Zagin Ali: Bambanci tsakin sauye-sauye na
Layi 19: | Layi 19: | ||
==== Marwan Bn Hakam ==== | ==== Marwan Bn Hakam ==== | ||
Kan asasin abinda Zahabi Malamin tarihi ya nakalto a littafinsa hakika Marwan a shekara 41 h Kamari ya zama Gwamnan Madina ya kasance tsawon shekaru shida a matsayin Gwamna, a kowacce Ranar Juma’a yana hawa Mimbari ya zagi Imam Ali (A.S) bayan Marwan, Sa’id Bn Asi yayi Gwamna shekaru biyu sai dai cewa shi bai kasance yana zagin Imam Ali (A.S) ba, bayan Sa’id Bn Asi Marwan Bn Hakam ya Kara zama Gwamnan Madina ya cigaba mummunar al’adarsa ta zagin Ali (A.S), <ref>Dhahabi, Tarikh Islam, 1409 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 231.</ref> | Kan asasin abinda Zahabi Malamin tarihi ya nakalto a littafinsa hakika [[Marwan Bn Hakam]] a shekara 41 h Kamari ya zama Gwamnan Madina ya kasance tsawon shekaru shida a matsayin Gwamna, a kowacce Ranar Juma’a yana hawa Mimbari ya zagi Imam Ali (A.S) bayan Marwan, [[Sa’id Bn Asi]] yayi Gwamna shekaru biyu sai dai cewa shi bai kasance yana zagin Imam Ali (A.S) ba, bayan Sa’id Bn Asi Marwan Bn Hakam ya Kara zama Gwamnan Madina ya cigaba mummunar al’adarsa ta zagin Ali (A.S), <ref>Dhahabi, Tarikh Islam, 1409 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 231.</ref> | ||
==== Mugira Bn Shu’uba ==== | ==== Mugira Bn Shu’uba ==== |
Zubi na 13:15, 25 Oktoba 2023
Zagin Ali, furta miyagun Kalmomi tare da La’antar Imam Ali (A.S) da Mu’awiya Bn Abi Sufyan ya Assasa ya sunnanta shi, hakika Sarakunan Banu Umayyawa da Mabiyansu sun kasance suna Zagin Imam Ali (A.S) a Mimbarorin Hukuma, wannan mummunan aiki ya yadu ya kuma ja lokaci har kusan shekaru 60 ba a den aba sai lokacin Mulkin Umar Bn Abdul-Aziz da ya zo ya hana, tare da haka Imam Ali (A.S) bai Lamuncewa Mabiyansa Zagin Mu’awiya ba. Mu’awiya, Marwan Bn Hakam, Mugira Bn Shu’uba da Hajjaju Bn Yusuf Sakafi suna cikin Jumlar Sarakunan Banu Umayya da suke zagin Hazrat Ali (A.S) a kan Mimbari, an yi Ukuba kan Adiyyatu Bn Sa’ad sakamakon kin yarda ya zagi Imam Ali (A.S). Wasu ba’arin Malaman `Yan Shi’a suna ganin Zagi da La’antar Imam Ali (A.S) matsayin Misdakan Nasibanci.
Sanin Mafhumi
Kuna iya duba Makala Mai taken: La’ana Zagi yana nufin furta mummunar Kalma kan wani Mutum [1] Ibn Asir yace: mutane suna ganin (La’ana) ba ta da banbanci da Zagi `yan’uwan juna ne a ma’ana [2] wasu Ba’ari suma suna ganin La’ana tana daukar ma’anar Zagi ko kuma kora da nesantarwa [3] wasu kuma suna ganin akwai banbanci tsakanin ma’anar Zagi da La’ana, sun fassara Zagi da Ma’anar Muguwar Magana, La’ana kuma nesantarwa daga Rahamar Allah [4] Imam Bakir (A.S) ya nakalto daga Imam Sajjad (A.S) cewa ya Ya saki daya daga cikin Matansa sakamakon ta zagi Imam Ali (A.S) [5] wasu ba’arin Malaman sun fitar da hukunci daga wannan riwaya cewa zagin Ali Bn ABi Talib (A.S) Misdaki ne na Nasibanci, [6] Jafar Subhani yana ganin Assasa Zagin Ali Bn Abi Talib (A.S) da Mu’awiya yayi shine tushen farkon fara yaduwar Nasibanci tsakankanin Musulmai, [7] Malaman Fikihu na Shi’a suna Ganin Halascin Jinin Mutumin da ya zagi Ali (A.S) [8]
Takaitaccen Tarihi
Fara Zagi da La’anar Imam (A.S0 dag banu Umayya ya faro ne daga tun lokacin rayuwarsa, ta yanda ya kasance daya daga cikin sharuddan da Imam Hassan (A.S) ya gindaya a lokacin Sulhu da Mu’awiya akwai hana zagin Ali Bn Abi Talib a kan Mimbari, [9] cikin abubuwa da Banu Umayya suka na nuna kiyayya ga Hazrat Ali (A.S) akwai hana Nakalto duk wata Falala tasa, hana rwaiatar Hadisi daga gare shi [10] Bayan Kashe Usman Bn Affan Mabiyansa sun fake da tuhumar Imam Ali (A.S) da hannun cikin kashe shi don kada su yi ma Imam Mubaya’a, cikin Yunkurin Mu’awiya na rura wutar fitina tsakanin Musulmi sai ya bada umarni zagi da la’antar Imam Ali (A.S) [11] Marwan ya gayawa Imam Sajjad (A.S) cewa a lokacin da aka kewaye Gidan Usman babu wani mutum da ya bashi kariya kamar Ali (A.S), sai Imam yace: to me yasa kuke zaginsa a kan Mimbari? Sai Marwan ya bashi amsa da: Asasin Gwamnatinmu ba zai karfafu sai mun zage shi, [12] a cewar Zamakshari hakika a zamanin Banu Umayya an assasa Mimbari dubu saba’in don Raya Sunnar Mu’awiya ta zagin Imam (A.S) da La’antarsa [13] Zagin Imam ya dauki tsawon lokaci ana yinsa kusan shekaru Sittin har zuwa zamanin Halifancin Umar bn Abdul-Aziz wanda ya yi Mulki tsakanin shekaru 99-101 bayan karbi ragamar Halifanci ya aika da Sako ga baki dayan Gwamnoninsa yana umartarsu su dena zagi da La’anar Imam Ali (A.S). Ibn Khaldun Malamin Tarihi a karni na Takwas h kamari ya nakalto cewa Banu Umayya sun kasance suna La’antar duk wani mutum da yake da dangantaka da Imam Ali (A.S) har zuwa zamanin Halifancin Umar Bn Abdul-Aziz da ya aika da Wasika zuwa kowanne gari da yanki yana Umartarsu da a dagata da wannan mummunar Sunna ta Mu’awiya [14] kan asasin wata riwaya daga Ummu Salama da ta nakalto daga Annabi (S.A.W) yana cewa: Zagin Imam Ali (A.S) kamar zagina ne, wani lafazin ya zo cewa zaginsa daidai yake da zagin Allah [yadash 1] [15] Allama Majlisi a cikin Bihar-Anwar kari kan riwayar da aka dangantata ga Ummu Salama akwai wata riwaya da ya nakalto a wannan babi [16]
Mu’awiya
An bada rahoto kan wurare da Mu’awiya ya kasance yana zagi da La’antar Imam Ali (A.S), Ibn Abdu Rabbihi wanda ya mutu a shekara ta 328 h Kamari Malamin Tarihi na Ahlus-Sunna ya nakalto cewa Mu’awiya ya La’anci Imam Ali (A.S) a kan Mimbari, [17] Tabari Malamin Tarihi a Karni na hudu h Kamari ya nakalto cewa a shekara ta 41 h Kamari lokacin da Mu’awiya ya nada Mugira Bn Shu’uba matsayin Gwamnan Kufa ya umarce shi da Zagi da La’antar Imam Ali (A.S) a kan Mimbari da kuma matsawa cikin Girmama Usman Bn Affan [18] haka kuma yayi masa wasiyya da ya nesantar da Sahabbai da Mataimakan Hazrat Ali (A.S) [19] Bayan Mu’awiya ya yi Sulhu tare da Imam Hassan (A.S) ya karbi Mubaya’ar Mutane a Nakaliyya sannan cikin Hudubarsa ya zagi Imam Ali (A.S) da Imam Hassan (A.S) [20]
Marwan Bn Hakam
Kan asasin abinda Zahabi Malamin tarihi ya nakalto a littafinsa hakika Marwan Bn Hakam a shekara 41 h Kamari ya zama Gwamnan Madina ya kasance tsawon shekaru shida a matsayin Gwamna, a kowacce Ranar Juma’a yana hawa Mimbari ya zagi Imam Ali (A.S) bayan Marwan, Sa’id Bn Asi yayi Gwamna shekaru biyu sai dai cewa shi bai kasance yana zagin Imam Ali (A.S) ba, bayan Sa’id Bn Asi Marwan Bn Hakam ya Kara zama Gwamnan Madina ya cigaba mummunar al’adarsa ta zagin Ali (A.S), [21]
Mugira Bn Shu’uba
Balazari Malamin tarihi a karni na uku h Kamari, Mugira Bn Shu’uba wanda Mu’awiya ya nada shi Gwamnan Kufa tsawon shekaru tara yana Gwamna Hakika Mu’awiya san zai kasance cikin cigaba kan zagin Ali Bn Abi Talib da fadar miyagun kalmomi kansa [22]
Hajjaju bn Yusuf
Kan asasin abinda Ibn Abli Al-Hadid ya ambata cikin sharhin Nahjul Balaga, hakika Hajjaju Bn Yusuf kari kan La’antar Imam Ali (A.S) ya kasance yana umartar mutane da wannan kazamin aiki kuma yana farin ciki da jin dadi da hakan [23] wata rana wani Mutum ya zo wurin Hajjaju Bn Yusuf yana kawo masa kuka cewa Mahaifansa sun zalunce shi da suka sanya masa suna Ali, do Allah ka sauya min suna, sannan ka dan bani wani abu da zan rayu da shi, saboda ni Fakiri ne bani da komai, sai Hajjaju y ace masa na gode da wannan dabara da ka zo da ita, na sauya maka suna zuwa Wane, kuma na fawwala aiki kaza zuwa hannunka [24] A wasu riwayoyin, Hajjaju Bn Yusuf yana ganin zagin Ali matsayi wata karfaffar Falala ce, [25] ya zo cikin bayanin halin Adiyya Bn Sa’ad Bn Hannada Kufi cewa Hajjaju ya nemi da ya La’anci Ali Bn Abi Talib idan kuma yaki yi Zai masa Bulala 400, tareda wannan barazana Adiyya yaki yi, Hajjaju ya sa aka masa Bulalla 400 tareda aske gashin Kansa da Gemunsa [26]
Rashin Amincewar Ali kan Zagin Mu’awiya
Duk da cewa Mu’awiya ya bada Umarni a dinga zagin Imam Ali (A.S) a kan Mimbari amma tare da haka a lokacin Yakin Siffin Imam Hali ya tsawatar kan Zagin Mu’awiya, lokacin da Hujru Bn Adi da Umar BN Hamak daga Dakarun Imam (A.S) suka La’anci MU’awiya da Mutanen Sham sai Imam Ali (A.S) tsawatar musu kan wannan aiki ya nuna rashin amincewarsa, [27] lokacin da suka tambaye shi cewa ashe mu ba a kan gaskiya muke ba? Sai ya basu amsa: Eh mana muna kan gaskiya, sai dai cewa ba na son ku kasance masu Zage-zage da Tsinuwa, Imam Ali (A.S) cikin cigaban maganarsa ku nemi Allah yak are jininmu da nasu, ya kuma sulhunta tsakaninmu da su ya shiryar da su daga bata da suke ciki, duk wanda bai san gaskiya ba ya samu damar saninta, duk wanda ya kafe kan karya ya dena ya janye, [28] [yadasht 2]
Bayanin kula
- ↑ Turaihi, Majma Al-Baharaini, 1375, juzu'i na 2, shafi.80.
- ↑ Ibn Athir Jazri, Al-Nehaya, 1367, juzu'i na 4, shafi na 255.
- ↑ Bostani, Farhang Abjadi, 1375, shafi na 756.
- ↑ Fakhlai, Majmu'eh Guftemanhaye Mazahib Islami, 2003, shafi na 299.
- ↑ Tusi, Tahzib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 303.
- ↑ Balqan Abadi, Shawaheed An-nasabi fi Asar Bukhari, shafi na 79.
- ↑ Sobhani, Guzideh Simaye Aqayeed Shia, 2009, shafi na 22.
- ↑ Mughniyeh, Fiqhu Imam Sadik (a.s.), 1421H, juzu'i na 6, shafi na 278.
- ↑ Tabarsi, Elamul Alwara, 1390 AH, shafi na 206
- ↑ Duba: Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Amirul Mominin, 1428 AH, shafi na 475-483.
- ↑ Duba: Jamshidis da wasu Marubuta, “Farfagandaye Bani Umayyawa bar Khandane Payambar (S.A.W)”, shafi na 18-15; Kothari, "Barasi Rishehaye Taraki NasibGeri", shafi na 100-96.
- ↑ Dhahabi, Tarikhul Islam, 1409 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 461.
- ↑ Zamakhshari, Rabi'ul Al-Abrar, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 186.
- ↑ Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 3, shafi na 94.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Bana Al-Aqaqa Al-Fatimiyyah, 1411H, shafi na 212; Ibn Asaker, Tarikh Madina Dimashk, 1417H, juzu'i na 42, shafi na 533.
- ↑ Duba: Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 39, shafi na 311-330.
- ↑ Ibn Abd Rabbah, Al-Eqdul Al-Farid, 1987, juzu'i na 5, shafi na 114.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 253.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 AH, juzu'i na 5, shafi na 253; Dhahabi, Tarikh Islam, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 231;
- ↑ Al-Hosseini Al-Mosavi Al-Hairi Al-Karki, Tasliya Majalis wa Zinatil Majalis, 1418 AH, Juzu'i na 2, shafi na 51-52; Abul Faraj Esfahani, Muqatil Al-Talebein, 1419 AH, shafi na 78.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1409 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 231.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1400 AH/1979 miladiyya, juzu'i na 5, shafi na 243.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 4, shafi na 58.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 4, shafi na 58.
- ↑ Askari, Tarjamati Ma'alimil Al-Madrasataini, 2006, juzu'i na 1, shafi na 415-416.
- ↑ Ibn Saad, Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu'i na 6, shafi na 305.
- ↑ Dinouri, Al-Akhbar al-Tawwal, 1368, shafi na 165.
- ↑ Dinouri, Al-Akhbar al-Tawwal, 1368, shafi na 165.
Nassoshi
- Ibn Athir Jazri, Mubarak bin Muhammad, Al-Nehaya fi Gharib Al-Hadith wal- Al-Athar, scholar, proofreader, Tanahi, Mahmoud Muhammad, Qum, Ismailian Press Institute, 1367.
- Ibn Khaldun, Abd al-Rahman Ibn Muhammad, Diwan al-Mubatada wa al-Khobar fi Tarikh al-Arab va al-Barbar wa Man Aserham Man Dhu al-Shaan al-Akbar (History Ibn Khaldun), Khalil Shahadah ya yi bincike, Beirut, Darul Fikr, bugu na biyu, 1408H.
- Ibn Abd Rabbah, Ahmed Ibn Muhammad, al-Eqdul al-Farid, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1987.
- Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madina Damashk, Juzu'i na 42, Bincike na Ali Shiri, Beirut, Darul Fikr, 1417H/1996 Miladiyya.
- Abul Faraj Esfahani, Ali bin Hossein, Muqatil al-Talbeyin, Beirut, Al-alami printing, 1419 AH/1998 Miladiyya.
- Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Bincike na Ehsan Abbas, Beirut, Jamiat al-Mustareqin al-Almaniyah, 1400 AH/1979 AD.
- Balkhi, Muqatil bin Suleiman, Tafsir Muqatil bin Suleiman, Bincike: Shehate, Abdullah Mahmoud, Beirut, Dar Ihya al-Trath, bugun farko, 1423H.
- Balqanabadi, Hasan, Hujjar Shigarwa Cikin Ayyukan Bukhari, Gabatarwa: Najmuddin Tabasi, Bija, Bita.
- Jamshidiha Gholamreza, Rouhani Mohammad Reza, Alam Al-Hadi Seyyed Abdul Rasool, "Farfagandeye Banu Umayya bar Khandane Payambar (SAW)", a cikin Nazarin Shi'a na Kwata, Shekara ta 7, lamba 35, Kaka 2019.
- Al-Husaini al-Musawi al-Hairi al-Karki, Muhammad bin Abi Talib, Tasliya Majlis wa Zinatil Majalis: Al-Mosom Bumket al-Husayn (a.s), bincike na Fars Hassun Karim, Qum, Pasdar Islam. , 1418 AH.
- Dinouri, Abu Hanifa Ahmad bin Dawud, Al-Akhbar al-Tawwal, Kum, Al-Razi Manshurat, 1368.
- Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarikh al-Islam, bincike: Tadmari, Omar Abd al-Salam, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na biyu, 1409H.
- Zamakhshari, Mahmoud bin Amr, Rabi'ul Al-Abrar da Nasus al-Akhbar, Beirut, Cibiyar Kimiyya, 1412 AH.
- Sobhani, Jafar, Darsenamahe Guzdeh Simaye Akayid Shia, mai fassara: Javad Mohaddasi, Tehran, Mashaar, 2009.
- Sayyed Ibn Tawus, Ahmad Ibn Musa, Bina'i Makalatul Fatimiyya fi Nakadi Risalatil Umsaniyya, wanda Sayyid Ali Al-Adnani Al-Gharaifi ya yi bincike a Qum, Mu’assasa ta Al-Bait for Revival of Tradition, 1411H.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Ealamul Al-Wara tare da tutocin Al-Hadi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na uku, 1390H.
- Tabari, Abu Ja'afar Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Umamu wa al-Muluk (Tabari's history), bincike: Ibrahim, Muhammad Abul Fazl, Beirut, Darul-Tarath, bugu na biyu, 1387H.
- Tarihi, Fakhruddin, Majma Al-Baharin, bincike: Hosseini, Seyyed Ahmad, Tehran, kantin sayar da littattafai na Mortazavi, bugu na uku, 1375.
- Sheikh Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, Mohaghegh, Mousavi Khorsan, Hassan, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islami, bugu na 4, 1407H.
- Askari, Morteza, wanda Maalem al-Madrasteen ya fassara, mai fassara: Mohammad Javad Karmi, Qom, Faculty of Principles of Religion, 2006.
- Allameh Majlesi, Mohammad Bagher, Bihar al-Anwar, juzu'i na 39, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1430 AH/1983 AD.
- Kothari, Ahmad, "Brasi Rishehaye Tariki Nasibgeri", mujallar bincike na sukar Wahhabism; Siraj Munir, shekara ta hudu, lamba 16, hunturu 2013.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Imam Al-Sadiq (a.s.) fikihu, Qum, Cibiyar Ansari, 1421H.