Ayar shaida

Daga wikishia
(an turo daga Ayar shaid)
Ayar Shaida

Ayar shaida (arabic: آية الشاهد) ita ce aya ta goma sha bakwai 17 a cikin Suratul Hudu, wadda take tabbatar da haƙiƙanin gaskiyar annabtar manzon Allah (S.A.W) wadda ta kasance ta hanyar Alkur'ani maigirma da Muminai na Hakika da kuma littatafan da aka saukar daga sama. Waɗanda suka gabaci Al-ƙurani. bayan Muhsrikai sun zargi Annabi (S.A.W) da kasancewa Makaryaci domin tausasar sa da kuma ƙarfafa imaninsa Sai wannan aya ta sauka.

Yazo cikin littatafan tafsiri da kuma riwayoyi na ɓangaren shi’a da na Ahlus-sunna cewa abinda ake nufi da shaida a cikin wannan ayar shine Imam Ali (A.S) ɗan abi ɗalib. Hakanan wasu ruwayoyin sun ambaci Jibrilu da kuma shi kanshi manzon Allah a matsayin shaida, wasu kuma suka ce Al-kurani ne. Hakim Hasakani ya kawo riwayoyi sama da 16 da suke tabbatar da cewa Imam Ali (AS) shaida ne a cikin littafin Shawaheed At-Tanzil Hakanan ana kafa hujja da ayar shaida kan tabbatar da wilayar Imam Ali Bn abi Talib kan Halafancin Imam Ali (A.S) sabida siyaƙin ayar babu makawa manzon Allah shine shaida, Don haka kasancewar ayar mubahala (fito na fito) tanuna imam Ali kansa shine annabi kansa, hakan annabi shine imam ali kansa.

Nassin Aya

Aya ta goma sha bakwai 17 a Suratul Hudu [1]ta shahara ana kiranra da sunan ayar shaida.

افمن كان على بيينة من ربه ويتلوه شاهد منه ومن قبله كتب موسى اماما ورحمة ، أولئك يؤمنون به ، ومن يكفر به من الأحزاب فالنار موعدهم فلا تك فى مرية منه انه الحق من ربك ولكن أكثر الناس لا يؤمنون
Shin yanzu wanda ya kasance kan hujja bayananniya daga Ubangijinsa kuma wata shaida taba biyar sa daga gare shi. kuma gabaninsa akwai littaffin Musa abin koyi da rahama, waxannan suna yin imani da shi, duk wanda ya kafirta da shi daga qungiyoyi to wuta ce makomarsa. saboda haka kada ka kasance cikin shakka daga gare shi lallai shi gaskiya ne daga Ubangijinka sai dai cewa mafi yawan mutane basa imani.



(Kur'ani: Hudu: 17)


Abinda Ayar Ta Kunsa

Allama Ɗabaɗaba'i a cikin tafsirin Almizan ya ce ana fahimta daga zahirin ayar cewa ta saukane domin samar da yanayin tabbatar diga-digan Annabi (S.A.W) da kuma karfafarsa kan abin da Allah ya saukar masa. ance wannan aya ta sauka ne kan kihsiyantar Mushirikai bisa tuhumr Annabi (S.A.W) da suka da yin karya Ya zo cikin tafsirin amsal da kuma majma'ul bayan mahanga guda biyu. Mahanga Ta Farko

Abin da ake nufi da

افمن كان على بثينة منه به

shi ne Manzon Allah (S.A.W) ta hanya uku za a tabbatar da gaskiyar annabtakar sa.

1:- kasancewar al-kurani wanda ya kasance bayyananniyar hujja. 2:- littattafan da aka saukar daga sama wanda suka gabata irinsu Attaura da suka yi nuni zuwa siffofin Manzon ALLAH bayyanannu 3:- Mabiya Annabi na gaskiya Masu sadaukarwa Muminai misalin Ali Bn Abi Talib wadanda samuwar mutane irinsu a kowacce tafiya tana gasgata wannan Matafiya

Abi da ta Tattaro

Allama Tabataba’i, a cikin Tafsirin Almizan, yana ganin ayar Shahid a matsayin ginshikin tsayuwar imani da Annabi (S.A.W) ga littafin Allah. A cewarsa wannan ayar ta sauka ne a kan zargin da Mushrikai suke yi na cewa Annabi (S.A.W) ya yi karya[2]

A cikin tafsirin Majma'u Al-Bayan da tafiri Namuneh, an ambaci tafsiri guda biyu ga wannan ayar;

Abin da ake nufi da

افمن كان على بينة من ربه

gaba dayan muminan da suka yi imani bayan bayyanar hujjoji daga Annabi karara kuma a fili, baya ga gasgata shi da littattafan da aka saukar daga sama suka yi kan annabtar sa.

Sannan ma’anar البيّنة Allama Ɗabaɗaba'i ya ce hujjace wacce take bayyananniya me bayyanar da wasunta kamar haske,

Allama Ɗabarasi kuma yace

بينة من ربه

tana nufin hujja daga hankalinsa.

Wanene Shaida

Wasu daga Malaman tafsiri na shi’a da Ahlus-sunna sun tafi akan cewa shaida a cikin aya ta goma sha bakwai 17 ta suratul Hudu, shi ne Imam Ali Bn abi Talib kasancewar sa farkon wanda ya yi imani da Annabi muhammad (S.A.W) Sannan ya zo daga riwayar imam Ali kan tabbatar da shi ne shaida da kansa acikin ayar. Hakim Hasakani ya rawaito cikin littafinsa Shawaheed At-Tanzil riwayoyi sha biyar 15 wadanda ke bayyana Imam Ali (A.S) a matsayin shaida cikin ayar.

Daga cikin riwayoyin akwai riwayar Anas Bn malik kan cewa

افمن كان على بينة من ربه

ya ce shi ne Imam Ali Bn abi Talib, sannan Imam Ali ya kasance harshen manzon Allah (S.A.W) (wakilinsa) zuwaga mushirikan makka alokacin da suka saba al-ƙawarinsu da annabi.

Akwai wasu riwayoyin (Ɗabarasi) daban akan abinda ake nufi da shaida acikin ayar shine Jibrilu, sakamakon shine me karantawa manzon ALLAH wahayi (al-kurani) daga ALLAH, wasu kuma suka tafi akan cewa shaida shine harsher manzon Allah (S.A.W) wanda yake karanta Alkurani da shi aduk lokacin da yake karatu, Wasu kuma suka tafi kan cewa Alkurani kansa shine shaida . Sai dai Allama Ɗabaɗaba'i ya yi raddi akan sauran ra’ayoyin sannan ya ya kafa hujja da riwayoyi a bisa kasancewa Imam Ali (A.S) shi ne shaida a cikin wannan ayar.

Shiryarwa zuwa ga Wilayar Imam Ali Da Halifancinsa

an yi amfani da ayar Wilaya domin Tabbatar da matsayin da wilayar (imamanci) da kuma halifancin (shugabanci) Wasu daga masana da kuma tahkiki sun ce kalmarيتلوه da ke cikin ayar shaida tana nufin يتّبعه da ma’anar yana binsa ba yana karanta shi ba, sabida lamirin يتلوه acikin منه yana komawa ne ya zuwa افمن a farkon ayar, bisa hakane abin nufi da lamirin منه shi ne wanda yake da alaka ma'anawiyya da zatiyyar Manzon Allah (S.A.W), kuma na nufin shi Annabin a kankin kansa.

kamar yadda fi’ili mudhari’i yake nuni da cigaba acikin aiki da kuma ba da sakamakon Manzon Allah dai shine shaida a cikin dukkanin matakai da zamununnuka, wanda shi ne dacewar matsayin halifanci da imamanci zuwa ga wasiyyin manzon Allah wato Imam Ali, wanda aka bayyana shi a matsayin Annabin kansa ta hanyar riwayoyi da kuma ayar mubahala (fito na fito) wato Imam Ali (A.S).

Mahanga A Cikin Attaura

An ambaci littafi daya daga cikin littattafan da aka saukar (Attaura) acikin ayar shaida, dalilin hakan shine watsuwar ra’ayoyin Yahudawa da abinda suka yi imani da shi a cikin al’ummar Musulmi, da kuma yanayin da Alkur'ani ya sauka a ciki da Kiristoci da suke garuruwan sham da Yaman, Karin dalili kuma shine ambaton siffofin Manzon Allah da yazo cikin Attaura a bayyane.

Bayanin kula

  1. Allameh Hali, Nahj al-Haƙ, 1407H, shafi na 195.
  2. Allama Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 10, shafi na 183.

Nassoshi

  • Ibn Hayun al-Maghribi, Nu'man bn Muhammad,Da'a'imul Islam fi Zikiril Halal wa Haram, Al-ƙadaya da Al-Ahkam, Kum, Al-Bait (A.S.), Bugu na biyu, 1385 Hijira.
  • Ibn Ughda Kufi, Ahmad Ibn Muhammad, Fadael Amir al-Mu'minin (AS), ƙom, Dilil Ma, 1424H.
  • Haskani, Obaidullah bin Abdallah, shawaheed Al-Tanzil,Tehran, Cibiyar Buga Ma'aikatar Shiriya, 1411H.
  • Hawizi, Abd al-Ali bin Juma, Tafsir Noor Al-Saghalin, ƙum, Ismailian Institute, 1415 AH.
  • Siyuti, Abd al-Rahman bin Abi Bakr, Al-Dur al-Manthur fi al-Tafsir al-Mathur, ƙom, Ayatullah Murashi Najafi Library, 1404 AH.
  • Tabatabaei, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Taƙsir al-ƙur'an, Beirut, Al-Alami Press Institute, 1390 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma Al Bayan, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Allameh Hali, Hassan bin Yusuf, Nahj al-Haƙ, ƙum, Darul Hijra Institute, 1407H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-kafi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Nashon, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1371.
  • Mansouri, Seyyed Mohammad da Zahra Sadeghi. وجوه مختلف ادبی در عبارت آغازین آیه ۱۷ سوره هود و بازتاب آن در تفسیر عبارت شاهد منه» A cikin Mujallar Bincike na Kimiyyar Kur’ani da Hadisi, lamba ta 26, 1394.
  • Hilali, Sulaim bin ƙays, littafin Sulaim bin ƙays al-Hilali, Kum, Al-Hadi, 1405H.