Dauma ƴar Wahab
Dauma ƴar Amru ɗan Wahab(Larabci:دومة بنت عمرو بن وهب) mahaifiyar Mukhtar ɗan Abi Ubaidu Assaƙafi. An kashe ta a lokacin yaƙin Al-Mukhtar tare da Mus'ab ɗan Zubairu.
Nasabarta da Auranta
Ita ce Dauma ƴar Amar ɗan Wahab ɗan Mu'attib ɗan Wahab ɗan Ka'ab al-saƙafi.[1] Wasu sun ambaci nasabarta ta hanyar cire wani sashe, sai suka ce sunan babanta Wahab Mu'attib.[2]Aamma ya bayyana cewa an cire sunan Amar ne bisa kuskure.[3] Dauma ta auri Abu Ubaidu Assaƙafi,[4] a wasu rahotanni, Abu Ubaidu baban Mukhtar lokacin da ya shagalu da zaɓar mata da zai aura cikin matan mutanensu,ya yi taƙoƙari har sai da ya yi mafarki wani yana ce masa ya auri Dauma.[5]
Ƴaƴanta
- Mukhtar: an haife shi a shekara ta farkon hijira,[6] kuma ya tashi ya yi wa Banu Umayyawa tawaye yana neman fansar jinin Imam Husaini (A.S).[7]
- Jubair
- Abu Jubair
- Abu Hakam Abu Umayya.[8]
Mafarkin Dauma
An danganta wani mafarki ga Dauma game da cikinta tare da zaɓaɓɓen ɗanta, Lokacin da take da cikin ɗanta mai suna Mukhtar, ta ga wani mutum a mafarki yana ce mata:
Tarjama: Ki yi murna da yaron nan wanda ya fi komai kama da Zaki. yayin da mazaje ke takaddama cikin abubuwa marasa muhimmanci, to shi abu mafi tsada da daraja yana kasancewa cikin rabonsa .[9]
Bayan haihuwar Mukhtar, ta yi da'awar mafarki, cikin wannan mafarki an sanar da ita cewa yaronta zai samu mabiya masu yawan gaske[10] babu tabbacin ingancin danganta wannan mafarki zuwa gare ta.
Kasancewa Tare da Mukhtar
Ɗan Ɗaifur ya ambace ta a cikin Balaghat Al-Nisa cewa tana da kwarewa cikin balagar zance, lokacin da aka kewaye fadar Mukhtar da sahabbansa, ta kasance tare da da shi, sai abokan gaba suka bata dama ta miƙa wuya domin ta tsira da ransa, amma ta ƙi miƙa wuya.[11]
Bayanin kula
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375; Ibn Juzi, al-Muntazem, 1412 AH, juzu'i na 6, shafi na 67.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 439.
- ↑ Thaghafi Kofi, Al-Gharat, 1353, juzu'i na 2, shafi na 517, bayanin ƙasa.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375; Ibn Juzi, al-Muntazem,
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375; Ibn Juzi, al-Muntazem,
- ↑ Tarikh Ibn Khaldoun/fassarar, juzu'i na 2, shafi na 44
- ↑ Ibn Nama Hilli, Zob Al-Nazar, 1416H, shafi na 60.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 375; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 350.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 6, ku. 375; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 45, ku. 350.
Nassoshi
- Ibn Khaldoun, Abdurrahman Ibn Khaldoun, Mukadimmadtu Ibn Khaldoun, wanda Mohammad Parvin Gonabadi ya fassara, Tehran, wallafe-wallafen kimiyya da al'adu, babi na 8, 1375.
- Mehlati, Zabihullah, Riyahin al-Sharia, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na biyar, 1368.
- Balazari, Ahmad bin Yahya, Jamal Min Ansab al-Ashraf, wanda Sohail Zakar da Riaz Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, bugun farko, 1417H/1996 miladiyya.
- Ibn Juzi, Abd Al-Rahman bn Ali, al-Muntazem fi Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, bincike: Muhammad Abd al-ƙader Atta da Mostafa Abd al-ƙader Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na farko, 1412 AH/1992 AD.
- Ibn Nama Hilli, Jafar bin Muhammad, Zob Al-Nazar fi Sharh Al-Nathar, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1416H.
- Ibn Tefur, Ahmad bin Abi Tahir, Balagat Al-Nisa, Bincike: Youssef Beƙa'i, Beirut, Darul-Azwa, 1420H/1999 Miladiyya.
- Majlesi, Muhammad Baƙir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Tarat Al-Arabi, 1403H.
- Thaƙfi Kofi, Ibrahim bin Mohammad, Al-Gharat, bincike: Jalaluddin Hosseini Ermoi, Tehran, National Artifact Association, 1353.