Jump to content

Daƙiƙa:Yin Tsadar Kaya

Daga wikishia

Yin tsadar kaya na nufin sayar da kaya ko ba da wani sabis a farashin da ya wuce farashin da aka ƙayyade,[1] ko kuma karɓar kuɗi fiye da yadda aka saba ko abin da ya dace bisa adalci.[2] Haka kuma, duk wani mataki da yake jawo wa mai sa ya ƙarin kuɗin da bai dace ba ana ɗaukarsa a matsayin yin tsadar kaya.[3]

A cikin fiƙihun Musulunci, ana tattauna yin tsadar kaya a ƙarƙashin batun gabnu (Yaudara ta fuskar farashi) da kuma haƙƙin soke ciniki sakamakon hakan.[4] Bisa wannan, idan mai sayarwa ya sayar da kaya a farashin da ya fi ainihin ƙimarsa, alhali mai saya bai san ainihin farashin ba, to gabnu ya tabbata, kuma mai saya yana da haƙƙin soke cinikin.[5]

A cikin ruwayoyi, an yi kakkausar suka ga yin tsadar kaya. An ruwaito daga Annabi Muhammad (S.A.W) cewa jawo tsadar kaya a kasuwar Musulmi yana sa mutum ya cancanci azabar Allah.[6] Haka kuma, wasu ruwayoyi sun bayyana cewa sauƙin farashi alama ce ta yardar Allah, yayin da tsadar kaya alama ce ta fushinSa.[7] A wata ruwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ma, an bayyana samun ribar da ta wuce ƙima a matsayin abin ƙi.[8]

Malaman fiƙihu sun bambanta ra'ayi game da hukuncin yin tsadar kaya. Wasu, bisa dogaro da wasu ruwayoyi, musamman hadisin:«غَبْنُ المُسْتَرْسِلِ سُحْتٌ» (Kuɗin da aka samu ta hanyar yaudarar wanda ya amince da mai sayarwa haramun ne).[9] sun ce yin tsadar kaya haramun ne.[10]

A cewar Faizul Kashani, mustarsil shi ne mutumin da yake dogara ga mai sayarwa wajen tantance farashi.[11] Saboda haka, yaudarar irin wannan mutum wani nau'i ne na gabnu,[12] kuma cinikin da ya ginu a kan irin wannan yaudara haramun ne kuma ba ingantacce ba ne.[13]

A gefe guda kuma, wasu malaman fiƙihu sun ɗauki cewa asalin cinikin ingantacce ne, amma wanda aka cuce shi yana da haƙƙin soke cinikin.[14]

Imam Khomaini[15] da Sayyid Ali Khamna'i[16] sun bayyana cewa yin tsadar kaya bai halatta ba idan yana ƙunshe da zaluntar mai saya ko kuma ya saɓa wa dokokin gwamnatin Musulunci.

Sayyid Ali Sistani ya ce idan bai saɓa wa al'ada da ƙa'idoji ba, yana iya halatta ta fuskar fiƙihu, amma ta fuskar ɗabi'a abin ƙi ne.[17]

Nasir Makarim Shirazi kuma yana ganin cewa adadin riba ya dogara ne da yardar ɓangarorin biyu, sai dai idan hukumomi sun ƙayyade farashin kaya ko sabis.[18]

Safi GulFaigani ma yana ganin ingancin ciniki ya ta'allaka ne da yardar mai saya da mai sayarwa; amma idan gabnu ya tabbata, mai saya yana da haƙƙin soke cinikin.[19]

A cikin ilimin Kalam, ana tattauna batun tsada da sauƙin farashi a ƙarƙashin bahasin Is'ar (ƙayyade farashi), ta fuskar ko Allah ne tushensa ko kuma mutane ne suke haddasa shi.[20] Ash'ariyawa, bisa ra'ayinsu cewa dukkan ayyukan bayi halittun Allah ne, sun jingina tsada da sauƙin farashi ga Allah.[21] Amma malaman Kalam na Shi'a suna ganin cewa idan tsadar kaya ta samo asali ne daga ayyukan mutane, to alhakin hakan yana kansu ne.[22]

An kuma bayyana yin tsadar kaya a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara tsananta rayuwar masu ƙaramin ƙarfi a cikin al'umma.[23] Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na biyu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana yin tsadar kaya a matsayin zalunci, kuma ya ce yaƙi da shi yaƙi ne da zalunci.[24]

A tsarin dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuwa, an bayyana ma'anar yin tsadar kaya tare da ɗaukarsa a matsayin laifi a cikin Dokar Ta'azirori ta Gwamnati (wadda aka amince da ita a shekara ta 1367Sh) daidai da 1988 M.[25] da kuma Dokar Tsarin Kasuwanci (wadda aka amince da ita a shekara ta 1392Sh) wanda ya zo daidai da 2013 M, inda aka tanadi hukuncin da ya dace ga masu aikata hakan.[26]

A dokokin Najeriya, ƙara farashin kaya ba haramun ba ne gaba ɗaya, domin farashi yana canzawa bisa yanayin kasuwa. Amma doka ta hana ƙara farashi ta hanyar zalunci, yaudara, boye kaya domin jawo ƙaranci, ko haɗa kai wajen ɗaga farashi.

Dokar Kare Haƙƙin Masu Amfani ta Najeriya (FCCPA, 2018) tana kare masu saye daga ayyukan kasuwanci marasa adalci, kuma hukumar FCCPC tana da ikon bincike da ɗaukar mataki idan ‘yan kasuwa suka yi amfani da jama'a.

A jihohin Arewa masu amfani da Shari'ar Musulunci, wannan batu yana da alaƙa da ka'idojin fikihu kamar hana zalunci (darar), hana yaudara (ghish), da hana ɓoye kaya domin ƙara farashi (ihtikar). Don haka, Musulunci ya amince da riba, amma ya hana cin moriyar wahalar jama'a ta hanyar tsadar kaya marar adalci.[27]

Batutuwa Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. ↑ Markaze Pajuhesh-haye Majlisi Shuraye Islami, Qanune Ta'azirate Hukumati, sashe na 2.
  2. ↑ Haƙiƙi, «Dar Waraye Geranfurushi Wa Ihtikar,» shafi na 25.
  3. ↑ Markaze Pajuhesh-haye Majlisi Shuraye Islami, Qanune Ta'azirate Hukumati, sashe na 2.
  4. ↑ Hilli, Tabsiratul Muta'allimin, shafi na 123; Khomaini, Tahrirul Wasila, juzu'i na 1, shafi na 522.
  5. ↑ Shaik Ansari, Kitabul Makasib, juzu'i na 5, shafi na 157.
  6. ↑ Nishaburi, Al-Mustadrak Alas Sahihaini, juzu'i na 2, shafi na 15.
  7. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 5, shafi na 162.
  8. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 10, shafi na 48–50.
  9. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 10, shafi na 24.
  10. ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 17, shafi na 456.
  11. ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 17, shafi na 456.
  12. ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 17, shafi na 456.
  13. ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 17, shafi na 456.
  14. ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 17, shafi na 457.
  15. ↑ Khomaini, Istifta'at, juzu'i na 2, shafi na 62; Imam Khomaini, Sahifeye Nur, juzu'i na 6, shafi na 510.
  16. ↑ Ku duba: «Masa'il Mutafarriƙe Tijarat, Su'al 1612,» Shafin Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Ayatullahi Al-Uzma Khamna'i.
  17. ↑ «Aya Geran Furushi Haram Ast?» Shafin Hadana.
  18. ↑ «Mu'amale Salaf,» Shafin Ittala Rasani Ayatullahi Makarim Shirazi.
  19. ↑ «فتوای آیت‌الله صافی گلپایگانی درباره فروش اجناس به قیمت روز و گران‌تر از قیمت اولیه»، Shafin yanar gizon Shi'a News.
  20. ↑ Hilli, Kashful Murad, juzu'i na 1, shafi na 342.
  21. ↑ Taftazani, Sharhul Maƙasid, juzu'i na 4, shafi na 320.
  22. ↑ Hilli, Kashful Murad, juzu'i na 1, shafi na 342.
  23. ↑ «ریشه گران‌فروشی کجاست؟/ تاملی بر یکی از جدی‌ترین چالش‌های اقتصادی»، Shafin yanar gizon Bashgahe Khabarnegarane Jawan.
  24. ↑ «پیام به رئیس‌ جمهور در خصوص مبارزه‌ با گران‌فروشی»، Shafin Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Ayatullahi Al-Uzma Khamna'i.
  25. ↑ Markaze Pajuhesh-haye Majlisi Shuraye Islami, Qanune Ta'azirate Hukumati, sashe na 2.
  26. ↑ Qanune Nezame Senfiye Keshwar, sashe na 57.
  27. ↑ Officialwebsiteofnigeriangoverment:https://fccpc.gov.ng/fccpc-takes-action-to-address-rising-prices-and-protect-consumers/

Nassoshi

  • «مسائل متفرقه تجارت»، (Mas'aloli daban0daban na kasuwanci), Shafin ofishin Hifze Wa Nashre Asare Ayatullahi Al-Uzman Khamna'i, ranar da aka duba : 9 Agusta 2026M.
  • Qanune Nezame Senfiye Keshwar, wanda aka amince da shi a shekarar 1392Sh, sashe na 57.
  • Markaze Pajuhesh-haye Majlisi Shuraye Islami, Qanune Ta'azirate Hukumati, wanda aka amince da shi a shekarar 1367Sh, sashe na 2.
  • Faizul Kashani, Al-Wafi, Isfahan, Kitabekhune Imam Amir Al-Mu'uminin Ali (Alaihis-Salam), 1406H.
  • Haƙiƙi, Majid, «Dar Waraye Geranfurushi Wa Ihtikar,» (Game da Haramcin Tsadar Farashi da Boye Kaya Domin Tada Farashi.) mujallar Gozarish, lamba ta 47, watan De 1373Sh/994M.
  • Hilli, Hassan Bin Yusuf, Kashful Murad Fi Sharhi Tajrid Al-I'itiƙad, Qom, Cibiyar Annashrul Islami, 1413H.
  • Hilli, Hassan Bin Yusuf, Tabsiratul Muta'allimin, Tehran, Mawallafar Faƙih, bugu na farko, 1368Sh.
  • Khomaini, Sayyid Ruhullahi, Istifta'at, Qom, Jami'e Mudarrisin Hauze Qom, bugu na farko, 1372Sh.
  • Khomaini, Sayyid Ruhullahi, Sahifeye Nur, Qom, Cibiyar Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khomaini, 1378Sh.
  • Khomaini, Sayyid Ruhullahi, Tahrirul Wasila, Najaf, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, 1390H.
  • Kulaini, Muhammad bn Ya'qub, Al-Kafi, Qom, Mawallafar Dar al-Hadis, 1430H.
  • Nishaburi, Abu Abdullahi Al-Hakim, Al-Mustadrak Alas Sahihaini, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, bugu na farko, 1411H.
  • Taftazani, Sa'adud-Din, Sharhul Maƙasid, Qom, al-Sharif al-Radi, bugu na farko, 1409H.
  • Ansari, Shaik Murtada, Kitabul Makasib, Qom, Majma' al-Fikr al-Islami, 1415H.
  • Iji, Sayyid Mir Sharif, Sharhul Mawaƙif,Qom, al-Sharif al-Radi, bugu na farko, 1325H.
  • Officialwebsiteofnigeriangoverment:https://fccpc.gov.ng/fccpc-takes-action-to-address-rising-prices-and-protect-consumers/?Ranar shigarwa April 17, 2024, ranar ziyara April 17, 2024M.
  • «فتوای آیت الله صافی گلپایگانی درباره فروش اجناس به قیمت روز و گران‌تر از قیمت اولیه»، (Fatwar Ayatullahi Safi Golfaigani game da sayar da kaya da farashin da ake da shi a wannan rana, ko fiye da farashin farko da aka saya), Shafin yanar gizon Shi'a News, ranar wallafa bayani: 29 ga Agusta, 2013; ranar duba shafin: 6 ga Nuwamba, 2020M.
  • «ریشه گران‌فروشی کجاست؟/ تاملی بر یکی از جدی‌ترین چالش‌های اقتصادی»، (Asalin yin tsadar kaya yana ina? / Tunani kan ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tattalin arziki), Shafin yanar gizon Bashgahe Khabarnegarane Jawan, ranar wallafa bayani: 29 ga Satumba, 2017M; ranar duba shafin: 16 ga Nuwamba, 2020M.
  • «آیا گران‌فروشی حرام است؟»، (Shin yin tsadar kaya ya haramta?), Shafin yanar gizon Hadana, ranar wallafa bayani: 8 ga Afrilu, 2017; ranar duba shafin: 6 ga Nuwamba, 2020M.
  • «معامله سلف»، (Kasuwancin Salaf), Tashar yaɗa bayanai ta Ayatullahi Makarim Shirazi, ranar duba shafin: 6 ga Nuwamba, 2020M.
  • «پیام به رئیس‌ جمهور در خصوص مبارزه‌ با گران‌فروشی»، (Saƙon shugaban ƙasa kan yaƙar halayyar yin tsadar kaya), Shafin khamenei.ir, ranar wallafa bayani: 7 ga Oktoba, 1994; ranar duba shafin: 6 ga Nuwamba, 2020M.
  • «استفتائات جدید»، (Sabbin Fatawowi), Shafin ofishin Ittala Rasani, ranar wallafa bayani: 30 ga Satumba, 2018; ranar duba shafin: 6 ga Nuwamba, 2020M.