Jump to content

Allahumma Il’an Ƙatalata Amirul Muminin

Daga wikishia

Allahumma Il'an ƙatalata Amiril Muminin (Larabci:اللهم العَنْ قَتَلَةَ امیرالمؤمنین) (ma'ana Allah ka yi la'ana kan makasan Sarkin muminai) wata jumla ce da ta zo cikin ba'arin ziyarorin Imam Ali (A.S),[1] Shaik Abbas Ƙummi maimaita wannan jumla ƙafa 100 yana daga ayyukan daren 19 ga watan Ramadan, (lailatul Ƙadri).[2]

A cewar Ayatullahi Khamna'i jam'i sigar ƙatilan (Makasa) tana ishara zuwa ga ƙari kan makashinsa Ibn Muljam wanda ya zare takobi ya sari Hazrat (A.S) haƙiƙa ta haɗo da duk wani mutum da ya bada gudummawa kan kisansa, daga jumlarsu akwai waɗanda suka taka rawa cikin waƙi'ar tahkim a lokacin yaƙin Siffin, waɗanda suka tilatsa Imam Ali (A.S) kan karɓar tahkim dama duk wanda suka zama sababin shahadantar da shi,[3] Muhsin Ƙara'ati malamin tafsiri na shi'a shima ya bayyana cewa kalmar ƙatalata (Makasa) tana ishara kan gungun mutane da suke kasance kan tunani hallaka Imam Ali (A.S) waɗanda suka yi amfani da Ibn Muljam domin zartar da wannan babban ta'addanci.[4] Wani karon kuma ana amfani da wannan jumla hatta kan mutane da suka ji daɗi da kashe Imam Ali (A.S).[5]

Kan asasin amsar tambayoyin fatawa daga Mirza Jawadi Tabrizi ya ce: babu matsala a karanta wannan addu'a cikin alƙunutu da cikin sujjadar sallah.[6]

Bayanin kula

  1. Ibn Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, juzu'i na 1, shafi na 44
  2. Qomi, Koliat Mofatih al-Jannan, 2004, Aamal Maksus Shabhaye Kadri.shafi na 366.
  3. بیانات در خطبه‌های نماز جمعه تهران. ۲۱ مهر ۱۳۸۵ش.
  4. «شب قدر»، Cibiyar Al'adun Darussan Alqur'ani.
  5. «ثبت همه اعمال انسان در دنیا»،Cibiyar Al'adun Darussan Alqur'ani.
  6. Tabrizi, Taaliqat bar Siratin Najat, 1433 AH, juzu'i. 2, ku. 609.

Nassoshi