Jump to content

Haihata Minna Azzilla

Daga wikishia

Haihata minna azzilla, ma'ana ba za mu taɓa yarda da ƙasƙanci ba, wata sananniyar jumla ce daga sashen huɗubar Imam Husaini (A.S) a ranar Ashura da ya faɗawa sojojin Umar Bin Sa'ad.[1]

Kan asasin madogaran tarihi, Imam Husaini (A.S) ya faɗi wannan jumla ne lokacin da yake ba da amsa ga Ibn Ziyad sa'ad da ya bawa Imam zaɓi ciki ɗayan biyu ko dai ya miƙa wuya ko kuma su yaƙe shi.[2] Ya bayyana cewa Allah da Annabi (S.A.W) da hankula masu lafiya ba sa karɓar ƙasƙanci, ya zaɓi mutuwa cikin mutunci da ɗaukaka kan rayuwa cikin ƙasƙanci da wulaƙanta.[3]

Makokin mutanen Yaman tare da rera taken Haihata minna azzilla a Ranar Ashura

Mas'udi malamin tarihi a ƙarni na huɗu, ya naƙalto wannan jumla cikin wannan shakali kamar haka: Ɗan zina ɗan ɗan zina[Tsokaci 1] ya bamu zaɓi cikin ɗayan biyu, ko dai mu zaɓi kisa ko kuma ƙasƙanci, mu ba zamu taɓa zaɓar ƙasƙanci ba.[4] Tare da haka, ba'arin madogaran sun zo da Kalmar «القتلة» maimakon«القتلة»[5] wasu kuma Kalmar «الدَّنِیئَةُ» maimakon «الذِّلَّة» suka naƙalto.[6]

Haihata minna azzilla, a yau ta zama wani take na `yan gwagwarmaya muslunci. `yanshi'a cikin makoki da muzahara, suna rera wannan take matsayin ba za su taɓa sallamawa girman kan duniya ba.[7]

Bayanin kula

  1. Mas’udi, a cikin littafinsa Isbatul Wasiyya, bugun shekara ta 1384 Hijira Shamsiyya (2005), shafi na 166
  2. Mas’udi, a cikin littafinsa Isbatul Wasiyya, bugun shekara ta 1384 Hijira Shamsiyya (2005), shafi na 166
  3. Mas’udi, a cikin littafinsa Isbatul Wasiyya, bugun shekara ta 1384 Hijira Shamsiyya (2005), shafi na 166
  4. Mas’udi, a cikin littafinsa Isbatul Wasiyya, bugun shekara ta 1384 Hijira Shamsiyya (2005), shafi na 166
  5. Muktalul Husain na Khwarazmi (1381 SH, jildin 2, shafi na 10)
  6. Tuhaf al-Uqul na Ibn Shubah al-Harrani (bugun shekara ta 1404 Hijira, shafi na 241)
  7. Misali, dubi: "Masiratu Ashura Ihya'an Li Zikra Istish'ahadi Al-Imam Husaini,Alaihs Salam, Bil Asimati...", Mu'assasar Al-Shaheed Zayd Ali Mosleh.

Tsokaci

  1. Kinaya ce game da mutumin da ake ce-ce kuce kan asalinsa da danginsa

Nassoshi