Gabobin Sujjada
- Wannan wata qasida ce mai bayyanawa game da Mafhumin fiqihu ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Gabobin Sujjada (arabic: أعضاء السجدة) ko Masajidul Sab'atu (gabbai Bakwai) wasu sassa ne daga gangar jikin Mai sallah a lokacin Sujjada yake dora su kan Kasa, kan asasin ra'ayin Malaman fikihun Shi'a sa'ilin Sujjada dole a dora goshi, Tafin Hannu guda biyu, saman gwiwa da kuma saman yatsun Hannuwa da yatsun kafafu kan kasa, dora Hanci kan Kasa yana daga mustahabbi. Aksarin Malaman fikihu suna kan ra'ayin cewa ba dole ba ne sai dukkanin gabban sun damfara da kasa, bari dai idan suka shafi kasa ya wadatar, na'am shi goshi an togace hukuncinsa, dole ne alal akalla mikdarin dirhami ya damfaru da kasa. Wajibi abin da Mai Sallah zai dora Goshi a kansa ya kasance daga jinsin Kasa da kuma abin da kasar ta tsirar da su da sharadin kada su kasance daga abin da ake ci.
Sanin Mafhumi
Gabban Sujjada ko gabbai bakwai ko Masajidul Sab'atu ko kuma ace wurare guda bakwai daga sassan jiki da ake dora su kan kasa a yayin yin sujjada, wajibi ne su taba kasa [1] wadannan gabbai sun kasance kamar haka: Goshi, Tafin Hannun guda biyu, saman gwiwowin kafa biyu da kuma saman yatsun hannu da saman yatsun kafa [2] ana bahasi kan wadannan gabbai guda bakwai cikin babin Sallah a litattafan fikihu. [3] Hukunce-hukunce ba'ari daga hukunce-hukuncen gabban sujjada sun kasance kamar haka:
- a cewar Yusuf Bahrani Malamin Fikihun Shi'a wanda ya mutu a shekara ta 1186 h Kamari, kan asasin ra'ayin da mashhur daga Malaman fikihun Shi'a suke kai, wajibi ne yayin yin sujjada a dora gabbai bakwai na sujjada a kan kasa. [4]
- alal akalla gabban su shafi kasa a lokacin yin sujjada in banda Goshi shi dole ne ya damfaru da kasa. [5] ba'arin Malaman fikihu sun tafi kan ra'ayin cewa shima goshi idan ya shafi kasa ya tabata ya wadatar. [6] sabanin sauran Malamai da suke ganin wajabcin damfaruwar mikdarin girman dirhami daga Goshi a kan kasa. [7]
- lokacin karanta zikirin Sujjada dago da gabban sujjada bakwai sama bisa ganganci yana bata sallah; [8] kan asasin fatawar Ayatullahi Sistani koda Mai sallah baya cikin halin karanta zikirin Sujjada sai ya dago da daya daga gabban Sujjada guda bakwai sama, bisa Ihtiyadi Wujubi sallarsa ta baci. [9]
Mustahabbai
- dora Hanci kan kasa; Malaman fikihu suna ganin mustahabbi ne a dora saman hanci kan kasa a yayin sujjada. [10] dalili kan wannan hukunci wata riwaya ce da aka nakaltota daga Imam Sadik (A.S) da ya bayyana cewa dora saman Hanci kan kasa yana cikin Sunnar Annabi (S.A.W) [11]-[12] a ra'ayin Allama Hilli dora saman Hanci kan kasa Mustahabbi ne mai karfi [13]
- Thakwiyya: Mustahabbi ne bude Dantse da rashin dora gwiwar hannaye kan kasa a halin Sujjada. [14] haka kuma Mustahabbi ga Mace a halin sujjada ita ta dora gwiwar hannayenta kan kasa tare da damfare gabban jikinta da juna. [15]
Hukunce-hukuncen Gabban Sujjada
Kan asasin ra'ayin Mashhur din Malaman Shi'a, cikin gabban sujjada bakwai kadai Goshi ne ya zama wajibi inda za a dora shi ya kasance tsarkakke daga najasa, [16] na'am Abu Salah Halabi daga Malaman fikihun Shi'a a karni na 4-5 h Kamari, yana ganin wajabcin kawar da najasa daga inda za a dora gabban sujjada bakwai. [17] Mahallin Sujjada inda za a dora goshi a kai wajibi ne ya kasance daga jinsin Kasa ko kuma abin da kasa ta tsirar da sharadin kada su kasance daga abin da ake ci ko ake sawa. [18] madogarar wannan hukunci ya kasance Ijma'in Malaman Fikihu. [19] da wannan dalili ya zama baya inganta a dora Goshi kan abin da ba kasa ba ko abin da ta tsirar, kamar dai Zinare, Azurfa, da dutsen Akik da Fairuz da suka kasance an fito da su ne daga Ma'adanan Kasa. [20]
Bayanin kula
- ↑ muassaseh dayiratul maref fikh islami, mausu'atu fikh islami, 1423 AH, juzu'i na 15, shafi na 108.
- ↑ Bahrani, Al-Hadaeq al-Nadrah, 1363, juzu'i na 8, shafi na 276.
- ↑ Misali, duba Tabatabaei Yazdi, al-urwa al-Wughta, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 176.
- ↑ Bahrani, Al-Hadaeq al-Nadrah, 1363, juzu'i na 8, shafi na 276
- ↑ Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1363, juzu'i na 8, shafi.277
- ↑ Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 218.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 10, shafi na 144.
- ↑ Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam, Al-Al-Bait Institute, juzu'i na 1, shafi na 40
- ↑ Sistani,Tauzihul Al-Masa'il, 1415 AH, Juzu'i na 1, shafi na 224.
- ↑ muassaseh dayiratul maref fikh islami, mausu'atu fikh islami , 1423 AH, juzu'i na 18, shafi na 288-289.
- ↑ Hurrul amili, wasa'il al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 6, shafi na 343; Kilini, Al-Kafi, 2007, juzu'i na 6, shafi na 144.
- ↑ Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1363, juzu'i na 8, shafi na 276.
- ↑ Allameh Hilli, Tazkire al-Fuqaha, 1414 AH, juzu'i na 3, shafi na 188.
- ↑ Mohaghegh Karki, Jame Al-Maqassed, 1414 AH, juzu'i na 2, shafi na 306.
- ↑ Mohagheq Karki, Jame Al-Maqassed, 1414 AH, juzu'i na 2, shafi na 365.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wughta, 1417 AH, Mujalladi na 1, shafi na 177.
- ↑ Abu Salah Halabi, Al-Kafi Fiqhu, 1403H, Mujalladi na 1, shafi na 140.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Wughta, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 388.
- ↑ Sabzevari, Mahezzab Al-Ahkam, 1413 AH, juzu'i na 5, shafi na 434.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wughta, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 389.
Nassoshi
- Abu Salah Halabi, Taqi al-Din bin Najm al-Din, Al-Kafi fi Fiqh, Isfahan, Maktabatu Imam Amirul Mumineen, 1403H.
- Allameh Hali, Hasan bin Yusuf, Tahrir al-Ahkam, Mashhad, Al-Bait Institute, bugun farko, beta.
- Allameh Hali, Hasan bin Yusuf, Tazkire al-Faqha, Qum, Al-Bait Institute, 1414H.
- Bahrani, Yusuf bin Ahmad, al-Hadaiq al-Nadrah, Qum, Al-Nashar al-Islami Institute, 1363.
- Hurrul aamili, Muhammad bin Hassan, wasa'il al-Shia, Qum, Al-Al-Bayt Institute, 1416H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, Kum, Darul Hadith, bugun farko, 1387.
- Mohagheg Karki, Ali bin Hossein, Jame Al-Maqassed, Qom, Al-Bait Institute, bugu na biyu, 1414H.
- Najafi, Mohammad Hassan, Jawaher Al-Kalam, Beirut, Dar Ahya Al-Trath Al-Arabi, bugu na 7, 1362.
- Sabzevari, Sayyid Abdul-Ali, Mahezzab Al-Ahkam, Qom, Darul Tafsir, bugu na 4, 1413H.
- Shahid Thani, Zain al-Din bin Nur al-Din, Masalak al-Afham, Qom, Al-Maarif al-Islamiya Institute, bugu na farko, 1413H.
- Sistani, Sayyid Ali, Tauzihul al-Masa'il, Kum, Mehr Publications, 1415H.
- Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa al-Wughqa, Qom, Al-Nashar al-Islami Institute, bugu na farko, 1417H.
- , Qum, muassaseh dayiratul maref fikh islami, mausu'atu fikh islam tabdakn li mazhab Ahlil-baiti (A.S), bugu na farko, 1423 Hijira.