Daƙiƙa:Nahrawan
| Ƙasa | Iraƙ |
|---|---|
| Jiha | Bagdad |
| Harshe | Larabci |
| Tsohon suna | Birnin Jisru Nahrawan |
| Shekara da aka kafa ta | Zamanin Daular Sasaniyawa |
| Muhimman abubuwan da suka faru | Yaƙin Nahrawan |
Nahrawan wani yanki ne a yake a gabashin Dajla a ƙasar Iraƙ wanda ya kasance tsakanin Bagdad da Wasiɗ.[1] An raba wannan yanki zuwa sasannin guda uku, na sama, na tsakiya da na ƙasa wanda ake kira Ƙatul, Tamarra da Jisru Nahrawan.[2]Yaƙin Nahrawan, shi ne ƴakin da Imam Ali (A.S) ya gwabza tare da Khawarijawa, da ya faru a shekara ta 83H, a kusa da Jisru Nahrawan[3]
Nahrawan yna da nisan farsaki huɗu (Kilomita 22) daga Bagdad.[4] Kuma yana daga masaukin matafiya daga hanyar Khurasan[5] Wasu malamai da masana masu tunani na Musulunci[6] kamar Abul Faraj Nahrawani an danganta su da wannan yanki.[7]
Nahrawan a asali suna ne na wata ƙorama da ya ware kansa daga kogin Dajla kuma yake shayar da sassan yanki ruwa.[8] samar da wannan ƙorama ana jingina shi da Iraniyawa a zamanin Sasaniyawa musamman zamanin Shapur na biyu.[9] an kuma gina gadoji da madatsun ruwa a kansa,[10] Birnin Jisru Nahrawan shima ya kasance kusa da ɗaya daga cikin waɗannan gadoji.[11]
An samu rahotanni daban-daban game tushen wannan kogi, daga ciki akwai masu cewa tushensa yana Azerbaijan, ko kuma kusa Tamarra da Halwan[12] Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sunansa na Farsi shi ne Jurawan amma bayan shiga harshen Larabci sai aka koma ana kiransa da Nahrawan[13] Cikin rarrabawar Iraƙ a wannan zamani, Nahrawan wani ɓangare ne na garin Mada'in da yake babban birnin Bagdad.[14]
Bayanin kula
- ↑ Ƙazwini, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, shafi na 472; Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
- ↑ Alawi Isfahani, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, shafi na 413.
- ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325; Muhammadi Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
- ↑ Isɗarkhi Karkhi, Al-Masalik Wal Mamalik, shafi na 86.
- ↑ Alawi Isfahani, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, shafi na 413.
- ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
- ↑ Ƙazwini, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, shafi na 472.
- ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 242-243.
- ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 252.
- ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
- ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 245-246.
- ↑ Hamawi, Mu'ujam Al-Buldan, juzu'i na 5, shafi na 325.
- ↑ Hamadi Malayeri, Tarikh Wa Farhange Iran, juzu'i na 2, shafi na 244.
- ↑ «Hai'atul Istisma Tawajjih Bi Ishgal Al-Marakiz Al-Khadmiyya Fi Majma Basmaya As-Sakani,» gidan yanar gizo na Zagros News.
Nassoshi
- Hududul Alam min al-Mashriƙ ilal Maghrib, fassarar Sayyid Yusuf al-Hadi, Alkahira, Darus Saƙafa lin Nashr, 1423M.
- Alawi Isfahani, Ibrahim Bin Nasir, Muntaƙila Aɗ-Ɗalibiyya, binciken Muhammad Mahadi Khurasan, Qom, Al-Maktabatul Haidariyya, 1377Sh.
- Hamawi, Yaƙut Bin Abdullah, Mu'ujam Al-Buldan, Beirut, Darus Sadir, bugu na biyu, 1995M.
- Himyari, Muhammad Bin Abdullah, Ar-Raudul Mi'iɗar fi Khabaril Aƙɗar, binciken Ihsan Abbas, Beirut, Cibiyar Nasir lis-Saƙafa, bugu na biyu, 1980M.
- Isɗakhri Karkhi, Ibrahim Bin Muhammad, Al-Masalik Wal Mamalik, Beirut, Darus Sadir, 2004M.
- Muhammadi Malayeri, Muhammad, Tarikh Wa Farhange Iran dar Daurane Intiƙal az Asre Sasani be Asre Islami, Tehran, Ɗus, bugun na biyu, 1379Sh.
- «هیئة الاستثمار توجه باشغال المراکز الخدمیه فی محمع بسمایة السکنی»، (Mayar da hankali kan mamaye cibiyoyin hidima a rukunin gidajen zama na Bismaya), Gidan yanar gizon Zagros News, ranar da aka buga labari: 14 ga Agusta, 2022, ranar da aka duba: 14 ga Satumba, 2026M.
- Ƙazwini, Zakariyya Bin Muhammad, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, Beirut, Darus Sadir, 1380H.