Jump to content

Daƙiƙa:Jami'atul Mustafa Al-Alamiyya

Daga wikishia
Jami'atul Mustafa Al-Alamiyya
Kafawa2007 miladiyya
Waɗanda suka kafaSayyid Ali Husaini Khamna'i
ƘarƙashinOfishin jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Nau'in ayyukaKoyar da kuma bincike
Faɗaduwar aikiƘasa da ƙasa
ManufofiYaɗa ilimin Musulunci da tarbiyyar ɗaliban addini waɗanda ba 'yan Iran ba
AyyukaKoyarwa ta kai‑tsaye (a aji) da kuma ta yanar gizo•Fitar da wallafe‑wallafen bincike da na ilimi a harsuna daban‑daban•Buga littattafai da mujallu
WuriQum, Isfahan, Mashhad, da ƙasashe 60 daban
Halitana kan aiki
Cibiyoyin da suke ƙasantaJami'ar yanar gizo ta Al‑Muṣṭafa• Gidan Bugawa na ƙasa da ƙasa na Al‑Muṣṭafa• Cibiyar koyar da gajerun darussa
Adireshin yanar gizohttp://miu.ac.ir


Jami'atul Mustafa Al-Alamiyya ko Jami'ar Al‑Muṣṭafa ta Duniya wata cibiyar ilimi ce ta ƙasa da ƙasa mai asalin tsarin hauza (Makarantar addinin Musulunci), wadda aka kafa da nufin yaɗa ilimin Musulunci da kuma tarbiyyar ɗaliban addini waɗanda da ba 'yan Iran ba.

An kafa wannan cibiyar a shekarar 2007 miladiyya, ta hanyar haɗa "Ƙungiyar Hauzohi da Makarantun Addini na Waje" da "Cibiyar Duniya ta Ilimin Musulunci", bisa umarnin Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Hanyar aikinta ya ta'allaƙa ne kan ilimi, bincike, da kuma tarbiyya.

Jami'ar al‑Muṣṭafa tana da rassa 170 da ke ƙarƙashinta, kuma tana da cibiyoyin koyarwa a ƙasashe 60 na duniya. Bisa ga bayanin da cibiyar ta bayar, zuwa shekarar 2015 miladiyya, mutane 50,000 ne ke karatu a cikinta, daga cikinsu kuma 25,000 sun kammala karatu.

Ana gudanar da cibiyar ne ta Kwamitin Amintattu (Board of Trustees) kuma tana aiki ƙarƙashin kulawar ofishin Jagora.

Taƙaitaccen Tarihi

Kafin nasarar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, kasancewar ɗaliban addini da ba 'yan Iran ba a Hauzar Ilimi ta Qum ya kasance kaɗan ne, kuma yawanci ana gudanar da shi ta hanyar Cibiyar Darul Tabligil Islami (Cibiyar Yaɗa Addinin Musulunci).[1] Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, tare da ƙaruwa da sha'awar wasu su yi karatun ilimin addini a Iran, shugabannin hauza suka kafa "Majalisar Kula da Ɗaliban Addini da ba 'Yan Iran ba". Wannan majalisa ta ci gaba da aiki daga Shahriwar 1358 H.Sh (Agusta/Satumba 1979 M.) har zuwa 1365 H.Sh (1986/1987 M.). A wannan shekarar ne aka sake tsara tsarinta, aka kuma canza sunanta zuwa "Cibiyar Duniya ta Ilimin Musulunci".

Cibiyar Duniya ta Ilimin Musulunci ta kasance ana tafiyar da ita har zuwa 1372 H.Sh (1993/1994 M.) bisa tsarin gargajiya da ake amfani da shi a hauzozi. Amma daga wannan lokaci, bayan da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ya naɗa shugaba, cibiyar ta fita daga tsarin majalisa mai rashin tattara tsari wuri guda, kuma ayyukanta suka shiga ƙarƙashin kulawar Ofishin Jagora. Tsarin karatunta da takardun shaidar da take bayarwa suna samun amincewar Ma'aikatar Kimiyya, Bincike da Fasaha ta Iran.[Akwai buƙatar kawo madogara] An kafa "Ƙungiyar Hauzohi da Makarantun Addini na Waje" ne domin cika buƙatar Jagoran Jamhuriyar Musulunci wadda ta shafi horarwa da tarbiyyar ɗalibai addini daga ƙasashen waje ta hanya mai tsari da cibiyanci. An kafa wannan ƙungiya a shekarar 1991/1992 M., kuma a hankali ta kafa rassa a fiye da ƙasashe 45 na duniya.[2]

Bisa buƙatar Sayyid Ali Khamenei a ranar 28 Azar 1386 H.Sh (19 Disamba 2007 M.) cewa a haɗa waɗannan cibiyoyi biyu, aka kafa sabuwar cibiyar mai suna "Jami'atul Muṣṭafa A-Alamiyya (Jami'ar al‑Muṣṭafa ta Duniya)".[3]

Ali Rida A'rafi shi ne ya kasance shugaban wannan cibiyar tun daga kafuwarta har zuwa Aban 1397 H.Sh (Oktoba/Nuwamba 2018 M.), daga baya kuma aka zaɓi Ali Abbasi a matsayin sabon shugaba.[4]

Manufofi Da Tsari

A cikin kundin tsarin cibiyar, an ɗauki wasu manufofi a matsayin manyan buri na cibiyar. Daga cikinsu akwai: horar da mujtahidai, malamai, masu bincike, ƙwararru, malamai masu koyarwa, masu wa'azi, masu fassara, masu tarbiyya da shugabanni waɗanda suke masu tsoron Allah, masu sadaukarwa, kuma masu fahimtar zamaninsu; da kuma bayyanawa, samar da tunanin addini, da yaɗawa da watsa Musulunci na gaskiya da yake kan tafarkin Annabi Muhammadu (S.A.W).

Bisa wannan kundin tsarin, shugabancin ƙoli na Jami'at Al‑Muṣṭafa yana hannun Mujtahidi mai riƙe da jagorancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Haka kuma amincewa da kundin tsarin, zaɓen membobin kwamitin amintattu (Borad Of Trustee), da naɗa ko sauke shugaban jami'ar suna cikin ikon Jagoran.[5]

A halin yanzu, Murtada Muƙtadayi, Sayyid Hashim Husaini Bushehri, Muhammad Ali Taskhiri, Mahmud Muhammadi Araki, Sayyid Hassan Rabbani Khurasani, Sayyid Abul Hassan Nawab, Muhammad Hassan Mahadawi Mehr, da Mahadi Ahari Mustafawi su ne membobin tushe na kwamitin amintattu.

Haka kuma Ali Rida A'rafi, Muhsin Araki, Muhammad Hassan Akhtari, Abu Zar Ibrahimi Turkaman, Muhammad Mahadi Shabzindedar, da Muhsin Ƙummi su ne mambobin hukuma a wannan kwamitin.[6]

Bugu da ƙari, Shugaban Jami'at Al‑Muṣṭafa, wakilin Majalisar ƙoli ta Hauza, mataimakin hulɗar ƙasashen waje na Ofishin Jagora, shugaban Hukumar Al'adu da Hulɗar Musulunci ta Iran, babban sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul‑Baiti, da kuma babban sakataren Majalisar Duniya ta Kusantar Mazhabobin Musulunci su ne membobin hukuma na wannan cibiyar.[7]

Tushen Kuɗaɗen Shiga

Bisa ga sashe na 29 na kundin tsarin wannan cibiyar, tushen kuɗaɗen Jami'at Al‑Muṣṭafa sun haɗa da: taimakon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tallafin gwamnati, kuɗaɗen da ake samu daga kadarori da dukiyoyi, da kuɗaɗen shiga daga ayyukan hidima da ake bayarwa, waƙafi (Dukiyoyin sadaka), kuɗaɗen shari'a, kyaututtuka da tallafin kuɗi daga mutane ko ƙungiyoyi, da kuma rance ko sauƙaƙa bashin da ake samu daga bankuna da cibiyoyin kuɗi na cikin gida da na ƙasashen waje.[8]

Haka kuma, bisa ƙarin bayani na sashe na 34 na kundin tsarin, duba lissafi daga hukumomin da doka ta ba su damar duba lissafi da kula da kasafin kuɗin jama'a yana halatta, muddin shugabancin ƙoli ya amince da hakan.[9]

Fannonin Karatu Da Matakan Karatu

A Jami'at Al‑Muṣṭafa, ana koyar da fannoni na ilimin Musulunci kamar fiƙihu, usulul fiƙhi, Al'ƙur'ani, hadisi, falsafa, irfani, Akhlaƙ, ilimin kalam, da tarihin Musulunci.

Haka kuma a fannin ilimin ɗan Adam (Human sciences) ana koyar da fannoni da rassa kamar ilimin tarbiyya, shari'a (doka), ilimin halayyar ɗan Adam, tattalin arziki, ilimin zamantakewa, ilimin siyasa, harkokin banki, sadarwa, gudanarwa, da harsuna da adabinsu kamar Farisi, Larabci, Turanci, Faransanci, da Rashanci, duk da tsarin fahimta na Musulunci.

Ana koyar da waɗannan fannoni a cikin tsarin karatun hauza da kuma tsarin jami'a (akademik), a cikin kimanin fannoni da rassa guda 170, a matakai daban‑daban na tsarin ilimin hawza da na jami'a.

  • Matakin Shirye‑shiryen Farko (Koyar da harshen Farsi da ilimin Musulunci).
  • Mataki na 1 Diploma na farko / associate degree.
  • Mataki na 2 digiri na farko.
  • Mataki na 3 digiri na biyu.
  • Mataki na 4 – Doktora (PhD).
  • Mataki na 5 – Ijtihad (matakin samun ikon fitar da hukunci a fiƙihu).[10]

Koyarwa Ta Yanar Gizo

Wannan cibiyar ta kafa sashen karatu daga nesa (Jami'ar yanar gizo ta Al‑Muṣṭafa) Tun daga wannan lokaci, masu sha'awar karatu sun sami damar yin karatu a wannan cibiyar ta hanyar intanet (sararin yanar gizo).

Bisa bayanan da ke shafin Jami'at Al‑Muṣṭafa, har zuwa shekarar 2015/2016 M., ɗalibai daga ƙasashe 70 daban‑daban suna karatu a Jami'ar kama‑da‑wane ta Al‑Muṣṭafa. (jami'ar Yanar Gizo) Domin tallafa wa ɗalibanta, jami'ar ta samar da littattafan lantarki, darussa na lantarki, da kuma manhajojin koyarwa (Software na ilimi).

Daga cikin fannoni na karatu a wannan cibiyar akwai: Akhlaƙ, harshen Farsi da adabinsa, nazarin Musulunci, nazarin Al‑Kur'ani, fiƙihu, da kuma shari'a (doka).[11]

Ƙwasa‑ƙwasai Na Gajeren Zango

Koyarwa ta gajeren lokaci da kuma damar bincike na wannan cibiyar an tsara su ne musamman domin fitattun masu ilimi da masu tunani na duniyar Musulunci.

Wannan sashe na Jami'at Al‑Muṣṭafa yana ba masu bincike da malamai da ba 'yan Iran ba daga cibiyoyin ilimi da na al'adu damar bincike, tare da samar musu da yanayin gudanar da ayyukan bincike a kan batutuwan Musulunci.

Daga cikin sharuddan karɓa a wannan shiri akwai: Mallakar digirin digirgir (PhD) ko kuma kasancewa ɗalibi a matakin PHD a wata jami'a mai inganci, samun ƙwarewar koyarwa a jami'a ko wata cibiyar ilimi, da kuma samun tarihin bincike, rubuce‑rubuce, ko wallafa maƙalolin kimiyya.[12]

Hidima Da Tallafi

Daga cikin sauƙaƙawa da tallafin da wannan cibiyar ke bayarwa ga ɗalibanta akwai: taimako wajen samun biza da izinin zama na karatu, biyan tallafin karatu (kuɗin makaranta), tallafin gidaje da kuma rancen kuɗi ba tare da riba ba, samar da masaukin ɗalibai (Ɗakunan kwana), bayar da hidimomin lafiya da jinya, shawarwari na ilimi da tarbiyya, koyar da ƙwarewa da sana'o'i masu amfani ga mata da 'ya'yan ɗalibai, samar da kayayyakin wasanni, da kuma shirya karatu na musamman ga iyalan ɗaliban addini. Waɗannan na daga cikin abubuwan tallafi da wannan cibiyar ke tanada ga masu bincike da ɗalibanta.[13]

Sassan Koyarwa Na Ilimi

Babban ofishin Jami'at Al‑Muṣṭafa yana cikin Iran, a birnin Qum, kuma akwai fiye da sassa ko rukunin koyarwa 170 da suke ƙarƙashinta a cikin Iran da kuma a ƙasashen waje.

Waɗannan sassan suna cikin biranen Mashhad, Tehran, Isfahan, Gorgan da Ƙeshem, da kuma a fiye da ƙasashe 60 na duniya.

Daga cikin ƙasashen waje da ake da waɗannan rukunin koyarwa akwai: Afirka ta Kudu, Albaniya, Jamus, Afganistan, Indonesiya, Ingila, Uganda, Birazil, Bulgariya, Bangaladesh, Burkina Faso, Bosniya da Herzegovina, Benin, Pakistan, Tanzaniya, Thailand, Togo, Denmak, Japan, Ivory Coast, Siwidin, Senegal, Siriya, Sierra Leone, Iraƙi, Ghana, Philippines, Kyrgyzstan, Kazakhstan, Kamaru, Kosovo, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, Comoros, Gambia, Georgia, Guyana, Guinea, Labanun, Madagascar, Malawi, Malesiya, Mali, Myanmar, Norway, Nijar, Najeriya, Indiya, da sauransu.[14]

Ƙungiyar Jami'o'in Duniyar Musulunci (FUIW), Ƙungiyar Jami'o'i ta Duniya (IAU), Ƙungiyar Shugabannin Jami'o'i ta Duniya (IAUP), Ƙungiyar Jami'o'in Asiya da Tekun Pasifik (AUAP), da kuma Ƙungiyar Daliban Duniyar Musulunci (Rohama) na daga cikin ƙungiyoyin kimiyya da Jami'at al‑Muṣṭafa ke da mamba a cikinsu.[15]

Bisa ga abin da aka rubuta a shafin yanar gizo na Jami'atul Al‑Muṣṭafa, har zuwa shekarar 2015/2016 M., wannan cibiyar ta koyar da fiye da ɗalibai maza da mata 50,000 daga ƙasashe 122 daban‑daban, kuma kusan 25,000 daga cikinsu sun kammala karatunsu.[16]

Cibiyar Bincike

Waɗannan su ne wasu daga cikin rukunin bincike na Cibiyar Bincike ta ƙasa da ƙasa ta Al‑Muṣṭafa:Ilmin kalam da mazhabobi, Falsafa da irfani (Sufanci), Nazarin Al‑Kur'ani da Hadisi, Tarihi, Fiƙihu da Usul al‑Fiƙhi, Nazarin Mahadawiyya (Imani da zuwan Imam Mahdi), Nazarin zamantakewa da sadarwa, Tunani na siyasa da Juyin Juya Halin Musulunci, Nazarin Afirka da duniyar Larabawa, Nazarin duniya (global studies), Nazarin Asiya da yankin Tekun Fasifik, Nazarin Shi'awa, Nazarin Hawzohin ilimi da malamai na addini, Nazarin addinan Ibrahimiyya, Addinan Gabas, da kuma ƙungiyoyi ko sabbin aƙidu da suka bayyana kwanan nan..[17]

Bugawa Da wallafawa

Ayyukan bincike da koyarwa na Jami'atul Al‑Muṣṭafa ana bugawa da wallafawa da harsuna da dama, ciki har da: Farsi, Larabci, Turanci, Faransanci, Jamusanci, Rashanci, Urdu, Azeri, Turkancin Istanbul, Hausa, Swahili, Bengali, da Tajiki.

Ana bugawa da kuma rarraba waɗannan littattafai da wallafe‑wallafe a ƙasashe kamar Ingila, Indonesiya, Malesiya, Labanun, Indiya, Pakistan, Afganistan, da Thailand..[18]

Mujallu

  • Mujallar ƙwata‑ƙwata ta ƙungiyar kimiyya ta Mizan.
  • Mujallar ƙwararru ta ƙungiyar fiƙihun Shari'ar kotuna.
  • Mujallar ƙwararru ta Ƙungiyar Ilmin Kalam na Musulunci.
  • Mujallar ƙwata‑ƙwata ta ƙungiyar kimiyya ta Roshana'i.
  • Mujallar bincike kan Hikima da Falsafar Musulunci.
  • Mujallar ƙwararru ta ƙungiyar fiƙihun tattalin arziki.
  • Jaridar sau biyu a wata ta bayanai mai suna al‑Bayan.
  • Mujallar ƙwararru ƙwata‑ƙwata kan binciken yankuna.
  • Mujallar kimiyya mai sau biyu a shekara kan Al‑Kur'ani da Kimiyya.
  • Mujallar al'adu da zamantakewa ƙwata‑ƙwata mai suna Ṭali'at Nur.
  • Mujallar ƙwararru ƙwata‑ƙwata ta Larabci mai suna Al‑Ḥayat Al‑Ṭayyiba (Rayuwa Mai Kyau).
  • Mujallar al'adu da zamantakewa kwata‑kwata mai suna Shamim Huda.
  • Mujallar ƙwararru ta ƙungiyar binciken Shari'a.
  • Jaridar sau biyu a wata ta bayanai mai suna Safiran Nur.
  • Mujallar kimiyya mai sau biyu a shekara mai suna Sukhane Tarikh (Maganar Tarihi).
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan nazarin karatun Al‑Kur'ani.
  • Mujallar kimiyya ta bincike sau biyu a shekara mai suna Binciken Ilimin Kalam.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan nazarin fiqhun tarbiyya.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan fiƙihun mazhabar Imamiyya.
  • Mujallar ƙwararru ta ƙungiyar Nistan kan addinai da mazhabobi.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan Usul fiƙihi na Imamiyya.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan koyar da harshen Farsi.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan ilmin hadisi na kwatantawa.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan ilimin ɗan‑adam na Musulunci.
  • Mujallar kimiyya mai yaɗa ilimi sau biyu a shekara mai suna Nazarin Kur'ani na masu nazarin Gabas (Orientalists).
  • Mujallar kimiyya ta bincike sau biyu a shekara kan tarihin duniyar Musulunci.
  • Mujallar kimiyya ta bincike ƙwata‑ƙwata kan nazarin kwatantawa tsakanin Al‑Kur'ani da Hadisi.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan mata da iyali a Musulunci.
  • Mujallar ƙwararru sau biyu a shekara kan da'awa da sadarwar addini.
  • Mujallar kimiyya mai yaɗa ilimi sau biyu a shekara kan fiƙihun Musulunci da tushen shari'a.
  • Har ila yau akwai wasu mujallu da ake bugawa da harsuna daban‑daban, kamar:
  • HIKMET
  • Lumturia
  • RELIGIOUS THOUGHT
  • Metafyzika dhe Morali
  • Pure Life (Student Journal)
  • THE LIGHT OF THE QUR'AN
  • Journal of Shi'a Islamic Studies
  • Misbah İslami Düşünce ve Araştırma Dergisi.[19]

Bayanin kula

  1. Ja'fariyan, Rasul, Jaryan-ha va Sazman-ha-ye Mazhabe‑Siyasi‑ye Iran, ṣ. 328.
  2. Juzwa-ye ashenayi ba Sazman-e Hawzeha wa Madares-e Elmiyye-ye Kharej az Keshvar, Qom, Sazman-e Madares-e Kharej az Keshvar, shafi na 4-5.
  3. Asasname-ye Nahad-e Elmi wa amuzeshi-ye Jame‘at al-Muṣṭafa al-‘alamiyya (Mosavvab-e Jalse-ye 635-om-e Shora-ye ali-ye Enqelab-e Farhangi).
  4. «رئیس جدید جامعi المصطفی العالمیi انتخاب شد»، خبرگزای دانشجویان ایران،
  5. Asasname-ye Nahad-e Elmi wa amuzeshi-ye Jame‘at al-Muṣṭafa al-‘alamiyya (Mosavvab-e Jalse-ye 635-om-e Shora-ye ali-ye Enqelab-e Farhangi)."
  6. سایت اطلاع رسانی جامعi المصطفی العالمیi.
  7. Asasname-ye Nahad-e Elmi wa amuzeshi-ye Jame‘at al-Muṣṭafa al-‘alamiyya (Mosavvab).
  8. Asasname-ye Nahad-e Elmi wa amuzeshi-ye Jame‘at al-Muṣṭafa al-alamiyya (Mosavvab-e Jalse-ye 635-om-e Shora-ye ali-ye Enqelab-e Farhangi).
  9. Asasname-ye Nahad-e Elmi wa amuzeshi-ye Jame‘at al-Muṣṭafa al-alamiyya (Mosavvab-e Jalse-ye 635-om-e Shora-ye ali-ye Enqelab-e Farhangi).
  10. سایت جامعi المصطفی العالمیi
  11. سایت موسسi آموزش‌iای کوتاi مدت و فرصت‌iای مطالعاتی.
  12. سایت اطلاع رسانی جامعi المصطفی العالمیi.
  13. سایت اطلاع رسانی جامعi المصطفی العالمیi.
  14. سایت اطلاع رسانی جامعi المصطفی العالمیi.
  15. سایت اطلاع رسانی جامعi المصطفی العالمیi.
  16. وب سایت جامعة المصطفی، تاریخ بازدید ۱۳۹۵/۱۲/۱۴.
  17. سایت پژوiشگاi بین المللی المصطفی.
  18. سایت اطلاع رسانی جامعة المصطفی العالمیi.
  19. سامانه یکپارچه نشریات جامعه المصطفی العالمیه.

Nassoshi