Alamul Amru

Daga wikishia
(an turo daga Alamul Amri)

Alamul Amru (arabic: عالم الأمر) ko Alamul Mujarradat, wata duniya ce da ba a iya riskarta da Mariskai biyar (Ji, Gani, Dandano, tabawa, Shaka) kishiya ga Alamul Khalk wacce ake iya riskarta da Mariskai guda biyar, Malamai su na ganin tushen Imani da samuwar Alamul Amru ya samo Asali ne daga gabar wannan aya ta 54 cikin Suratul A'araf:

Kitab al-Awalim Al-Ghaibiyyah fi Kur'an Al-Karim, Ayatullah Subhani ya rubuta
«أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ»

Tabbatuwar Halittu a Alamul Amru take kai tsaye yake faruwa ba tare da bukatuwar samar da sharuddan Makan da zaman ba, sabanin Alamul Khalk wacce tabbatuwar abubuwa na faruwa ne sannu-sannu kuma ya dogara da kebantattun sharudda na Zahiri. Tare da Imani ba'arin wasu Malaman Falsafa kan samuwar Alamul Amru sai dai cewa kuma akwai wasu adadin Malaman Tafsiri suna ganin ayar Alkur'ani da ta zo da Kalmar Amru ta zo domin ishara zuwa ga Alamul Mada bawai Alamul Amru ba, Allama Tabataba'i cikin karshen aya ta 54 daga Suratul A'araf kalmomin Khalk da Amru da aka ambata cikin Surar yana ganin basa bada ma'anar samuwar wata duniya mai cin gashin kanta, bari dai ma'anarsu shi ne Kudurar Halitta Allah da umarninsa.

Sanin Mafhumi

Alamul Amru, wata duniya ce kishiyar Alamul Khalk, hakika ta daga abubuwa na zahiri kuma ba a riskarta da Mariskai guda biyar [1]Mulla Sadra Masanin Falsafa a karni na goma sha daya h kamari, ya ce: hakika Allah ya halicci duniyoyi masu yawa sannan ya tattare baki dayansu cikin duniya guda biyu: Alamul Khalk da Alamul Amru, Alamul Khalk ita ce dai wannan duniya da muke raye cikinta, sannan Alamul Amru wata duniya ce ta halittu Mujarradai (halittu marasa gangar jiki) ana iya riskar wannan duniya kadai ta hanyar Mariskan Badini. [2] A akidar Mulla Hadi Sabzawari, Arifai sun ciro Isdilahin Alamul Amru [3] daga aya 54 cikin Suratul A'araf [4]cikin littafin Hujjatul At-Tafasir a karshen aya ta 85 cikin Suratul Isra'i an yi Magana dangane da duniyoyi guda biyu Alamul Khakl da Alamul Amru kuma kan asasinta ne gangar jikin Mutum ya kasance Samfuri daga Alamul Khalk da Ruhu, kuma shi Misali da Samfuri ne na Alamul Amru [5]

Hususiyoyi

A cewar Nasir Mukarim Shirazi, ita Alamul Amru sabanin Alamul Khalk ce wacce afkuwar abubuwa yake kasancewa da sannu-sannu, a Alamul Amru kai tsaye take halittu suke samuwa [6] Malamin ya dogara ne da aya ta 82 cikin Suratul Yasin kuma kan asasin wannan aya ne duk sanda Allah ya nufi yin wani abu ya bashi umarni kai tsaye take zai kasance [7] Cikin Alamul Amru halittu da zarar Allah ya yi Irada kansu take suke kasancewa ba tare da samar da sharudda na mada misalin Zamani da Bigire, sabanin Alamul Khalk da kafin samar da wani abu dole a samu cikar kebantattun Sharuddansa na Mada [8]

Mahanga

Wasu ba'arin Malaman Falsafa Musulmai sun yi Magana kan samuwar Alamul Amru kishiya ga Alamul Khalk [9] Faizul Kashani a cikin littafinsa As-Safi fi tafsir, jumlar

لَهُ الْخَلْقُ وَ الْأَمْرُ»،

[10]

Tana bayani ne kan bambance-bambance da yake tsakanin Alamul Khalk da Alamul Amru, [11] Faizlul Kashani cikin Tafsirin Suratul Falak daga ayar (Min Sharri Ma Khalak) ya bayyana cewa anyi amfani da ita kan cewa dukkanin sharri yana cikin Alamul Khakl, haka dukkanin alheri yana tare da Alamul Amru [12] tare da haka kamar yanda ya zo cikin Tafsir Namuneh, Alkur'ani ya yi amfani da Kalmar Amru kan Alamul Mada, alal misali cikin aya ta 54 daga Suratul A'araf wadda ita babbar Madogarar Alamul Khalk, Rana da Wata da Taurari suna karkashin Umarnin Ubangiji, [13] Allama Tabataba'I shima cikin Tafsirin Almizan kan wannan aya a 54 bai yi Magana kan samuwar wannan duniya, kadai dai ya yi bayani ne kan bambance-bambance da yake tsakanin halittun Allah da Amru ma'ana umarnin Ubangiji. [14]Alkur'ani mai

Bayanin kula

  1. Balaghi, Hajjat ​​al-Tafaseer, 1386 AH, juzu'i na 4, shafi na 84.
  2. Kalantari, “Cisti Alaml Amri dar ayar Alqur’an Al-Kareem”, shafi na 150.
  3. أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ؛ آگاه باش که [عالم‌] خلق و امر از آن اوست (ترجمه فولادوند).
  4. Ansari Shirazi, Darus Sharh Manzumeh, 2007, juzu’i na 2, shafi na 335.
  5. Balaghi, Hajjat ​​Al-Tafaseer, 1386 AH, juzu'i na 4, shafi na 84.
  6. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 6, shafi na 207.
  7. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 6, shafi na 207.
  8. Beheshti, "Wani Ta'ammuli bar Alame Khalk wa Alame Amr", shafi na 17.
  9. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 6, shafi na 207.
  10. Suratul A'araf, aya ta 54.
  11. Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 205.
  12. Al-Faiz al-Kashani, al-Tafsir al-Safi, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 395.
  13. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 6, shafi na 207.
  14. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, Mujalladi na 8, shafi na 153-150.

Nassoshi

  • Alkur'ani girma, wanda Mohammad Mahdi Fouladvand ya fassara.
  • Ansari Shirazi, Yahya, Darus Sharh Manzumeh Hakim Muta'allihi Haj Molahadi Sabzevari, Juzu'i na 2, Qom, Cibiyar Kitab ta Bostan, 2007.
  • Balaghi, Seyed Abd al-Hujjat, Hajja al-Tafaseer da Balag al-Axir, Kum, Hekmat Publications, 1386 AH.
  • Beheshti, Seyyed Mohammad, "Ta'ammuli bar Alame Khalk wa Alame Amr", a cikin Mujallar Golestan Kur'an, shafi na 88, Nuwamba 2008.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
  • Faiz Kashani, Mulla Mohsen, Tafsir Al-Safi, Tehran, Sadr Publications, 1416 AH.
  • Kalantari, Ebrahim da Hamra Alavi, "Cisti Alame Amri dar ayat Kur'an Kareem", a cikin Mujallar binciken Kur'ani da Hadisi, juzu'i na 1, bazara da bazara 2013.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Nashon, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374.