Ƙungiyar Khoja Ta Ƴan Shi'a Imamiyya

Daga wikishia

The World Federation of KSIMC(ƘUNGIYAR KHOJA TA ƳAN SHI'A IMAMIYYA(Larabci:الاتحاد العالمي لجماعات شيعة الخوجة الاثني عشرية).[1]

Babbar cibiyar yanke shawara ta Khoja Shi'a imamiyya ta duniya, wacce dukkanin ƙungiyoyin Khoja ke aiki a ƙarƙashinta. Ita ce babbar ƙungiya mai taka rawa wajen daidaita tsakanin ƙungiyoyin Khoja, Wadda cibiyarta take a Landan.

Tarihi

A farkon shekarun 1970 ne aka kafa wannan ƙungiyar ta duniya a birnin London bayan korar 'yan Asiya daga Uganda.[2] A wannan taro an yanke shawarar kafa kwamitin da zai tsara kundin tsarin mulkin wannan ƙungiya. A wani taro da aka gudanar a shekara ta 1980, ƙungiyoyi daban-daban sun amince da kafa ita wannan babbar Ƙungiyar ta Duniya, dan ta fara aiki a hukumance. A cikin wannan shekarar, an yi wa wannan ƙungiya rajista a matsayin ƙungiyar agaji ta addini a Ingila.[3] Shuwagabannin wannan ƙungiya sune malla asgar sai hasanain walji bayan shi sai Hashim jawad.[4]

Ayyukan Wannan ƙungiya

Kula da ƙungiyoyin yanki yanki da sauran Khojah ƴan shi'a a duniya.[5] Yanke hukunce hukuncen da suka shafesu masu muhimmanci kamar marja'in taƙlidi, ba khumusi da zakka da sauransu.[6]

Sanin Haiƙanin Yawan Adadin Khoja A Duniya

ƙungiyar khoja watanni shida kafin taron Ƙungiyar Ƙasa ta Duniya, sun sanar da yawansu, wanda duk bayan shekaru uku, suke sanar da yawan al'ummar Khoja a gurin. Ana ganin wannan ƙididdiga a matsayin tushen jimillar 'yan Shi'a na Khoja[7]


Tsare Tsarensu

Wannan ƙungiyar tana da mambobi 135 waɗanda aka zaɓa daga ƙananan ƙungiyoyi 40 da mutanan khoja guda 26.[8] Hedkwatarta tana Landan.[9] kuma sakatariyarta tana Stanmore Islamic Center na wannan birni.[10] Kamar yanda kundin tsarin mulkin su ya tanada, wannan ƙungiya ce mai zaman kanta wadda ake zabar shugabanta da mambobinta na tsawon shekaru uku a lokacin babban zabe.[11] An tsara manufofin[12] wannan ƙungiya ne a yayin taron kowace shekara uku.[13] Hukunce-hukuncen da suka yanke sun zama dole ga dukkan ƙananan ƙungiyoyin yanki yanki.[14]

Manufofinsu

ƙarfafa mazhabar Shi'a imamiyya. Inganta hanyoyin kawo kuɗi na membobin su. Haɓaka matakin ilimin kimiyya da na addini ga membobin su Ci gaban zamantakewa da taimakon marasa galihu.[15]

Ayyukan Wannan Ƙungiya

Tun bayan kafuwart ƙungiyar duniya ta shirya matakan inganta rayuwar al'ummar Khoja a duniya, musamman a nahiyar Indiya, galibin waɗannan ayyuka a shekarun 1980-1990, a fagen warware matsalolin al'adu, zamantakewa da tattalin arziki. na Khojas a Indiya, musamman a jihar Gujarat kuma shi ne yankin Kutch na Indiya da wasu jihohin Pakistan.[16]

Ƙungiyoyin Yanki Yanki

Wannan ƙungiya tana da ƙungiyoyin yanki yanki a nahiyoyi na Afirka, Amurka, Turai da Asiya da kuma wasu nahiyoyin.[17] sauran ƙungiyoyin sune wakilan babbar ƙunyi kuma suna taka rawa mai yawan gaske.[18]

Ƙungiyar Khoja Ta Ƴan Shi'a Imamiyya A Afrika

Ƙungiyar Shi'a ta Khoja ta africa ƙungiya ce ta 'yan Shi'a ta Gabashin Afirka wadda ta haɗa ƴan asalin Indiya acikinta wacce ke da hedkwatarta a Darus-salaam.[19]

Samar Da Kuɗaɗen Shiga

Babbar hanyar samun kuɗin shiga na ƙungiyoyin shi'ar Khoja , da suka hada da ƙungiyoyin duniya da na shiyya-shiyya da cibiyoyin da ke da alaƙa da su, ana samar da su ne da taimakon 'yan Shi'a Khoja da ke zaune a ƙasashen gabashin Afirka da Arewacin Amurka. Yawancin waɗannan mutane manyan ’yan kasuwa ne kuma a kowace shekara suna bayar da wani ɓangare na ribar da suke samu na hada-hadar kasuwancinsu ga jami’an ƙungiyoyin duniya ko na shiyya-shiyya.[20] Bugu da ƙari, jami’an su sun naimi izinin marja'in su .Ayatullah Sistani, suna bayar da wani bangare na khomusin su na rabon Imam da Sadat, wajan ayyukan da daawa da gine-ginen guraran addini don gudanar da ayyukan ibadu da wa’azi.[21]

Bayanin kula

  1. The World Federation of Khoja Shia Ithna-Asheri Muslim Communities
  2. Jafarian, Atlas Shia, shafi na 556.
  3. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari a duniya, shafi na 244.
  4. Jafarian, Atlas Shia, shafi na 556.
  5. Jafarian, Atlas Shia , shafi na 556-557; Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari a duniya, shafi na 245.
  6. Jafarian, Atlas Shia, shafi na 556-557
  7. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 249.
  8. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 249.
  9. Jafarian, Atlas Shia, shafi na 556-557
  10. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 244.
  11. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 249.
  12. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 244.
  13. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashri a duniya, shafi na 249.
  14. Jafarian, Atlas Shia, shafi na 556-557
  15. Roghani, Shi'ayan Khoja dar Ayineh Tarikh, shafi na 24
  16. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari dar Gustareshe Jahan, shafi na 249.
  17. Daftare Muɗala'at Siyasi wa Bainal Al-Milali, Tanzaniya, shafi na 21.
  18. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari dar Gustasreh Jahan, shafi na 245.
  19. Daftare Muɗala'at Siyasi wa Bainal Al-Milali, Tanzaniya, shafi na 21.
  20. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari Gustareh Jahan, shafi na 93
  21. Arab-Ahmadi, Shi'a Khoja Esna Ashari Gustareh Jahan, shafi na 93

Nassoshi

  • Amini, Rahim, Tanzaniya, Daftare Muɗala'at Siyasi wa bainal milali wezarat umuri kharijeh, Tehran, 1375.
  • Arab-Ahmadi, Amir Bahram, Khoja Esna Ashari Gustareh, ƙom, 2009.
  • Jafarian, Rasul, Atlas Shia, Tehran, 2011.
  • Roghani, Zahra, Shi'ayan Khoja dar Ayineh Tarikh, Tehran, 2007.