Babul Sa'at

Daga wikishia

Babul Sa'at (Larabci: باب الساعات) ko ƙofar Sa'at, wani wuri ne a ƙasar Siriya da aka tsare fursunonin Karbala tsawon lokaci kafin shigar da su fadar Yazidu, Sahal Sa'idi, Sahabin Annabi (S.A.W), ya bada rahoton yadda aka shigar da su ta ƙofar Sa'at da take Damashƙ, da wannan dalili ne aka ambaci sunan wannan ƙofar a Adabin Ashura.

Dalilin Sanya Mata Wannan Suna

Zanen taswirar tsofaffin ƙofofin garin dimashƙi

Babul Sa'at ɗaya ce daga ƙofofin shiga masallacin bani umayya da yake garin Dimashƙi, saman wannan ƙofa an rataye wani ƙaton Agogo, haka kuma ana kiran wannan ƙofa da sunan Babul Jirun,[1] an samata wannan suna ne sakamakon agogon da aka rataya a saman ƙofar,[2] haka kuma cikin matanan litattafan riwaya da suke da alaƙa da rahotannin da aka bayar kan fursunonin Karbala a lokacin da aka kai su Sham an ambaci babul sa'at,[3] an ce wannan ƙofar Sa'at ba ta kasance ƙofar sa'at ta masallacin Umawi na Damashƙ ba, an ajiye kan Imam Husaini (A.S) tsawon lokaci a wannan wuri kafin shiga fadar Yazidu,[4] sakamakon tsare fursunonin Karbala tsawon lokaci sai wannan ƙofa ta samu shahara.[5] Na'am akwai wasu jama'a da suke ganin ayarin fursunin Karbala sun shiga Sham ne ta ƙofar Tauma'u.[6] sannan akwai waɗanda suka ce ai ƙofar Sa'at ita ce dai ƙofar Tauma'u daga ungunwar da Kiristoci suke zaune a Damashƙ, kuma har zuwa yanzu akwai kufaifayinta da suka rage.[7]

Rahoton Sahal Sa'idi

An karɓo daga Sahal Sa'idi lokacin da fursunonin Karbala suka shiga Damashƙ mutanen gari sun ratu bakin ƙofar Sa'at suna murna suna rawa tare da shewa[8] Shaik Abbas ƙummi ya bada rahoto daga Kamil Baha'i cewa an tsare iyalan Imam Husaini (A.S) har tsawon kwanaki uku a ƙofar shiga Dimashƙi.[9] Sahal Sa'idi ya bada labarin yanda aka shiga da fursunonin Karbala garin Damashƙ, a cewarsa an shiga da su alhalin an ɗaga kawunkan Shahidai sama suna tsire kan tsinin masu ana kora su tare da fursunoni, sai Sukaina ƴar Imam Husaini (A.S) a bada wata dukiya ga waɗannan da suka ɗaga kawukan shahidai da su motsa ga can su dena tafiya tare da su domin waɗanda ba muharramansu ba kada su kalli matan da suke cikin wannan ayarin fursunon,[10] da wannan dalili ne cikin karatun makokin Imam Husaini (A.S) za ka ji ana maganar Babul Sa'a. Cikin Babul Sa'a da take Masallacin Umawi, akwai wani ƙaton Dutse da aka ce anan ne Habila da ƙabila suka ɗora abin da suk sadaukarwa da neman kusanci.[11]

Adabi Da Al'adar Farisanci

An yi amfani da Kalmar Babul Sa'at a cikin adabin farisanci da waƙoƙi, wannan kalma anyi ishara da ita cikin waƙoƙin Ashura daga fuskanin Halab da Kufa wanda daga nan aka koro fursunonin Karbala tare da tsare su. wakar da za ta zo a kasa tana cikin jumlar wakokin da aka rera a kan wannan batu:

Mutanen garin sham sun yi cincirindo da turmutsitsi* Yayin da aka kawo tsarakakakken kan Husaini garin sham

suna ta murna suna shewa da farin ciki da ganin yankakken kan Husaini

Zainab kadai take kuka da bakin ciki sun shagaltu da buga bandiri suna ta shewa

Mutanen garin sham suna kewaya Zainul Abidin suna shewa suna tafi

Malam Sahal saboda zafin zuciya da rai daga abin da ya afku haka ya shiga ta kofar Sa'at

An bude kofar sa'at sai ya ga kai kace rana ta bude.[12]

Shirin talabijan

Babul Sa'at sunan wani shiri ne na talabijin mai kashi huɗu da aka yi a shekara ta 2008, wanda Sayyid Jawad Hashemi ya ba da umarni, ya rubuta shi kuma ya shirya shi, wanda ke ba da labarin abubuwan da suka faru a kewayen wannan ƙofa a lokacin isowar fursunonin karbala. An watsa wannan fim aTashar Al-Kur'an ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran.[13]

Bayanin kula

  1. Ibn Battuta, Safarnameh, 1359, juzu'i na 1, shafi na 90.
  2. Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, Darul Fikr, juzu'i na 9, shafi na 158.
  3. Duba: Majlesi, Bihar al-Anwar, 1404 AH, juzu'i na 45, shafi na 128.
  4. Duba: Bizoun,Mausu'atu Al-Karbala, 1427 AH, juzu'i na 2, shafi na 414.
  5. Muhaddi, Farhang Ashura, 1378, shafi na 188
  6. Ibn Atham, al-Futuh, 1411 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 129-130.
  7. Shahidi, “Bab al-Sa’at” Dayiratul Almarif, 1380, juzu’i na 3.shafi na 12; Muhaddi, Farhang Ashura, 1378, shafi na 188.
  8. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1404H, juzu'i na 45, shafi na 128.
  9. ƙomi, Nafs Al-Mahmum, 1421 AH, shafi na 394.
  10. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1404 AH, juzu'i na 45, shafi na 128; Khwarazmi, Maktal al-Hussein, 1423 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 68.
  11. Hamawi, Majam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 2, shafi na 464; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, Darul Fikr, juzu'i na 9, shafi na 154.
  12. بازگشتم آتش از پا تا به سر، «پایگاه اطلاع‌رسانی نخل میثم».
  13. <a class="eɗternal teɗt" href="https://ƙurantɓ.ir/content/10240">مینی سریال «دروازه ساعات»</a>

Nassoshi

  • Bizoon, Labib, Mausu'atu Karbala, Beirut, Al-Alami Foundation, 1427 AH.
  • Hamawi, Yaƙut bin Abdallah, Majam Al-Buldan, Beirut, Dar Sadir, 1995.
  • Ibn Atham Koofi, Ahmed, Al-Futuh, bincike na Ali Shiri, Beirut, Darul Awtah, 1411H/1991 Miladiyya.
  • Ibn Battuta, Safarnameh Ibn Battuta, wanda: Mohammad Ali Mohd, Tehran, Kamfanin Fassara da Bugawa, 1359 ya fassara.
  • Ibn Kathir Damashƙ, Ismail Ibn Umar, al-Badaiya and al-Nahiya, Beirut, Dar al-Fikr, Bita.
  • Khwarazmi, Muwafaƙ bn Ahmad, Maƙtale Al-Hussain r.a, ƙum, Anwar Al-Huda, 1423H.
  • Majlisi, Mohammad Baƙer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1404 AH.
  • Mini-Siryal "Babul Sa'at". An sabunta ta Agusta 30, 2019.
  • Muhaddi, Jawad, Farhang Ashura, ƙom, shahararren bugu, 1378.
  • Shahidi, Abdul Hossein, "Bab al-Saat", Dairat Al-Arif Shi'i (Juzu'i na 3), Shahid Saeed Mohebi Publication, 1380.
  • ƙomi, Sheikh Abbas, Nafs Al-Mahmoum, Najaf, Al-Maktab al-Haydriya, 1421H.