Ƴan Shi'a Ku Tuna Da Ni Duk Sanda Za Ku Sha Ruwa

Daga wikishia
Karatun wakar "Shiati ma an sharbatam" a cikin littafin Sayyid Mohammad Zahedi.

Ƴan Shi’ata ku tuna da ni duk sanda za ku sha ruwa, (Larabciشیعَتي ما إِن شَرِبتم ماءَ عَذبٍ فاذکروني)wani sanannen baitin waƙa ne da ake danganta shi ga Imam Husaini (A.S) wannan baitin waƙa tunatarwa ne kan yanda Imam Husaini (A.S) ya yi shahada cikin ƙishirwa ba tare da samun ruwan da zai sha ba a lokacin waƙi’ar Karbala, wannan baitin waƙa yana wasicci ga ƴan Shi’a duk sanda za su sha ruwa su tuna da Imam Husaini (A.S)[1] wasu ba’arin Malaman Shi’a tare da dogara da wannan waƙa da kuma adadin wasu riwayoyi daga Ma’sumai, suna ganin wajabcin tunawa da Imam Husaini (A.S).[2] lokacin shan ruwa, wasu kuma suna ganin mustahabbancin hakan.[3]

شِیعَتِی مَا إِنْ شَرِبْتُمْ ماءَ عَذْبٍ فَاذْکرُونِی [4] أَوْ سَمِعْتُمْ بِغَرِیبٍ أَوْ شَهِیدٍ فَانْدُبُونِی

ƴan shi’aya duk sanda zaku sha ruwa ku tuna da ni* duk lokacin da kuka ji labarin baƙo ko wani shahidi ku yi kuka saboda ni.[5]

Hoton rubutun Hoz Anbar Rajab Khorasan

A cewar Fadil Darebandi cikin l;ittafin Asrarul Ash-shahada, haƙiƙa wannan waƙa ce ta Imam Husaini (A.S).[6] wasu ba’arin masadir sun bayyana cewa Sukaina ƴar Imam Husaini (A.S) ce ta rera wannan waƙa bayan shahadarsa lokacin da ta ga Jana’izarsa,[7] Kaf’ami Malamin Shi’a a ƙarni na tara h ƙamari, cikin naƙali daga Sukaina ya bada rahoton cewa bayan shahadar Imam Husaini (A.S) lokacin da Sukaina ta ga gawarsa sai ta rungumeshi cikin halin baƙin ciki da shiɗewa sai ya miƙo min hannunsa a wannan hali ne na ji babana yana rera wannan baitin waƙa.[8] amma tare da haka wasu Malamai misalin Shaik Abbas ƙummi cikin littafin Nafasul Al-Mahmum da Muntahal Al-Amal [9] da Muƙram cikin Maƙtalu Al-Husaini.[10] cikin naƙalto wannan waƙa a litattafansu ba su kawo sanadinta ba ko wani tushe na tarihi, Sayyid Muhammad Sadar wanda ya rasu a shekarar 1377 h shamsi, tare da jingina da abin da waƙar ta ƙunsa da take bayanin yanayin yanda Imam Husaini (A.S) ya yi shahada da kuma abubuwan da suka biyo baya, ya ce tabbas wannan waƙa ba Imam Husaini (A.S).[11] ya yi ta ba,[12] shi da wasu ba’ari sun bijiro da tsammanin cewa wannan waƙa tana hakaito halin da Imam Husaini (A.S) ya kasance ciki. Wannan waƙa, musamman gaɓar farko, an rubutata a kofar magudanun ruwa da maɓuɓɓugar ruwa, da jikin Salka da sauransu.[13] wasu ba’arin mawaƙan Shi’a misalin Mulla Basim Karbala’i da Mahmud Karimi sun kasance suna rera wannan baitin a waƙa cikin waƙoƙin juyayin Shahadar Ahlul-baiti.[14] Cikin ba’arin litattafai an kawo rahotan wannan baituka

«شیعتی مهما شَربتُم عَذْبَ ماءٍ»

ko

«شیعتی ما ان شِربتُم رَیَّ عَذْبٍ...»

Ko kuma gaɓa ta biyu

«او سَمِعتُم بشهیدٍ أو قَتیلٍ»

Ko kuma

»

‌«أو سَمعتُم بقتیلٍ أو جریحٍ

Dukkanin baitukan suna da ma’ana masu kusanci da juna.[15] cikin ba’arin rahotannin an kawo wasu baitukan waƙoƙi da aka danganta su ga asalin wannan waƙa baituka ne guda biyar,[16] Shaik Abbas ƙummi ya yi imani kan cewa sauran baitukan sun kasance baitukan da mawaƙa suka ƙara su kan asalin waƙar, kuma akwai matsala cikin danganta su zuwa ga Imam Husaini (A.S).[17] cigaban baitukan ya kasance cikin sharhin da zai zo a ƙasa:[18]

وَ أَنا السِّبْطُ الَّذي مِنْ غَیرِ جُرْمٍ قَتَلُوني وَ بِجُرْد الخَیلِ بَعْدَ القَتْلِ عَمْداً سَحِقُوني

لَیتَکُم فی یوْمِ عاشُوراء جمیعاً تَنْظُروني کَیفَ أَسْتَسْقي لِطِفْلي فَأبَوْا أَن یرْحَمُوني و سَقَوهُ سَهْمَ بَغْي عِوَضَ الماءِ المَعینِ یا لَرُزْءٍ وَمُصابٍ هَدَّ أرْکانَ الحَجِونِ

وَیلَهُم قَدْ جَرَحُوا قَلْبَ رَسُولِ الثَّقَلَینِ فَالْعَنُوهُم مَا اسْتَطَعْتُم شِیعَتِي فِی کُلِّ حِینٍ

Ni jikan Manzon Allah ne wanda suka kashe ni ba tare da laifin komai ba. Bayan kashe ni suka Tattake jikina da Kofatan Dawakai. Inama ace kun kasance a ranar Ashura ku kallane. Yaya na roƙe su ruwa saboda ƙaramin ɗana amma sai suka ƙi tausaya mini. Suka shayar da shi ruwan kibbai maimakon ruwan sha. Kaicon wannan Musiba da bala’i wacce sai da ta girgiza Dutsen Makka. Kaiconsu tabbas sun jiwa zuciyar Manzon Mutane da Aljanu. Yan shi’ata ku tsinewa waɗannan mutane gwargwadon iyawarku a kowanne lokaci.[19]

Bayanin kula

  1. Shoushtari, Al-Khasa'is Al-Husainiyya, 1414 AH, shafi na 116 da 184.
  2. Haeri, Ma'ali al-Sabatin, 2009, shafi na 452.
  3. Muhaddith Nouri, Mustadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i na 17, shafi na 26.
  4. Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 741.
  5. Rabbani Khalkhali, Simaye Darakshan Hussaini bn Ali (A.S), 2005, shafi na 8.
  6. Fazel Darbandi, Eksir ibadat, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 257.
  7. Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 741.
  8. Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 741.
  9. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 3, shafi.787; Qomi, Nafs al-Mahmum, 1379, juzu'i na 1, shafi na 344.
  10. Muqram, Maktal al-Hussein, 1426H, shafi na 322.
  11. Sadr, Azwa ala sauratil al-Hussain, 1430H, Mujalladi na 1, shafi na 145.
  12. Sadr, Azwa ala sauratil al-Hussain, 1430H, Mujalladi na 1, shafi na 145.
  13. Anani, Mohammadian, Sharif Kazemi, "Simaye Waqfname dar Sarayan dar Khurasan Junubi", shafi na 152-153.
  14. Karbalai, Madddahi y"Shiati Mehma Sharbatam"; Karimi, "Shiati Mehma Sherbatam Ma Azaz Fazkhroni" yabo.
  15. Misali, duba: Tabrizi, al-Shaa’er al-Husainiyya, 1433H, shafi na 380; Sadr, Azwa ala Ali Thorat al-Hussein,(A.S), 1430 AH, juzu'i na 1, shafi na 145; Madrasi, Imtidad Harkate Anbiya, 1407H, shafi na 131.
  16. Jam'i az Nawisendigan, Maus'atu shahadat Al-Masoomin,(A.S) 1380, juzu'i na 2, shafi na 325.
  17. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 3, shafi.787.
  18. Jam'i az Nawisendigan, Maus'atu shahadat Al-Masoomin,(A.S) 1380, juzu'i na 2, shafi na 325.
  19. Rabbani Khalkhali, Simaye Darakshan Hussaini bn Ali (A.S), 2005, shafi na 8.

Nassoshi

  • Anani, Bahram wa Mohammadian, Fakhreddin wa Sharif Kazemi, Khadija, "Simaye Waqfnameh dar Abe Anbarhaye Sarayan dar Khorasan Junubi", dar Waqf Miras Jawidaneh, No. 90, 2014.
  • Haeri Mazandarani, Mahdi, Ma'ali al-Sabatin (mai fassara: Reza Koushari da Yusuf Asadzadeh), Qom, Tehzib, 1389.
  • Jam'i az Nawisandegan, Mausu'atu Shahadat Al-Masoomin, (A.S), Qum, Noor al-Sajjad, 1380.
  • Kafami, Ibrahim bin Ali, Al-Masbah, Dar al-Rezi (Zahidi), 1405H.
  • Madrasi, Mohammad Taqi, Imtidad Harkate Al-Anbiya, Tehran, Maktabat Allama Madrasi, 1407H.
  • Muhaddith Nouri, Hossein, Mostadrak al-Wasail, Qom, Al-Bayt Foundation for Revival of Heritage, Bita.
  • Muqram, Sayyid Abd al-Razzaq, Maktal al-Hussein (a.s.), Beirut, Al-Khursan Publishing House, 1426H.
  • Qomi, Abbas, Mentehi al-Amal, Qum, Dalil, 1379.
  • Qomi, Abbas, Nafs al-Mahmoum fi Masibat Sayyidna al-Hussein al-Mazloum, Qum, al-Maktab al-Haydariyya, 1379.
  • Rabbani Khalkhali, Ali, Simaye Hossein bin Ali (a.s), Qum, Mazhabar Hussaini (a.s), 1385.
  • Sadr, Sayyid Muhammad Baqir, Azwa Ala Thora Al-Hussein (A.S), Iraki, Al-Tarat al-Sayyid al-Shaheed al-Sadr, 1430H.
  • Shirwani al-Hairi, Agha bin Abed (Fazel Darbandi), Eksir Al-Ibadat, Bahrain, Al-Mustafa Company for Culture Services, 1415 AH.
  • Shushtri, Ja'afar bin Hossein, al-Khajasat al-Husainiyyah, Beirut, Darul-Suror, 1414H.
  • Tabrizi, Jafar, al-Shaa'er al-Husainiyya, Qum, Darul Sadiqah, 1433H.
  • Yaqoubi, Muhammad, Fi Sakafat Alrafd wa Islahi Al-Mujtama, Najaf, Dar al-Sadejin, 1435H.
  • کربلایی، باسم، مداحی «شیعتی مهما شربتم»، در موکب شهداء الحشد الشعبی هیئة جواد الائمه العزیزیه عراق، شب شهادت امام علی(ع) ۱۴۲۲ق.
  • کریمی، محمود، مداحی «شیعتی مهما شربتم ماء عذب فاذکرونی»، هیئت رایة العبّاس تهران، شب اول محرم الحرام ۱۳۹۷ش.