Jump to content

Auren Misyar

Daga wikishia

Auren misyar (Larabci: نكاح المسيار) wani nau'in aure ne a wurin ahlus-sunna. Wannan aure yana tattare da sharuɗɗan auren da'imi a wurin ahlus-sunna daga misalin karanta sigar aure, halartar shaidu guda biyu da sadaki, sai dai cewa cikin wannan aure matar bisa zaɓinta tana yafewa mijinta haƙƙin ɗawainiyar ciyar da ita da haƙƙin kwanciya wuri ɗaya, cikin wannan aure miji zai iya zuwa wurin matarsa duk sanda ya buƙaci hakan, ita ma matar tasa tana da ƴancin cikin al'amuranta.

Auren misyar ya yi kama da auren mutu'a a wurin ƴan shi'a ta fuskanin rashin wajabcin haƙƙin samarwa mace matsuguni kan miji da ciyarwa; haka kuma ya yi kama da auren da'imi ta fuskar iyakantuwar matan da za a aure cikin adadin matan huɗu, buƙatar halartar shaidu, rabuwa ta hanyar saki, khulu'i ko fasaki, waɗanda dukkaninsu babu su a cikin auren mutu'a, ana cewa shi auren misyar yana cikin sababbin maudu'ai cikin fiƙihu wanda a karo na farko ya ɓulla a yankin Tamin ƙasar Saudiyya, Fahad Ganim ya kasance mutum na farko da ya fara amfani da isɗilahin auren misyar.

Malaman fiƙihun shi'a bisa la'akari kamanceceniyar misyar da mutu'a da kama daga fuskanin samuwa sun tuhumi malaman ahlus-sunna da yin fatawa mai fuska biyu cikin haramta auren mutu'a da halasta auren misyar. Bisa rahotan Nasir Makarim shirazi bakiɗayan malaman fiƙihu na shi'a da suka yi bahasi game da auren misyar bisa la'akari da sharuɗɗan yin fatawa sun halasta wannan aure, wasu jama'a daga masu fatawa daga ahlus-sunna sun halasta auren misyar wasu kuma daga cikinsu sun haramta shi, wasu ba'ari kuma sun dagata ba su ce komai ba kan hukuncin halasci ko haramcin wannan aure.

Sanin Ma'ana

Auren misyar wani nau'in aure ne da yake tattare da sharuɗɗan auren da'imi a wurin ahlus-sunna misalin karanta siga ta shari'a cikin ɗaure aure, halartar shaidu biyu da kuma sadaki. Cikin wannan aure bisa zaɓi mace tana yafe haƙƙin ciyarwa da kanciya wuri ɗaya..[1] a cewar Yusuf ƙardawi mufti ahlus-sunna, auren misyar a galibi bai fiye kasancewa auren farko ga namiji ba, yawanci za ka samu dama yana da matarsa da yake ɗauke mata nauyin ciyarwa da matusguni.[2] A cewar Abdullahi Mani'u, memba cikin majalisar manyan malaman ƙasar saudiyya, haƙiƙa auren misyar ya na tattare da dukkanin hukunce-hukuncen aure daga gado, sadaki da halascin ƴaƴan da aka haifa, kuma mace za ta iya kau da kai daga ba'arin haƙƙoƙinta misalin kwanciya da ciyarwa.[3] Wahaba Zuhaili, malamin fiƙihu daga ahlus-sunna shi ma ya tabbatar da cewa haƙƙin gado yana nan a kiyaye cikin auren misyar.[4]

Cikin wannan aure duk sanda miji ya buƙaci zuwa wurin matarsa zai iya zuwa, ita kuma tana da ƴanci cikin al'amuranta.[5]kalmar misyar bata da samuwa cikin harshen larabci, kalma ce ta harshen amawa gama garin larabawa da take da ma'anar abu mai sauƙi da kuma sauri.[6]

Kamanceceiya Da Kuma Bambancinsa Da Auren Mutu'a

A cewar Nasir Makarim Shirazi, auren misyar yana kama da auren mutu'a saboda cikin misyar mace za ta yi zamanta a gidanta ta ɗauki nauyin kanta.[7] cikin duka auren guda biyu (Mutu'a da misyar) mace ba ta da haƙƙin ciyarwa da kwanciya da matsuguni, kuma ma'aurata ba za su gaji junansu ba, ƙari kan wannan bata buƙatar izinin mijinta domin fita unguwa.[8]

Bambanci tsakanin misyar da mutu'a shi ne cewa a auren mutu'a wajibi ne a ayyana lokacin da auren zai ɗauka, amma a cikin auren misyar ana ɗaura shi ne da surar aure na da'imi, haka nan haddi adadin matan da za a iya aura a misyar bashi da bambanci da auren da'imi ma'ana mata huɗu ne, amma a auren mutu'a babu iyakance adadi, haka nan sun ƙara bambanta da juna cikin hanyar rabuwa, shi misyar a na rabuwa ne ta hanyar saki, khulu'i, ko fasaki; amma shi auren mutu'a ana rabuwa ne ta hanyar ƙarewar lokacin da aka ɗauka ko kuma yafe ragowar lokacin da ya rage.[9] ƙari kan haka ɗaura auren misyar yana buƙatar halartar shaidu biyu, daidai lokacin auren mutu'a kwata-kwata babu wannan sharaɗi cikinsa.[10]

Taƙaitaccen Tarihin Samuwa

Ana cewa auren misyar yana cikin sababbin maudu'an fiƙihu wanda ya kari na farko ya ɓulla a yankin Tamim ƙasar Saudiyya, Fahad Ganim shi ne mutum na farko da ya fara amfani da isɗilahin misyar a Saudiyya,[11] wannan aure sannu-sannu a hankula-hankula ya dinga cirata tana tsallakawa ƙasashen larabawa misalin Qatar, Kuwait, Baharaini da Imarat akwai tsammanin ya shiga sauran ƙasashe.[12] ba'arin malaman ahlus-sunna sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen samawa misyar wuri cikin misalsalan fiƙihunsu.[13]

Sakamakon tsananta da tsadar buƙatun auren daga misalin samar da matsuguni da tsananin tsadar sadaki da kuma sha'awar da maza suke da ita cikin ɓoye aurensu na biyu sai wannan aure ya ɓulla cikin al'umma ahlu-sunna. ƙaruwar adadin zawarori wanda basu da mai kula da su, buƙatar maza ta ƙara aure adadin mata sakamakon wasu dalilai kamar misali cikin halin rashin lafiyar matarsa ta farko, ko kuma ace ita wace za a aura za ta ɗauke nauyin mijin da zai aure0.ta, duka waɗannan suna daga sabubba da illolin da suka kawo ɓullar auren misyar.[14]

Masu bincike daga shi'a sun yi amanna cewa adawar da fiƙihun ahlus-sunna yake yi da auren mutu'a da kuma yaƙar duk hanyoyinsa shi ne abin da ya haifar da ɓullar auren misyar.[15] ba'arin malaman fiƙihun shi'a sun yi raddi da suka kan malaman ahlus-sunna cikin wannan maudu'i na misyar tare da zarginsu da yin fuska biyu, a cewar su bisa la'akari da kamanceceniyar mutu'a da misyar da kamar da suke da ita cikin fagen samuwa, da wane dalili ne mufi na ahlus-sunna zai haramta auren mutu'a a gefe guda kuma ya halasta auren misyar.[16]

Hukuncin Auren Misyar

A rahotan Nasir Makarim Shirazi, bakiɗayan malaman fiƙihun shi'a da suka yi bahasi kan maudu'in misyar bisa la'akar da sharuɗɗan aure sun bada fatawar halasci kan wannan aure.[17] a ra'ayin malamin misalin wannan aure yana kasancewa ingantacce idan ya kasance kan fuskoki guda biyu:

1.cikin matanin sigar ɗaura auren bai kamata a kawo sharaɗin rashin neman haƙƙoƙi misalin ciyarwa, kwanciya, matsuguni da gado, bari dai mace da kanta ne bisa kyautatawa za ta ɗaukar ma kanta alƙawarin ba za ta nemi waɗannan haƙƙoƙi daga wanda ya aure ta ba.

2. wajibi ne Kau da kai daga ba'arin haƙƙoƙi ya kasance cikin matanin aure cikin yanayin sharaɗin aiki, ba wai sharaɗin natija da sakamako ba, cikin sharaɗin aiki mace za ta ce zan aureka ba kuma zan nemi haƙƙin ciyarwa da kwanciya daga gareka ba, amma da sharaɗin cewa baka da haƙƙi a kaina.[18] a mahangar Makarim Shirazi ta hanyar sharaɗin aiki mace na iya yafe hatta haƙƙin gado.[19]

Ana cewa Sayyid Ali Sistani da Husaini Ali Muntazari daga maraji'an shi'a sun bada fatawar halascin auren misyar.[20]

Cikin mufti ahlus-sunna, akwai ra'ayoyi guda uku dangane da hukuncin auren misyar: malamai da suka bada fatawar halasci, malamai da suka haramta da malamai da ba su bayyanar da matsayar su ba game da hukuncin wannan aure.[21] masu goyan bayan misyar sun yi Imani cewa wannan aure yana da sharuɗɗa da rukunan auren da'imi da muhimman maslahohinsa.[22]

A cewar Makarim shirazi da yawa yawan malaman fiƙihu na ahlus-sunna misalin Ibn Baz babban mufti na saudiyya, ƙardawi da Nasar Farid Wasil daga mufti misra sun halasta auren misyar; sai dai kuma Jadul Al-haƙƙi, tsohon shugaban jami'ar Al-azhar sun nuna rashin amincewarsu kan wannan nau'in aure.[23] Abdullahi Mani'u, memba cikin majalisar manyan malaman saudiyya,[24] da kuma Darul Al-ifta na Misra da yake ƙarƙashin jami'ar al-azhar sun tafi kan ingancin auren misyar.[25]

Bayanin Kula

  1. «نکاح مسیار جایز است»، سایت دار الافتاء مرکزی اهل سنت؛ مکارم شیرازی، کتاب النکاح، ۱۴۲۴ق، ج۵، ص۲۱؛ ایوبی، نصیری و تولایی، «ارزیابی تطبیقی مشروعیت نکاح مسیار در فقه اهل سنت و مذهب امامیه»، ص۲۶، حاتمی و شنیور، «نکاح‌های نوین معاصر و مشروعیت آن‌ها»، ص۵۰.
  2. ↑ Qaradawi, "Houle Zawaj al-Masyar", shafi na 6
  3. «عضو بکبار العلماء السعودیة یجیز زواج المسیار و یثیر جدلا»، سایت عربی21.
  4. Sadiqi, “Ahle Tasanunnun wa Izdiwaje Misyar,” shafi na 49
  5. Sadiqi, “Ahle Tasanunnun wa Izdiwaje Misyar,” shafi na 65
  6. Qaradawi, "Houle Zawaj al-Masyar", shafi na 7
  7. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 21.
  8. Sadiqi, “Ahle Tasanunnun wa Izdiwaje Misyar,” shafi na 54
  9. Qaradawi, "Houle Zawaj al-Masyar", shafi na 15.
  10. Ameri, "Mut'a wa Mesyar Dar Fikihi Mu'asir", shafi na 680.
  11. Sadiqi, “Ahle Tasanunnun wa Izdiwaje Misyar,” shafi na 51.
  12. Khalifa Faraj Al-A’ib, “Misyar Ziwaje Al-misyar bainal Al-ibahati wal Al-tahrim,” shafi na 320.
  13. Sadiqi, “Ahle Tasannun w izdiwaje Misyar,” shafi na 51.
  14. Khalifa Faraj Al-A’ib, “Ziwaje Misyar Baibal Al-ibahati wal Al-tahrim,” shafi na 320-321.
  15. Misali, duba: Ameri, "Mut'ah wa Mesyar dar fikhi muasir", shafi na 683; Sadeghi, “Auren Ahlul Tasan da Mesyar”, shafi na 66.
  16. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 20, 21-22.
  17. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 22.
  18. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 23.
  19. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 24.
  20. Hatami da Sheniour, “Nikahaha Newen Muasir wa Mashru'iyat anha,” shafi na 56.
  21. «اهل تسنن و ازدواج مسیار»، پژوهشگاه علوم انسانی و مطالعات فرهنگی.
  22. Amiri, "Mut'ah wa Mesyar dar fikh muasir", shafi na 681-682, Qaradawi, "Houle Zawaj al-Misyar", shafi na 6
  23. Makarem Shirazi, Kitab al-Nikah, 1424 AH, juzu'i na 5, shafi na 21-22.
  24. «عضو بکبار العلماء السعودیة یجیز زواج المسیار و یثیر جدلا»، سایت عربی21.
  25. «ازدواج مخفی برای اهل سنت مجاز شد»، سایت تابناک.

Nassoshi

  • «ازدواج مخفی برای اهل سنت مجاز شد»، وبگاه تابناک، تاریخ درج مطلب: ۴ آبان ۱۳۸۶ش، تاریخ بازدید: ۱۵ مرداد ۱۴۰۳ق.
  • Ayoubi, Hussein da Dijran, “ Erziyabi Tadbiki Mashru'iyyat Nikahe Misyar dar Fiqh Ahlus-Sunnah wa dar fikh Imamiyya,” a cikin ‘Journal of Islamic Jurisprudence and Law Studies, Shamara 5, Bayez and Zamistan, 1390.
  • Hatami, Ali Asghar da Qadir Shanyur, “Nikah hay nawiyin maasir wa shar’iyyat anha,” a cikin Journal of Islamic Jurisprudence and Rights Studies, Shamarah 3, Zamistan 1389 AH.
  • Khalifa Faraj Al-A’ib, Abu Al-Qasim, “Zawaje Misyar bainal Al-ibahati wal Al-tahrim,” a cikin Jarida ta Kimiyyar Shari’a da Sharia, Danish Zawiya - Libya, Shamarah 7, 2015 AD.
  • Sadiqi, Muhammad, “Ahle Tasanunn wa Zuwaj Misyar,” a cikin littafin karatun Rahbardi Zanan, Shamarah 40, Tabistan 1387 Hijira.
  • Ameri, Suhaila, “Mat’ah wa Misyar dar fikih Muasir” a cikin tarin kasidu na taron Dovazdahmin tsakanin malaman addini na Iran da ilimin dan Adam, 1402H.
  • «عضو بکبار العلماء السعودیة یجیز زواج المسیار و یثیر جدلا»، سایت عربی21، تاریخ درج مطلب: ۱۹ فوریه ۲۰۰۹، تاریخ بازدید: ۱۳ مرداد ۱۴۰۳ش.
  • Qaradawi, Yusuf, Haule Ziwaje Misyar,” ra’ayinsa da aka gabatar a gefen majalisar shari’ar Musulunci, zama na 18, Makkah, 1427H/2006 Miladiyya.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Kitabul Al-Nikahi edita: Muhammad Reza Hamidi da Masud Makarem, Qum, Wallafar Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), babi na farko, 1424 BC.
  • «نکاح مسیار جایز است»، سایت دار الافتاء مرکزی اهل سنت، تاریخ درج مطلب: ۱۰ مرداد ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید: ۱۳ مرداد ۱۴۰۳ش.