Daƙiƙa:Wasiƙar Imam Ali Zuwa Ga Usman Bin Hunaif
Littafin Buɗaɗɗiyar Wasiƙar Imam Ali (A.S.) zuwa Usman Bin Hunaif, wanda Muhammadi Ishtihardi ya rubuta. | |
| Zamanin fitowa | Farkon Hukumar Imam Ali (A.S) a shekara ta 36H |
|---|---|
| Ta fito daga | Imam Ali (A.S) |
| Wanda ake magana da shi | Usman Bin Hunaif |
| Yare | Larabci |
| Maudu'i | Gudanar da mulki da siyasar tafiyar da al'umma. |
| Fagen da ta fito | Tsawatar da Usman Bin Hunaif saboda halartar wani liyafar masu hannu da shuni. |
| Madogaran Shi'a | Nahjul Balaga•Al-Amali |
| Siffofi | Tsantseni•Illolin rayuwar masu ƙasaita • Rayuwa cikin sauƙi da kauce wa almubazzaranci. |
| Nazarin Kwafi | Sharhin Littafin Amirul Muminina (A.S.) zuwa Usman bn Hunaif al-Ansari• Buɗaɗɗiyar Wasiƙar Imam Ali (A.S.) zuwa Usman bn Hanif, gwamnan Basra•Mulki nagari da takawa• Ali da jami'an gwamnatinsa. |
Wasiƙar Imam Ali (A.S) zuwa Usman Bin Hunaif wasiƙa ce da Imam Ali (A.S) ya rubuta wa Usman Bin Hunaif, wakilinsa a Basra. Wannan wasiƙa tana daga cikin wasiƙun da ke cikin Nahjul Balaga, kuma babban jigon ta shi ne tsawatar wa Usman Bin Hunaif saboda halartar wata liyafar masu hannu da shuni, alhali talakawa ba su samu halarta ba.[1]
Wasu masu bincike sun ɗauki wannan wasiƙa a matsayin mafi ƙarfi daga cikin misalan da ke goyon bayan ra'ayin cikakken shigar addini cikin dukkan al'amuran rayuwa.[2] Haka kuma, an ce ta hanyar wannan wasiƙa za a iya fahimtar halayen Imam Ali (A.S) a fagen siyasa da shugabanci.[3] Saboda haka, ana yawan ambatonta a cikin littattafan da ke bayani kan ƙa'idar siyasar Musulunci.[4]
Tun da wannan wasiƙa ta bayyana irin salon mulkin Imam Ali (A.S), masana sun bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin muhimman wasiƙunsa zuwa ga gwamnoni da wakilansa.[5]
A mafi yawan bugun Nahjul Balaga, wannan wasiƙa tana a lamba ta 45.[6]
| Sunan kwafi | Lambar wasiƙa[7] |
|---|---|
| Al-Mu'jam al-Mufahras, Subhi Salih, Fayz al-Islam, Mulla Salih, Ibn Abi al-Hadid, Abduh | 45 |
| Khu'i, Ibn Maytham, Fi Zilal | 44 |
| Mulla Fatahullah | 48 |
Daga cikin muhimman abubuwan da Imam Ali (A.S) ya ba da shawarar a kiyaye a cikin wannan wasiƙa akwai: tsabtar ɗabi'a, tsoron Allah, kulawa da mabuƙata, sarrafa son zuciya, ƙosawa da abin da Allah Ya azurta, nisantar almubazzaranci, tausaya wa jama'a, rayuwa mai sauƙi, koyi da Imam wajen salon rayuwa, da kuma yin taka-tsantsan wajen karɓar gayyata da halartar liyafa.[8]
A cikin wannan wasiƙa, ban da bayyana illolin rayuwar masu hannu da shuni da son alatu, an kuma gabatar da hanyoyin da za a bi wajen yaƙi da wannan ɗabi'a.[9] A cewar wasu masu bincike, wannan wasiƙa ta gabatar da kyakkyawan abin koyi na ɗabi'a da zamantakewa wajen tunkarar matsalar son alatu da rayuwar masu arziki.[10]
An ruwaito wasu sassa na wasiƙar Imam Ali (A.S) zuwa Usman Bin Hunaif a cikin littafin Al-Amali na Shaik Saduƙ,[11] haka kuma a wasu littattafai daban.[12] A cewar wasu masana, Imam Ali (A.S) ya rubuta wannan wasiƙa ga Usman bn Hunaif ne a farkon zamanin mulkinsa, a shekara ta 36 bayan Hijira.[13]
Baya ga sharhi da fassarar wasiƙa ta 45 ta Nahjul Balaga da ke cikin cikakkun fassarori da sharhinsa, an kuma rubuta littattafai na musamman cikin Farisanci da Larabci kan wannan wasiƙa. Daga cikinsu akwai:
- Name-ye Sargushade-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bin Hunaif Ostondar-e Basra, ta Muhammad Muhammadi Ishtihardi;[14]
- Zamamdari wa Parsayi, na Musɗafa Delshad Tehrani;[15]
- Sharh-e Ketab-e Amir al-Mu’minin (A.S.) ilā Usman bin Hanif al-Ansari, na Hashim Milani;[16]
- Ali wa Kargozaran-e Hokumat, na Ali Akbar Hamidzade.[17]
Bayanin kula
- ↑ Muntaziri, Dars-ha’i az Nahj al-Balagha, juzu’i na 13, shafi na 120.
- ↑ Mansuri Larijani, Irfan-e Siyasi, shafi na 57.
- ↑ Itratdust da Mahdiyya Ahmadi, Rahkarha-ye Moqabale ba Ashrafi-gari bar Mabna-ye Tahlil-e Mohtava-ye Name-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bn Hunaif, shafi na 89–90.
- ↑ Don duba misali: Mansuri Larijani, Irfan-e Siyasi, shafi na 56–57; Akhlaƙi, Rabita-ye Qudrat wa Adalat dar Fiƙh-e Siyasi, shafi na 275; Irwani, Mabani-ye Fiƙhi-ye Eqtisad-e Islami, shafi na 362; Murtazawi, Daneshnameh-ye Imam Khomaini, juzu’i na 2, shafi na 6743.
- ↑ Itratdust da Mahdiyya Ahmadi, Rahkarha-ye Moqabale ba Ashrafi-gari bar Mabna-ye Tahlil-e Mohtava-ye Name-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bn Hanif, shafi na 70–71.
- ↑ Duba: Dashti da Kazim Muhammadi, Al-Mu‘jam al-Mufahras li Alfaz Nahj al-Balagha, 1375 sh, shafi na 515.
- ↑ Dashti, da Kazim Muhammadi, Al-Mu'jam al-Mufahras li Alfaz Nahjul Balaga, shafi na 515.
- ↑ Duba: Nahj al-Balagha, wasiƙa ta 45, 1414 ƙ, shafi na 416–420.
- ↑ Itratdust da Mahdiyya Ahmadi, Rahkarha-ye Moqabale ba Ashrafi-gari bar Mabna-ye Tahlil-e Mohtava-ye Name-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bn Hanif, shafi na 90.
- ↑ Itratdust da Mahdiyya Ahmadi, Rahkarha-ye Moqabale ba Ashrafi-gari bar Mabna-ye Tahlil-e Mohtava-ye Name-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bn Hanif, shafi na 70.
- ↑ Shaik Saduƙ, Al-Amali, shafi na 620–623.
- ↑ Duba domin ganin wasu madogara na wannan wasiƙar: Al-Husayni al-Khatib, Masadir Nahj al-Balagha wa Asaniduhu, juzu’i na 3, shafi na 362.
- ↑ Nahj al-Balagha, wasiƙa ta 45, fassarar Muhammadi Dashti, shafi na 553.
- ↑ Muhammadi Ishtihardi, Name-ye Sargushade-ye Imam Ali (A.S.) be Usman bn Hunaif, shafin bayanan littafin (shafi na bayanin buga littafi).
- ↑ Dilshad Tehrani, Zamamdari wa Parsayi, shafin bayanan littafin (shafi na bayanin buga littafi).
- ↑ Milani, Sharh-e Ketab-e Amir al-Mu’minin (A.S.) ilā Usman bn Hunaif al-Ansari, 1433 ƙ, shafin bayanan littafi (shafi na bayanin buga littafi).
- ↑ Hamidzade, Ali wa Kargozaran-e Hokumat, 1389 sh, shafin bayanan littafi.
Nassoshi
- Akhlaƙi, Ghulam Sarwar, Rabita-ye Qudrat wa Adalat dar Fiqh-e Siyasi, Qum, Cibiyar -e Bayn al-Milali-ye Tarjama wa Nashr al-Mustafa (S.A.W). 1390Sh.
- Husayni Khaɗib, Sayyid Abdul Zahra, Masadir Nahjul Balaga wa Asaniduhu, Bayrut, Dar al-Zahra.1409H.
- Irwani, Jawad, Mabani-ye Fiqhi-ye Iqtisad-e Islami, Mashhad, Daneshgah-e Ulum-e Islami-ye Razawi. 1393Sh.
- Hamidzadeh, Ali Akbar, Ali wa Kargozaran-e Hukumat, Isfahan, Uqyanus-e Ma'arifat.1389Sh.
- Dashti, Muhammad, da Kazim Muhammadi, Al-Mu'jam al-Mufahras li Alfaz Nahjul Balaga, Qum, Cibiayar Farhangi Tahqiqati Amir al-Mu'minin (A.S).1375Sh.
- Delshad Tehrani, Mustafa, Zemamdari wa Parsayi, Tehran, Darya.1397Sh.
- Sayyid Radi, Muhammad Bin Husain, Nahjul Balaga, tarjame Husain Ansariyan, Tehran, Payam-e Azadi.1388Sh.
- Sayyid Radi, Muhammad Bin Husain, Nahjul Balaga, tarjame Muhammad Dashti, Qum, Mashhur.1379Sh.
- Sayyid Radi, Muhammad Bin Husain, Nahjul Balaga, Tas'hih Subhi Salih, Qum, Hijrat.1414H.
- Shaik Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi.1376Sh.
- Itratdust, Muhammad, da Mahdiyya Ahmadi,«راهکارهای مقابله با اشرافیگری بر مبنای تحلیل محتوای نامه امام علی(ع) به عثمان بن حنیف»، (Hanyoyin tunkarar rayuwar masu ƙasaita (ashrafanci), bisa nazarin abin da ke cikin wasiƙar Imam Ali (A.S.) zuwa Usman bn Hunaif.), A Mujallar Musulunci da Nazarin Zamantakewa, fitowa ta 34, damina. 2021 M.
- Muhammadi Ishtihardi, Muhammad, Name-ye Sargushada-ye Imam Ali (A.S) be Usman Bin Hunaif, Ustandar-e Basra, Qum, Akhlaƙi.1383Sh.
- Murtazawi, Sayyid Ziya, Daneshname-ye Imam Khomeini, Tehran, Cibiyar Tanzim wa Nashr-e Asar-e Imam Khomeini (rh).1400Sh.
- Muntazari, Husain Ali, Darshayi az Nahjul Balaga, Tehran, Mawallafar Intisharat-e Sarayi.1395Sh.
- Mansuri Larijani, Isma'il, Irfan-e Siyasi, Tehran, Mahdi al-Qur'an.1385Sh.
- Milani, Hashim, Sharh Kitab Amir al-Mu'minin (a) ila Usman Bin Hunayf al-Ansari, Najaf, Al-Ataba al-Alawiyya al-Muqaddasa.1433Sh.
أَمَّا بَعْدُ، یا ابْنَ حُنَیفٍ فَقَدْ بَلَغَنِی أَنَّ رَجُلًا مِنْ فِتْیةِ أَهْلِ الْبَصْرَةِ دَعَاكَ إِلَی مَأْدُبَةٍ فَأَسْرَعْتَ إِلَیهَا
تُسْتَطَابُ لَكَ الْأَلْوَانُ وَ تُنْقَلُ إِلَیكَ الْجِفَانُ وَ مَا ظَنَنْتُ أَنَّكَ تُجِیبُ إِلَی طَعَامِ قَوْمٍ عَائِلُهُمْ مَجْفُوٌّ وَ غَنِیهُمْ مَدْعُوٌّ
فَانْظُرْ إِلَی مَا تَقْضَمُهُ مِنْ هَذَا الْمَقْضَمِ فَمَا اشْتَبَهَ عَلَیكَ عِلْمُهُ فَالْفِظْهُ وَ مَا أَیقَنْتَ بِطِیبِ وُجُوهِهِ فَنَلْ مِنْهُ
أَلَا وَ إِنَّ لِكُلِّ مَأْمُومٍ إِمَاماً یقْتَدِی بِهِ وَ یسْتَضِیءُ بِنُورِ عِلْمِهِ أَلَا وَ إِنَّ إِمَامَكُمْ قَدِ اكْتَفَی مِنْ دُنْیاهُ بِطِمْرَیهِ وَ مِنْ طُعْمِهِ بِقُرْصَیهِ
أَلَا وَ إِنَّكُمْ لاتَقْدِرُونَ عَلَی ذَلِكَ وَ لَكِنْ أَعِینُونِی بِوَرَعٍ وَ اجْتِهَادٍ وَ عِفَّةٍ وَ سَدَادٍ
فَوَاللهِ مَا كَنَزْتُ مِنْ دُنْیاكُمْ تِبْراً وَ لاادَّخَرْتُ مِنْ غَنَائِمِهَا وَفْراً وَ لاأَعْدَدْتُ لِبَالِی ثَوْبِی طِمْراً وَ لاحُزْتُ مِنْ أَرْضِهَا شِبْراً وَ لاأَخَذْتُ مِنْهُ إِلَّا كَقُوتِ أَتَانٍ دَبِرَةٍ وَ لَهِی فِی عَینِی أَوْهَی وَ أَوْهَنُ مِنْ عَفْصَةٍ مَقِرَةٍ
بَلَی كَانَتْ فِی أَیدِینَا فَدَكٌ مِنْ كُلِّ مَا أَظَلَّتْهُ السَّمَاءُ فَشَحَّتْ عَلَیهَا نُفُوسُ قَوْمٍ وَ سَخَتْ عَنْهَا نُفُوسُ قَوْمٍ آخَرِینَ وَ نِعْمَ الْحَكَمُ اللهُ
وَ مَا أَصْنَعُ بِفَدَكٍ وَ غَیرِ فَدَكٍ وَ النَّفْسُ مَظَانُّهَا فِی غَدٍ جَدَثٌ تَنْقَطِعُ فِی ظُلْمَتِهِ آثَارُهَا وَ تَغِیبُ أَخْبَارُهَا وَ حُفْرَةٌ لَوْ زِیدَ فِی فُسْحَتِهَا وَ أَوْسَعَتْ یدَا حَافِرِهَا لَأَضْغَطَهَا الْحَجَرُ وَ الْمَدَرُ وَ سَدَّ فُرَجَهَا التُّرَابُ الْمُتَرَاكِمُ
وَ إِنَّمَا هِی نَفْسِی أَرُوضُهَا بِالتَّقْوَی لِتَأْتِی آمِنَةً یوْمَ الْخَوْفِ الْأَكْبَرِ وَ تَثْبُتَ عَلَی جَوَانِبِ الْمَزْلَقِ وَ لَوْ شِئْتُ لَاهْتَدَیتُ الطَّرِیقَ إِلَی مُصَفَّی هَذَا الْعَسَلِ وَ لُبَابِ هَذَا الْقَمْحِ وَ نَسَائِجِ هَذَا الْقَزِّ وَ لَكِنْ هَیهَاتَ أَنْ یغْلِبَنِی هَوَای وَ یقُودَنِی جَشَعِی إِلَی تَخَیرِ الْأَطْعِمَةِ وَ لَعَلَّ بِالْحِجَازِ أَوْ الْیمَامَةِ مَنْ لاطَمَعَ لَهُ فِی الْقُرْصِ وَ لاعَهْدَ لَهُ بِالشِّبَعِ
أَوْ أَبِیتَ مِبْطَاناً وَ حَوْلِی بُطُونٌ غَرْثَی وَ أَكْبَادٌ حَرَّی أَوْ أَكُونَ كَمَا قَالَ الْقَائِلُ:
وَ حَسْبُكَ دَاءً أَنْ تَبِیتَ بِبِطْنَةٍ * وَ حَوْلَكَ أَكْبَادٌ تَحِنُّ إِلَی الْقِدِّ
أَ أَقْنَعُ مِنْ نَفْسِی بِأَنْ یقَالَ هَذَا أَمِیرُ الْمُؤْمِنِینَ وَ لاأُشَارِكُهُمْ فِی مَكَارِهِ الدَّهْرِ أَوْ أَكُونَ أُسْوَةً لَهُمْ فِی جُشُوبَةِ الْعَیشِ
فَمَا خُلِقْتُ لِیشْغَلَنِی أَكْلُ الطَّیبَاتِ كَالْبَهِیمَةِ الْمَرْبُوطَةِ، هَمُّهَا عَلَفُهَا أَوِ الْمُرْسَلَةِ شُغُلُهَا تَقَمُّمُهَا تَكْتَرِشُ مِنْ أَعْلَافِهَا وَ تَلْهُو عَمَّا یرَادُ بِهَا
أَوْ أُتْرَكَ سُدًی أَوْ أُهْمَلَ عَابِثاً أَوْ أَجُرَّ حَبْلَ الضَّلَالَةِ أَوْ أَعْتَسِفَ طَرِیقَ الْمَتَاهَةِ وَ كَأَنِّی بِقَائِلِكُمْ یقُولُ إِذَا كَانَ هَذَا قُوتُ ابْنِ أَبِی طَالِبٍ فَقَدْ قَعَدَ بِهِ الضَّعْفُ عَنْ قِتَالِ الْأَقْرَانِ وَ مُنَازَلَةِ الشُّجْعَانِ أَلَا وَ إِنَّ الشَّجَرَةَ الْبَرِّیةَ أَصْلَبُ عُوداً وَ الرَّوَاتِعَ الْخَضِرَةَ أَرَقُّ جُلُوداً وَ النَّابِتَاتِ الْعِذْیةَ أَقْوَی وَقُوداً وَ أَبْطَأُ خُمُوداً.
وَ أَنَا مِنْ رَسُولِ اللهِ كَالضَّوْءِ مِنَ الضَّوْءِ وَ الذِّرَاعِ مِنَ الْعَضُدِ وَ اللهِ لَوْ تَظَاهَرَتِ الْعَرَبُ عَلَی قِتَالِی لَمَا وَلَّیتُ عَنْهَا وَ لَوْ أَمْكَنَتِ الْفُرَصُ مِنْ رِقَابِهَا لَسَارَعْتُ إِلَیهَا وَ سَأَجْهَدُ فِی أَنْ أُطَهِّرَ الْأَرْضَ مِنْ هَذَا الشَّخْصِ الْمَعْكُوسِ وَ الْجِسْمِ الْمَرْكُوسِ حَتَّی تَخْرُجَ الْمَدَرَةُ مِنْ بَینِ حَبِّ الْحَصِیدِ.
لم يذكر السيد الرضي جزءاً من منتصف هذه الرسالة، وقد ورد في الجزء الأخير منها ما يلي:
إِلَیكِ عَنِّی یا دُنْیا، فَحَبْلُكِ عَلَی غَارِبِكِ قَدِ انْسَلَلْتُ مِنْ مَخَالِبِكِ وَ أَفْلَتُّ مِنْ حَبَائِلِكِ وَ اجْتَنَبْتُ الذَّهَابَ فِی مَدَاحِضِكِ
أَینَ الْقُرُونُ الَّذِینَ غَرَرْتِهِمْ بِمَدَاعِبِكِ؟ أَینَ الْأُمَمُ الَّذِینَ فَتَنْتِهِمْ بِزَخَارِفِكِ؟ فَهَا! هُمْ رَهَائِنُ الْقُبُورِ وَ مَضَامِینُ اللّحُودِ
وَ اللهِ لَوْ كُنْتِ شَخْصاً مَرْئِیاً وَ قَالَباً حِسِّیاً لَأَقَمْتُ عَلَیكِ حُدُودَ اللهِ فِی عِبَادٍ غَرَرْتِهِمْ بِالْأَمَانِی وَ أُمَمٍ أَلْقَیتِهِمْ فِی الْمَهَاوِی وَ مُلُوكٍ أَسْلَمْتِهِمْ إِلَی التَّلَفِ وَ أَوْرَدْتِهِمْ مَوَارِدَ الْبَلَاءِ إِذْ لاوِرْدَ وَ لاصَدَرَ
هَیهَاتَ مَنْ وَطِئَ دَحْضَكِ زَلِقَ وَ مَنْ رَكِبَ لُجَجَكِ غَرِقَ وَ مَنِ ازْوَرَّ عَنْ حَبَائِلِكِ وُفِّقَ،
وَ السَّالِمُ مِنْكِ لایُبَالِی إِنْ ضَاقَ بِهِ مُنَاخُهُ وَ الدُّنْیا عِنْدَهُ كَیوْمٍ حَانَ انْسِلَاخُهُ.
اُعْزُبِی عَنِّی، فَوَاللهِ لاأَذِلُّ لَكِ فَتَسْتَذِلِّینِی وَ لاأَسْلَسُ لَكِ فَتَقُودِینِی وَ اَیمُ اللهِ یمِیناً أَسْتَثْنِی فِیهَا بِمَشِیئَةِ اللهِ لَأَرُوضَنَّ نَفْسِی رِیاضَةً تَهِشُّ مَعَهَا إِلَی الْقُرْصِ إِذَا قَدَرْتُ عَلَیهِ مَطْعُوماً وَ تَقْنَعُ بِالْمِلْحِ مَأْدُوماً
أَ تَمْتَلِئُ السَّائِمَةُ مِنْ رِعْیهَا فَتَبْرُكَ وَ تَشْبَعُ الرَّبِیضَةُ مِنْ عُشْبِهَا فَتَرْبِضَ وَ یأْكُلُ عَلِی مِنْ زَادِهِ فَیهْجَعَ؟!
قَرَّتْ إِذاً عَینُهُ إِذَا اقْتَدَی بَعْدَ السِّنِینَ الْمُتَطَاوِلَةِ بِالْبَهِیمَةِ الْهَامِلَةِ وَ السَّائِمَةِ الْمَرْعِیةِ.
طُوبَی لِنَفْسٍ أَدَّتْ إِلَی رَبِّهَا فَرْضَهَا وَ عَرَكَتْ بِجَنْبِهَا بُؤْسَهَا وَ هَجَرَتْ فِی اللّیلِ غُمْضَهَا حَتَّی إِذَا غَلَبَ الْكَرَی عَلَیهَا افْتَرَشَتْ أَرْضَهَا وَ تَوَسَّدَتْ كَفَّهَا فِی مَعْشَرٍ أَسْهَرَ عُیونَهُمْ خَوْفُ مَعَادِهِمْ وَ تَجَافَتْ عَنْ مَضَاجِعِهِمْ جُنُوبُهُمْ
وَ هَمْهَمَتْ بِذِكْرِ رَبِّهِمْ شِفَاهُهُمْ وَ تَقَشَّعَتْ بِطُولِ اسْتِغْفَارِهِمْ ذُنُوبُهُمْ أُولئِكَ حِزْبُ اللهِ أَلا إِنَّ حِزْبَ اللهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
فَاتَّقِ اللهَ یا ابْنَ حُنَیفٍ وَ لْتَكْفُفْ أَقْرَاصُكَ لِیكُونَ مِنَ النَّارِ خَلَاصُكَ.
وَ حَسْبُكَ دَاءً أَنْ تَبِیتَ بِبِطْنَةٍ * وَ حَوْلَكَ أَكْبَادٌ تَحِنُّ إِلَی الْقِدِّ
Amma bayan haka, ya ɗan Hunaif! Lalle ne ya isar mini cewa wani mutum daga cikin samarin mutanen Basra ya gayyace ka zuwa liyafa, kuma ka yi gaggawar zuwa gare ta.
Sun karɓe ka da abinci iri-iri masu launuka, da kwanoni cike da abinci da ake kawo maka. Ban yi tsammanin za ka amsa gayyatar zuwa teburin mutanen da suke korar matalautansu da zalunci, kuma suna gayyatar mawadansu (zuwa liyafa) ba
To, ka dubi abin da kake ci daga wannan abincin. Abin da iliminsa ya ruɗe ka, to ka watsar da shi (ka bar shi), kuma abin da ka tabbatar da tsaftar fuskokinsa (ko ingancinsa), to ka ci daga gare shi.
Ka sani cewa lalle ga kowane mabiyi akwai jagora (limami) wanda yake koyi da shi kuma yake amfana da hasken iliminsa. Ka sani cewa lalle jagoranku (limaminku) ya wadatu daga dukan duniyarsa da tsofaffin tufafinsa biyu, kuma daga abincinsa da gurasa biyu (ko burodi biyu)..
Ku sani cewa lalle ku ba za ku iya yin haka ba (wato ku kai matakin wadatar da na kai), amma ku taimake ni da takawa (tsoron Allah), da himma (kokari a cikin ibada), da tsabtar rai (kamewa daga haram), da daidaito (tarbiyya a cikin al'amura).
Wallahi ban taɓa tara zinariya daga duniyarku ba, kuma ban taɓa ajiyar dukiya daga ganimominta masu yawa ba, kuma ban taɓa shirya wata tsohuwar tufa don maye gurbin wannan tsohuwar tufata ba, kuma ban taɓa mallakar ko da shiɗa ɗaya daga ƙasar duniya ba, kuma ban taɓa ɗauka daga abinci da qutun duniya ba sai dai kamar qutun wani raƙumi da ya gaji, wanda ƙugunsa ya ji rauni (ya fāɗi a gefe, ba zai iya ci ba, kuma ba zai iya yin aiki ba). Duniyarku a wurina ta fi rauni da ƙasƙanci fiye da 'afsa (kwayar itacen oak) mai ɗaci..
Na'am, daga abin da sama ta yi masa inuwa, Fadak kaɗai ne yake cikin hannayenmu, wanda wasu mutane suka yi kwaɗayi da shi (suka hana mu shi), yayin da mu kuma muka kyautata shi (muka bar shi) da karimci, kuma Allah ne Mafi kyawun Mai hukunci.
Mene ne zan yi da Fadak da wanin Fadak? Alhali a gobe (ranar kiyama) wurin mutum kabari ne, wanda a cikin duhunsa ayyukan mutum suke ɓacewa, kuma labaransa suke ɓuya. Rami ne wanda ko da an ƙara masa faɗi, kuma hannayen masu haƙa suka yi ƙoƙarin faɗaɗa shi, duk da haka duwatsu da ƙasar da aka tattara za su matsa masa, kuma ƙurar da ta taru za ta rufe hujjõjinsa (ramummukansa).
Wannan ita ce raina, ina horar da shi da takawa (tsoron Allah) domin ya zo lafiya a ranar tsoro mafi girma (ranar kiyama), kuma ya tsaya tsayin daka a gefuna na wurin zamewa (wato tsayawa kan hanya madaidaici). Kuma da na so, da na nufi hanya zuwa ga tacewar zuma, da tsakiyar wannan alkama, da saƙa na wannan alharini (tufafin alharini). Amma yaya zai yiwu sha'awata ta rinjaye ni, kuma zari na ya kai ni ga zaɓen abinci mai daɗi, yayin da wataƙila a Hijaz ko Yamanah akwai wanda ba shi da bege ga ko da gurasa ɗaya, kuma bai taɓa sanin koshi ba?
Ko in kwana da cikar abinci, yayin da a kusa da ni akwai cikkuna masu yunwa da hantõri masu zafi (saboda yunwa)? Ko in zama kamar yadda mai faɗi ya faɗa: 'Wannan ciwo da kunya ya ishe ka ka kwana da cikar abinci, yayin da a kusa da kai akwai cikkuna masu yi wa fatar busasshiyar nama buri (domin ci).
Ashe zan wadatu da a ce ni ne "Amirul Mu'minina" (Shugaban Muminai), amma ba tare da in yi tarayya da su a cikin wahalolin zamani ba, ko kuma in zama abin koyi a gare su a cikin ɓacin rai na rayuwa ba?
Ba a halicce ni ba don cinye abinci mai daɗi ya shagaltar da ni, kamar dabba da aka daure a wurin kiwo wadda duk burinta ci ne, ko kuma dabbar da aka saki wadda aikinta shi ne tattara ƙura da tarkace; tana cika cikinta da ciyawarta, kuma tana shagala da abin da mai gidanta yake nema gare ta (wato aikin da aka yi mata) daga cika ta.
Ba zai yiwu ba a bar ni ban da wani aiki (ba tare da manufa ba), ko a sake ni in yi shagala, ko in jawo igiyar ɓata, ko in bi hanyar ɓacewa da rudani. Kamar dai ina ganin mai magana daga cikinku yana cewa: 'Idan wannan shine abincin ɗan Abi Talib, to lalle rauni ya kama shi ya hana shi yaƙi da masu gaba da fafatawa da jarumawa!' Ku sani kuwa cewa itacen daji (na jeji) sun fi tauri, kuma itatuwa masu kore sun fi laushin fata, kuma tsire-tsire na jeji sun fi ƙarfin wuta kuma sun fi jinkirin kashewa (watau wutarsu tana da ƙarfi kuma tana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin ta mutu).
Ni da Manzon Allah muna kamar bishiyoyi biyu da suka fito daga tushe guda, kuma muna kamar hannu (daga gwiwa zuwa ƙafa) da babban hannu (daga kafaɗa zuwa gwiwa). Wallahi, ko da Larabawa suka haɗa kai don yaƙi da ni, da ban juya musu baya ba. Kuma ko da dama ta samu, da na yi gaggawar kai gare ta (zuwa Sham). Kuma zan yi ƙoƙari sosai don in tsarkake ƙasa daga wannan halitta mai jujjuyawar al'amura da jiki mai kifarwa (Ma'awiya), har sai ƙanƙarar duwatsu ta fito daga tsakanin ƙwayar hatsin da aka girbe (wato har sai an kawar da duk wata ƙazanta da ɓarna).
Ya duniya! Ki nisa da ni, domin na jefa igiyarki a kan wuyanki (na rabu da ke). Na kubuta daga farautarki, na tsere daga tarkunanki, kuma na nisanci tafiya a cikin wuraren zamewarki."
Ina su ƙarnuka (al'ummomin da suka shige) waɗanda ka yaudare su da wasanniki naki? Ina su al'ummomin da ka ruɗe su da kayan adonki da zinatarki? Ga su! Sun zama jingina (kamar jinginar da ake ajiyewa) a cikin kaburbura, kuma sun shiga cikin ramummuka.
Wallahi, ya duniya! Da kin kasance halitta mai gani (wanda ake iya gani) da jiki wanda ya cancanci a taɓa shi, da na aiwatar da hukunce-hukuncen Allah a kanki, saboda bayin da kika yaudare su da mafarkai (bege), da al'ummomin da kika jefa su a cikin ɓangarorin halaka, da sarakunan da kika mika su ga tafarkin halaka, kuma kika shigar da su maɓuɓɓugar bala'i, zuwa wurin da babu tsaro a shiga da fita.
Ya yi nisa (ba zai yiwu ba)! Duk wanda ya taka wuraren zamewarki, ya zame; kuma duk wanda ya hau ruwan da ya taru naki, ya nutse; kuma duk wanda ya kauce wa tarkunanki, an ba shi nasara.
Kuma wanda ya tsira daga fitinunki, ba ya damu ko rayuwa ta yi masa ƙunci, kuma duniya a wurinsa kamar rana ce da lokacin ƙarewarta ya yi kusa.
Ki rabu da ni! Wallahi ba zan zama mai tawali'u gare ki ba don ki wulakanta ni, kuma ba zan ba ki ragamar (igiya) ba don ki kai ni duk inda kika so. Ina rantse da Allah - rantsuwar da nake keɓe a cikinta da mashiyyar Allah (wato in ce 'in Allah ya so') - lalle zan horar da raina horon da zai sa ta yi farin ciki da gurasa ɗaya idan ta sami damar ci, kuma ta wadatu da gishiri a madadin miya.
Kuma zan sanya kwas ɗin idona a cikin kuka na dare da na yini, har ya zama kamar maɓuɓɓugar ruwa wadda ruwanta ya ƙare, ba ya rage a cikinta ko da hawaye ɗaya ba.
Shin kamar yadda dabbar kiwo take cika cikinta da kiwo har ta kwanta (ta huta), da kuma garken tumaki da suke koshi da ciyawa har suke komawa wurin kwanciyarsu, Ali ma zai ci daga abincinsa ya yi barci?!" (wato ba zai yiwu ba in zama kamar dabbobi masu kawai kwance da ci, domin ni mai ibada da tsayuwar dare ne)
Idonsa ya yi sanyi (ya ji daɗi) idan bayan shekaru masu tsawo ya koyi da dabbobi marar tarbiya da tumaki masu kiwo!" (wannan magana ce ta ban haushi, ma'ana: shin yana yiwuwa Ali ya zama kamar dabbobi bayan duk wannan matsayi da ilimi?)
Madalla ga wanda ya cika farillan Ubangijinsa, kuma ya haƙura da wahaloli, kuma ya nisa daga barci mai daɗi a cikin dare, har idan rashin barci ya rinjaye shi, sai ya shimfiɗa ƙasa a matsayin katifarsa, kuma ya sa hannunsa a matsayin matashin kansa, a cikin jama'ar da tsoron tashin kiyama ya sa idanunsu suka yi farke, kuma sassan jikinsu suka nisa daga gadajensu (saboda tsayuwar dare da ibada).
Kuma leɓunansu suna ta raɗa a hankali da ambaton Ubangijinsu, kuma zunubbansu sun kau da su saboda yawan neman gafarar da suke yi. 'Waɗannan su ne ƙungiyar Allah, kuma ku sani cewa lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu cin nasara (masu rabo mai kyau a duniya da lahira).
Ya ɗan Hunaif, ka ji tsoron Allah. Gurasa kaɗan da kake da su su ishe ka, domin hakan zai zama sanadin tsirarka daga wutar Jahannama.