Du'a'u Ifɗar

Daga wikishia

Addu'ar buɗa baki, (Larabci: دعاء الإفطار) Addu'a ce da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W)[1] da Imam Ali (A.S) wace ake karantawa a lokacin buɗa baki.[2] cikin wannan addu'a ana magana da Allah ana ce masa ya Allah kaɗai domin kai na yi wannan azumi kuma kan arziƙinka ne nake yin buɗa baki.[3] bayan nan sai a roƙi Allah da ya karɓi wannan ibada.[4] a cewar ba'arin masu sharhin wannan hadisi, ma'anar addu'ar buɗa baki shi ne cewa mun ɗauki azuminmu ne domin Allah, sakamakon Allah ne kaɗai mai azurtawa sai muka amfana daga arziƙinsa, kuma shi kaɗai za mu bautawa.[5] Wannan addu'a ta zo cikin madogaran riwaya a sashe ayyukan da ake yi cikin watan ramadan, amma riwayoyin da suka kawo wannan addu'a ba su keɓance ta da iya watan ramadan ba.[6] ya zo cikin riwayoyi cewa Annabi (S.A.W) bayan karanta wannan addu'a ya ce: wahala da ƙishirwar azumin sun tafi, amma ladansa yana nan.[7] a cikin ba'arin naƙali farkon wannan addu'a ya fara da bismilla.[8]

Nassin Addu'a

بِسْمِ اللَّه‏ اللَّهُمَ‏ لَكَ‏ صُمْنَا وَ عَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْنَا فَتَقَبَّلْ [فَتَقَبَّلْهُ] مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيم

Da sunan Allah Mai rahama mai kai ya Allah domin kai muka yi azumi kuma kan arziƙinka muka yi buɗa baki, muna roƙonka ka karbi ibadar da muka yi, lallai kai mai ji ne kuma masani.[9]

Bugu da ƙari an naƙalto wannan addu'a daga Imam Rida (A.S) sai dai cewa wani miƙdari daga abin da ya zo cikin yafi faɗaɗa da ɗan bambanta daga ta farko[10] [Tsokaci 1] wata addu'a daban da ita ma take kamanceceniya da wannan addu'a wace ake yin lokacin buɗa baki da Imam Kazim (A.S) ya naƙalto daga Annabi (S.A.W). magana ta zo game siffanta wannan addu'a da kuma ladanta da cewa duk wanda ya karanta wannan addu'a, zai samu ladan duk wanda suka yi azumi a wannan rana.[11] nassin wannan addu'a shi ne kamar haka:

اللَّهُمَ‏ لَكَ‏ صُمْتُ‏ وَعَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْتُ وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْت

Ya Allah domin kai na azumci wannan rana da kuma kai na dogara.[12]

Bayanin Kula

  1. Ibn Sani, Amalul Al-yaum wa Laila, Jeddah, shafi na 430.
  2. Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 200.
  3. Azimabadi, Aun al-Maboud, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 346.
  4. Darqtani, Sunan al-Darqtani, 1424 AH, juzu'i na 3, shafi na 156.
  5. Zidani, al-Mufatih, 1433 AH, juzu'i na 3, shafi na 24.
  6. Misali, duba: Ibn Babouyeh, Man La Yahdrah al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 2, shafi na 106; Ibn Hayyun, Dua'i al-Islam, 1385H, juzu'i na 1, shafi na 280.
  7. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 95.
  8. Tusi, Tahzib al-Ahkam, 1407 BC, juzu'i na 4, shafi na 200.
  9. Ibn Tawus, Iqbal al-A’mal, 1409 AH, juzu’i na 1, shafi na 116.
  10. Misali, duba: Ibn Babouyeh, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, 1396H, shafi na 96.
  11. Bin Tawoos, Iqbal al-Amal, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 117.
  12. Majlesi, Zad al-Maad, 1423H, shafi na 85.

Tsokaci

  1. اللَّهُمَ‏ لَكَ‏ صُمْنَا بِتَوْفِيقِكَ وَ عَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْنَا بِأَمْرِكَ فَتَقَبَّلْهُ مِنَّا وَ اغْفِرْ لَنَا إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِيم

Nassoshi

  • Ibn Babouyeh, Muhammad Bin Ali, Fadael al-Ashahr al-Thulasa, bincike na Gholamreza Irfanian Yazdi, Kum, kantin sayar da littattafai na Davari, bugun farko, 1396H.
  • Ibn Babouyeh, Muhammad bin Ali, Man la Yahzara al-Faqih, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyu, 1413 AH.
  • Ibn Hayyun, Nu'man bin Muhammad al-Maghrebi, Da'aim al-Islam, bincike na Asif Faizi, Qum, Al-Bait Institute, bugu na biyu, 1385H.
  • Ibn Sani, Ahmad bin Muhammad, A'mal al-Yaum wal Lailah, bincike na Kausar Barani, Jeddah, Dar al-Qibla for Islamic Culture, Beta.
  • Ibn Tawoos, Ali bin Musa, Iqbal al-Amal, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na biyu, 1409H.
  • Darqtani, Ali bin Omar, Sunan al-Darqtani, bincike na Shoaib Arnout da sauransu, Beirut, Mu’assasar Al-Rasalah, bugu na farko, 1424H.
  • Zidani, Hossein bin Mahmoud, al-Mufatih fi Sharh al-Masabih, bincike na Noor al-Din Talib, Kuwait, Darul Wader, bugun farko, 1433H.
  • Tusi, Muhammad bin Al-Hassan, Tahzeeb al-Ahkam, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Azeemabadi, Mohammad Ashraf bin Amir, Aunul Al-Ma'aboud: Sharhin Sunan Abi Dawud da Ibn Qayyim, Tahzib Sunan Abi Dawud, Beirut, Darul Kitab al-Alamiya, bugu na biyu, 1415 bayan hijira.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Majlesi, Mohammad Baqir, Zadul al-Ma'ad: Miftah al-Jinan, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, bugu na farko, 1423 AH.