12, shafi na 313.
  11. Andalusia, Muharrar al-Alwajiz, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 236; Andalusi, Al-Bahar Al-Muhait, 1420 AH, juzu'i na 8, shafi na 138; Tabarsi, Jameed al-Jame, 1377, juzu'i na 3, shafi na 163.
  12. Sheikh Tusi, Al-Tibyan, Beta, juzu'i na 8, shafi na 37 da juzu'i na 10, shafi.117; Alousi, Ruh Al-Ma'ani, 1415 Hijira, juzu'i na 12, shafi na 313.
  13. Mostafavi, Tahaqiq, 2013, juzu'i na 2, shafi na 287.
  14. Mostafavi, Tahaqiq, 2013, juzu'i na 2, shafi na 288.

Nassoshi

  • Alousi, Sayyid Mahmoud, Ruh Al-Ma'ani fi Tafsiri Qur'an Al-Azeem, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1415H.
  • Alqur'an Al-Kareem.
  • Andalusi, Abu Hayyan, Bahrul Muhait, Beirut, Darul Fikr, 1420H.
  • Andulsi, Ibn Attiyah, Al-Muharrar Al-wajiz fi Tafsir Al-Kitab Al-Aziz, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1422H.
  • Ibn Ha'im, Ahmad ibn Muhammad, Al-Tibyan fi Tafsir Gharib Al-Qur'an, Beirut, Dar al-Gharb al-Islami, 1423H.
  • Ibn Jozi, Abd al-Rahman bin Ali, Zad al-Masir fi ilmi Al-tafsir, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1422H.
  • Ibn Manzoor, Lasan Arab, Beirut, Darul Fikr-Dar Sadr, 1414H.
  • Jurjani, Hossein bin Hassan, Jala-ul-Azhan wa Jala-e-Ahzan, Tehran, Jami'ar Tehran, 1377.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1374.
  • Maraghi, Ahmed bin Mustafa, Tafsir al-Maraghi, Beirut, Dar Ihaa al-Tarath al-Arabi, Bita.
  • Mostafavi, Hassan, Al-Tahqiq fi Kalamat Al-Qur'an Al-Karim, Tehran, Kamfanin Fassara da Bugawa, 1360.
  • Qurashi, Sayyed Ali Akbar, Qamus Qur'an, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1371.
  • Rajeb Esfahani, Hossein bin Muhammad, Al-Mufradat fi Gharib Al-Qur'an, Damashq, Darul Alam, 1412H.
  • Razi, Fakhr al-Din, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Shabbar, Sayyid Abdullah, Tafsirin Qur'an al-Azeem, Beirut, Dar al-Balagha, 1412 AH.
  • Siyuti, Jalaluddin, Aldurrul Al-Manthor, Qom, Marashi Najafi, 1404H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Tafsirin Qur'an, Beirut, Darul Marafa, 1412H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Jameed Al Jame, Tehran University da Qum Seminary Management Center, 1377.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow, 1372.
  • Tarihi, Fakhreddin, Majma Al-Baharin, Tehran, Mortazavi, 1375.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Zamakhshari, Mahmoud, Al-Kashaf an haqa'iq Ghawamaz Al-Tanzil, Beirut, Dar al-Katb al-Arabi, 1407H.