Daƙiƙa:Wasiƙar Imam Ali Zuwa Ga Ash'as Bin Ƙaisi
| Wasiƙar Imam Ali (A.S) Zuwa Ga Ash'as Bin Ƙaisi | |
| Zamanin fitowa | Shekara ta 36H |
|---|---|
| Ta fito daga | Imam Ali (A.S) |
| Wanda ake magana da shi | Ash'as Bin Ƙaisi |
| Yare | Larabci |
| Maudu'i | Mai girma yana tunasar da shi mutuwar Usman da kuma karya mubaya'ar Ɗalha da Zubairu, sannan yana neman ya yi masa mubaya'a. |
| Ɗan aike | Ziyad Bin Marhab Hamadani |
| Inganacin isnadi | Ingantacce |
| Madogaran Shi'a | Nahjul Balaga• Littafin Waƙ'atu Siffin |
| Madogaran AhluS-sunna | Al-Futuh |
| Siffofi | Nuni ne ga cewa muƙaman gwamnati a tsarin mulkin Musulunci amana ce daga Allah • Kare dukiyar baitulmalin Musulmi |
| Mai alaƙa | Wasiƙar Imam Ali Zuwa Ga Usman Bin Hunaif• Wasiƙar Imam Ali Zuwa Ga Shuraih Ƙazi•Wasiƙar Imam Ali Zuwa Ga Sahlu Bin Hunaif |
Wasiƙar Imam Ali (A.S) zuwa ga Ash'as Bin Ƙaisi tana daga cikin wasiƙun Nahjul Balaga, inda Imam Ali (A.S), yayin tunasar da kisan Usman da kuma karya mubaya'ar Ɗalha da Zubairu, ya nemi Ash'as Bin Ƙaisi, wanda yake gwamnan Azarbaijan, ya yi masa mubaya'a.[1] A ƙarshen wasiƙar, Imam Ali (A.S) ya kuma yi wa Ash'as gargaɗi game da kare baitul-mali.[2] A cewar Ayatullahi Makarim Shirazi, mai sharhin Nahjul Balaga, babban abin da wasiƙar take jaddadawa shi ne cewa mukaman gwamnati a gwamnatin Musulunci amana ce daga Allah, kuma bai kamata a mayar da su wata hanya ta neman amfanin kai ko zaluntar jama'a ba.[3] Imam Ali (A.S) ya rubuta wannan wasiƙa a shekara ta 36H, bayan Yaƙin Jamal,[4] sannan ya aika da ita zuwa ga Ash'as ta hannun Ziyad Bin Marhab Hamdani.[5]
Masana tarihin sun rawaito wannan wasiƙa da ɗan bambancin lafazi. Ibn A'asam Kufi, marubucin tarihi (wanda da ya rasu bayan shekara ta 320H), ya kawo ta a cikin littafinsa Al-Futuh. Haka nan Nasru Bin Muzahim, wanda ya rayu a ƙarni na biyu bayan hijira, ya kawo wannan wasiƙa a cikin littafinsa Waƙ'atu Siffin, tare da ɗan bambancin rubutu.[6] Sayyid Radi kuwa, a cikin Nahjul Balaga, ya kawo ƙarshen wannan wasiƙa ne kawai.[7] Wannan wasiƙa ita ce wasiƙa ta biyar a Nahjul Balaga bisa gyaran Subhi Salih, da kuma bisa bugu na Faizul Islam, Ibn Maisam da sauran masu gyara.[8]
Ash'as Bin Ƙaisi Kindi (ya rasu a shekara ta 40H) yana daga cikin mutanen da suka halarci yaƙin da aka yi wajen buɗe Azarbaijan. A shekara ta 25H, Usman Bin Affan ya naɗa shi a matsayin gwamnan Azarbaijan.[9] A cewar wasu masana tarihi, da izinin Usman, Ash'as yana karɓar dirhami 1000 a shekara daga cikin harajin Azarbaijan domin kansa.[10] A farkon mulkin Imam Ali (A.S), bai cire Ash'as daga mukaminsa ba.[11]
Bisa wasu ruwayoyin tarihi, bayan Ash'as ya karanta wasiƙar Imam Ali (A.S) ga mutanensa, sai suka ƙarfafa shi ya yi mubaya'a ga Imam Ali (A.S). Amma ya ce yana tsoron cewa idan ya je wajen Ali (A.S), Imam zai karɓe masa dukiyoyin Azarbaijan, yayin da idan ya koma wajen Mu'awiya, ba zai karɓe masa komai ba.[12]
A cewar wannan ruwaya, bayan mutanensa sun zarge shi saboda wannan magana, Ash'as ya yi nadama.[13] Daga nan, kamar yadda masu binciken tarihi suka bayyana, Ash'as ya nufi Kufa, sai Imam Ali (A.S) ya karɓe dukiyar baitul-malin da take hannunsa, sannan ya cire shi daga mukaminsa.[14]
Rubutun Wasiƙa
أَمَّا بَعْدُ فَلَوْ لَا هَنَاتٌ كُنَّ فِيكَ كُنْتَ الْمُقَدَّمَ فِي هَذَا الْأَمْرِ قَبْلَ النَّاسِ وَ لَعَلَّ أَمْرَكَ يَحْمِلُ بَعْضُهُ بَعْضاً إِنِ اتَّقَيْتَ اللَّهَ ثُمَّ إِنَّهُ كَانَ مِنْ بَيْعَةِ النَّاسِ إِيَّايَ مَا قَدْ بَلَغَكَ
وَ كَانَ طَلْحَةُ وَ الزُّبَيْرُ مِمَّنْ بَايَعَانِي ثُمَّ نَقَضَا بَيْعَتِي عَلَى غَيْرِ حَدَثٍ وَ أَخْرَجَا أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ وَ سَارَا إِلَى الْبَصْرَةِ فَسِرْتُ إِلَيْهِمَا فَالْتَقَيْنَا فَدَعَوْتُهُمْ إِلَى أَنْ يَرْجِعُوا فِيمَا خَرَجُوا مِنْهُ فَأَبَوْا فَأَبْلَغْتُ فِي الدُّعَاءِ وَ أَحْسَنْتُ فِي الْبَقِيَّةِ
وَ إِنَّ عَمَلَكَ لَيْسَ لَكَ بِطُعْمَةٍ وَ لَكِنَّهُ أَمَانَةٌ وَ فِي يَدَيْكَ مَالٌ مِنْ مَالِ اللَّهِ وَ أَنْتَ مِنْ خُزَّانِ اللَّهِ عَلَيْهِ حَتَّى تُسَلِّمَهُ إِلَيَّ وَ لَعَلِّي أَلَّا أَكُونَ شَرَّ وُلَاتِكَ لَكَ إِنِ اسْتَقَمْتَ وَ لا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ
Amma bayan haka, da ba don wasu kura-kuran da suka faru daga gare ka ba, da ka riga sauran mutane ka zama jagora a wannan al'amari. Amma wataƙila za ka iya yin wani abu da zai gyara abin da ya faru daga gare ka, idan ka ji tsoron Allah. Abin da ya faru game da mubaya'ar mutane gare ni ya riga ya iso gare ka.
Ɗalha da Zubairu ma suna daga cikin waɗanda suka yi mini mubaya'a, amma ba tare da wani abin da ya faru ba, suka karya mubaya'arsu. Sun tafi Basra tare da Uwar Muminai, sai na nufi wajensu. Na gamu da su, na kira su da su koma ga abin da suka bari, amma suka ƙi. Na yi iya ƙoƙarina wajen yi musu kira, kuma a sauran mu'amalar da muka yi, na kyautata musu.
Ka sani cewa aikin da aka ba ka amanar riƙe shi ba ganima ba ne a gare ka, a'a, amana ce. Kuma a hannunka akwai dukiya daga cikin dukiyar Allah, kuma kai ma'aji ne daga cikin ma'ajin Allah har sai ka miƙa ta gare ni. Kuma wataƙila ba zan zama mafi munin gwamnoninka ba, idan ka bi hanya madaidaiciya. Babu wani ƙarfi face daga Allah..
Bayanin kula
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503.
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503; Ibn Muzahim, Waƙ'atu Siffin, shafi na 20.
- ↑ Makarim Shirazi, Payame Imam Amirul-Mu'uminin, juzu'i na 9, shafi na 67.
- ↑ Aghazade, «Hukumate Ash'as Bin Ƙaisi Dar Azarbaijan,» shafi na 34.
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503.
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503; Ibn Muzahim al-Minƙari, Waƙ'atu Siffin, shafina 20.
- ↑ Nahjul Balaga, Tas'hihu Subhi Salih, wasiƙa ta 5, shafi na 366.
- ↑ Nahjul Balaga, Tas'hihu Subhi Salih, wasiƙa ta 5, shafi na 366; Nahjul Balaga, Tas'hihu wa Tarjame Faizul Islam, wasiƙa ta 5, juzu'i na 5, shafi na 389; Ibn Abil Hadid, Sharhu Nahjil Balaga, juzu'i na 4, shafina 33; Ibn Maisam, Sharhu Nahjil Balaga, juzu'i na 4, shafi' na 350; Abduhu, Sharhu Nahjil Balaga, juzu'i na 3, shafina 7; Mughniyya, Fi Zilal Nahjil Balaga, juzu'i na 3, shafi na 388.
- ↑ Balazuri, Futuhul Buldan, juzu'i na 2, shafi na 420.
- ↑ Aghazade«Hukumate Ash'as Bin Ƙaisi Dar Azarbaijan,» shafina 30.
- ↑ Yaƙubi, Tarikhul Yaƙubi, juzu'i na 2, shafina 200.
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503; Ibn Muzahim, Waƙ'atu Siffin, shafi na 21.
- ↑ Ibn A'asam, Al-Futuh, juzu'i na 2, shafi na 503; Ibn Muzahim, Waƙ'atu Siffin, shafi na 21.
- ↑ Aghazade, «Hukumate Ash'as Bin Ƙaisi Dar Azarbaijan,» shafi na 38.
Nassoshi
- Abduhu, Muhammad, Sharhu Nahjul Balaga, Alkahira, Matba'atu al-Istiƙama. babu kwanan wata.
- Aghazade, Jafar «Hukumate Ash'as Bin Ƙaisi Dar Azarbaijan,» (Gwamnatin Ash'as Bin Ƙaisi A Azarbaijan) Mujallar Pajuhishnamaye Tarih-ha-ye Mahalli-ye Iran, mujalladi na 7, lamba na 1. 1397Sh?2018M.
- Balazuri, Yahaya, Futuhul Buldan, Alkahira, Matba'atu Lajnatil-Bayan al-Arabi. 1957M.
- Faizu Islam Isfahani, Ali-Naƙi, Tarjame Wa Sharhu Nahjul Balaga, ba a ambaci wurin bugawa ba, ba a ambaci gidan bugu ba.
- Ibn A'asam Kufi, Muhammad Bin Ali, Al-Futuh, Beirut, Dar al-Adwa.1411H.
- Ibn Abil Hadid, Abdul-Hamid, Sharhu Nahjil Balaga, Qom, Maktabatu Ayatullahi al-Uzma al-Mar'ashi al-Najafi. babu kwanan wata.
- Ibn Maisam, Maisam Bin Ali, Sharhu Nahjil Balaga, Tehran, Daftaru Nashril-Kitab.1404H.
- Ibn Muzahim Minƙari, Nasr, Waƙ'atu Siffin, Qom, Maktabatu Ayatullahi al-Mar'ashi al-Najafi.1404H.
- Makarim Shirazi, Nasir, Payame Imam Amirul-Mu'uminin, Tehran, Darul-Kutub al-Islamiyya. 1386Sh.
- Mughniyya, Muhammad Jawad, Fi Zilal Nahjil Balaga, Beirut, Darul-Ilmi lil-Malayin.1979M.
- Sayyid Radi, Muhammad Bin Husain, Nahjul Balaga, Tash'hihu Subhi Salih, Qum, Hijrat. 1414H.
- Yaƙubi, Ahmad Bin Abi Yaƙub, Tarikhul Yaƙubi, Beirut, Dar Sadir. babu kwanan wata.