Jump to content

Ayatul Kursiyu: Bambanci tsakin sauye-sauye na

Daga wikishia
Hassan (hira | gudummuwa)
Created page with "'''Ayar Kursiyu''' suratul Bakara:255 (wani adadi ne na Siffofin Jalal da Jamal na Allah da suka hado da siffofin zatin Allah daga jumlarsu akwai Dayantuwa, Rayuwa, Kayyumiyya, Ilimi da Kudura, haka kuma sun hado da siffofin aiki misalin Malllaka kan duniyar samuwa da Ceto, «وَسِعَ کُرسِیُّهُ السَّمواتِ و الارضَ» Kursiyunsa ta Yalwaci Sammai da Kasa. Ana kiranta da ayar Kursiyu ta kuma shahara da wannan suna, wasu ba’ari suna ganin a..."
 
Hassan (hira | gudummuwa)
Layi 7: Layi 7:
== Matani da Tarjama ==  
== Matani da Tarjama ==  
Aya ce ta 255 cikin Suratul Bakara ana kiranta da Ayatul Kursiyu sakamakon zuwan Kalmar Kursiyu ciki 1 ance ana kiran wannan aya da sunan Ayatul Kursiyu tun farkon Muslunci zamanin Annabi Akram (S.A.W) da A’imma (A.S) 2 Matani da tarjamarta shina kamar haka:

اَللَّـهُ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْ‌ضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْ‌سِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْ‌ضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ ﴿٢٥٥﴾ لَا إِكْرَ‌اهَ فِي الدِّينِ ۖ قَد تَّبَيَّنَ الرُّ‌شْدُ مِنَ الْغَيِّ ۚ فَمَن يَكْفُرْ‌ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِن بِاللَّـهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْ‌وَةِ الْوُثْقَىٰ لَا انفِصَامَ لَهَا ۗ وَاللَّـهُ سَمِيعٌ .
<center>
اَللَّـهُ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْ‌ضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْ‌سِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْ‌ضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ ﴿٢٥٥﴾ لَا إِكْرَ‌اهَ فِي الدِّينِ ۖ قَد تَّبَيَّنَ الرُّ‌شْدُ مِنَ الْغَيِّ ۚ فَمَن يَكْفُرْ‌ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِن بِاللَّـهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْ‌وَةِ الْوُثْقَىٰ لَا انفِصَامَ لَهَا ۗ وَاللَّـهُ سَمِيعٌ .</center>
Allah kenan babu abin bauta da gaskiya sai shi, Rayayye Tsayayye, Gyangyadi ko Bacci bai daukarsa, abinda yake Sammai da yae Kasa duka nasa ne, wane ne zai yi ceto sai bayan bada izini daga gareshi? Allah ya san abin yake gabansu da abind ayake bayansu. Basa kewaya da wani abu daga iliminsa sai abin da ya so, Karagarsa ta Mamaye Sammai da Kasa, kula da su bar da wahala a kansa, hakika shi Madaukaki Mai girma.   

________________________________________
________________________________________
آیة الکرسی یا آیات الکرسی
Ayar Kursiyu ko Ayoyin Kursiyu
Ayar Kursiyu ko Ayoyin Kursiyu
Abinda ya shahara a tsakankanin Malaman tafsirin Shi’a shine cewa aya ta 255 cikin Sutaul Bakara itace kadai Ayar Kursiyu 3 sauran ayoyi biyu da suka biyo bayanta bas a cikinta 4 a cewar Sayyid Muhammad Husaini Tahrani, Allama Tabataba’i Marubucin Tafsirul Almizan sun tafi kan cewa Ayar Kursiyu itace aya 255 kadai cikin Suratul Bakara wacce ta gama da jumlar (kuma shi ne Madaukaki Mai girma) 5 Mukarin Shirazi daya daga Malaman tafsirin Shi’a ya kawo shaidu daidai har guda shida kan cewa takaituwar taken Ayar Kursiyu a iya aya ta 255 cikin Suratul Bakara, daga jumlar shaidar kamar:

Zubi na 16:48, 4 Oktoba 2023

Ayar Kursiyu suratul Bakara:255 (wani adadi ne na Siffofin Jalal da Jamal na Allah da suka hado da siffofin zatin Allah daga jumlarsu akwai Dayantuwa, Rayuwa, Kayyumiyya, Ilimi da Kudura, haka kuma sun hado da siffofin aiki misalin Malllaka kan duniyar samuwa da Ceto, «وَسِعَ کُرسِیُّهُ السَّمواتِ و الارضَ» Kursiyunsa ta Yalwaci Sammai da Kasa. Ana kiranta da ayar Kursiyu ta kuma shahara da wannan suna, wasu ba’ari suna ganin ayoyin 256-257 bangare na ayatul Kursiyu, sai dia cewa wasu ba’ari tareda la’akari da riwayoyi da shaidu suna tafi kan cewa ayar ta 255 cikin suratul Bakara ita kadai ce Ayatul Kursiyu. Wannan aya tana da Falala da Hususiyamasu tarin yawan gaske kamar yanda ya zo cikin masadir din riwaya, daga jumlarsu akwai abinda ya zo cikin ba’arin wasu riwayoyi cewa wannan aya itace mafi darajar aya cikin Kur’ani, an wasiyya da karanta wannan aya a kowanne lokaci bayan sallah ne ko kuma bayan Allah, Kafin kwanciya bacci ko lokacin fita daga gida, yayin fuskantar Hatsari da wahala da dai sauransu.

Matani da Tarjama

Aya ce ta 255 cikin Suratul Bakara ana kiranta da Ayatul Kursiyu sakamakon zuwan Kalmar Kursiyu ciki 1 ance ana kiran wannan aya da sunan Ayatul Kursiyu tun farkon Muslunci zamanin Annabi Akram (S.A.W) da A’imma (A.S) 2 Matani da tarjamarta shina kamar haka:

اَللَّـهُ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْ‌ضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْ‌سِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْ‌ضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ ﴿٢٥٥﴾ لَا إِكْرَ‌اهَ فِي الدِّينِ ۖ قَد تَّبَيَّنَ الرُّ‌شْدُ مِنَ الْغَيِّ ۚ فَمَن يَكْفُرْ‌ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِن بِاللَّـهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْ‌وَةِ الْوُثْقَىٰ لَا انفِصَامَ لَهَا ۗ وَاللَّـهُ سَمِيعٌ .

Allah kenan babu abin bauta da gaskiya sai shi, Rayayye Tsayayye, Gyangyadi ko Bacci bai daukarsa, abinda yake Sammai da yae Kasa duka nasa ne, wane ne zai yi ceto sai bayan bada izini daga gareshi? Allah ya san abin yake gabansu da abind ayake bayansu. Basa kewaya da wani abu daga iliminsa sai abin da ya so, Karagarsa ta Mamaye Sammai da Kasa, kula da su bar da wahala a kansa, hakika shi Madaukaki Mai girma. ________________________________________ Ayar Kursiyu ko Ayoyin Kursiyu Abinda ya shahara a tsakankanin Malaman tafsirin Shi’a shine cewa aya ta 255 cikin Sutaul Bakara itace kadai Ayar Kursiyu 3 sauran ayoyi biyu da suka biyo bayanta bas a cikinta 4 a cewar Sayyid Muhammad Husaini Tahrani, Allama Tabataba’i Marubucin Tafsirul Almizan sun tafi kan cewa Ayar Kursiyu itace aya 255 kadai cikin Suratul Bakara wacce ta gama da jumlar (kuma shi ne Madaukaki Mai girma) 5 Mukarin Shirazi daya daga Malaman tafsirin Shi’a ya kawo shaidu daidai har guda shida kan cewa takaituwar taken Ayar Kursiyu a iya aya ta 255 cikin Suratul Bakara, daga jumlar shaidar kamar:

  • Baki dayan Riwayoyin da aka nakalto kan falalar ayar kadai aya ta 255 suka ambata.
  • Kalmar Kursiyu a iya aya ta 255 ta zo.
  • A ba’arin wasu Riwayoyi ya zo cewa ayar Kursiyu kadai tana da kalmomi guda 50 kuma kadai ta zo na a aya ta 255 cikin Suratul Bakara 6 a ra’ayin Malamin umarnin da aka bayar na aka karanta sauran ayoyi biyu da suka zo a bayanta ba a kirasu da Taken Ayar Kursiyu ba 7

Sannan akasin ra’ayin da ya shahara wasu ba’ari tare da dogara da ba’arin wasu riwayoyi 8 [Yadasht] ayoyi na 256-257 cikin Suratul Bakara sun tafi kan cewa suna cikin Ayar Kursiyu 9 wadannan riwayoyi sune suka zama sababin risker da wadannan ayoyi biyu cikin Ayar Kursiyu a ra’ayin wasu Malaman Shi’a, daga sauran dalilan da suka sanya risker da ita ayoyin 256-257 ga Ayar Kursiyu akwai damfaruwar a mai zurfi tsakanin Abinda wadannan ayoyi suka kunsa da Ayar Kursiyu 11 Sayyid Muhammad Kazim Tabataba’i Yazdi cikin littafin Urwatul Wuska yana ganin karanatawa daga 255 karshen aya ta 257 (sunan masu Dawwama cikinta) yafi dacewa da Ihtiyadu 12

Kalmar Kursiyu

Kalmar Kursiyu tana da wasu adadin ma’anoni 1 Karagar Mulki da Gado 2 Masarauta da wurin bada Umarni, Gudanarwa 3 Cibiyar Umarni da Gudanarwa 4 Ilimi 13 ance abin nufi daga Kursiyu a wannan aya shine Hukuma da Kayyumiya tsayuwa kan dukkanin abubuwa, Mulki da gudanarwar Allah 14 Ya zo cikina riwayoyi daban-daban daga Imaman Shi’a cewa Kalmar Kursiyu cikin wannan an fassarata da Ilmin Allah, sai ma’anar aya ta zamana: (Allah ya san abinda yake gabansu da wanda yake bayansu kuma basu tsinkaya da wani abu daga iliminsa sai abinda ya so. Kursiyunsa (=iliminsa) ya mamaye Sammai da Kasa 15 kan asasin hadisin da aka nakalto daga Imam Sadik (A.S) Kursiyu wani kebantaccen ilimin Allah ne da dukkanin Annabawa da da sauran Hujjojin Allah basu tsinkaya kansa ba 16

Abinda ta tattara kansa

Ayar Kursiyu ay ace da ta tattaro wasu adadin siffofin Jalal da Jamal 17 kasancewa an bijiro da sunayen da siffofin daidai har guda goma sha shida da wannan dalili da ya ake kiranta da take da sakon Allah 18 wannan aya ta tattaro siffofin zatin Allah daga cikinsu akwai Dayantaka, Rayuwa, Kayyumiya, Ilimi da Kudura haka kuma ta tattaro siffar aiki misalin Malikiyya Mallakar kan Duniyar samuwa da Ceto 19 Malaman tafsiri sun faifaice bahasi kan Rayuwar Allah cikin karshen wannan aya jumlar Hayyu Alkayyum da Alkursiyu , da kuma danganewar dukkanin halittu zuwa ga Allah sannan sun bayyana cewa abin nufi da Kursiyu shine Al’arshin Allah 20

Falala da Hususiya

Sayyid Muhammad Husaini Tabataba’i cikin Tafsirul Almizan ya tafi kan cewa girmamar Ayar Kursiyu ya kasance bisa la’akari da tattararta kan dandakakkun Ma’arif din Allah dangane da Tsantsar Tauhidi da mudlakin Kayyumiya 21 Cikin Falalar ayar Kursiyu an nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa Ayar Kursiyu itace Shugabar Ayoyi kuma itace mafi fifitar su, kuma ta tattaro dukkanin alherin Duniya da Lahira 22 a wata riwayar ya zo cewa ayatul Kursiyu itace shugabar dukkanin Maganganun Kur’ani, sannan kum Suratul Bakara itace Jagaban Kur’ani, sannan ayatul Kursiyu itace shugaban Bakara 23 Musulmai suna matuka damuwa da girmama wannan aya, hakan ya samo asali kasantuwar ta kunshi dukkanin ilimin sanin Allah da koyarwar Muslunci kan asasin karfafaffen Tauhidi, hakika Tauhidi ya kasance da Kammalallen shakali tareda yin bayaninsa a dunkule, wannan aya ta siffanta zatin Allah da siffofin aikinsa 24 Dangane da Hususiya Tilawarta akwai riwayoyi masu tarin yawa daga bangaren Shi’a 25 da Ahlus-Sunna, 26 cikin wata riwaya daga Imam Sadik (A.S) ya zo cewa duk wanda ya karantata sau daya zai kawar masa da bala’i dubu daga bala’o’in duniya kuma mafi saukin cikinsu shine Talauci, haka kuma zai kawar masa wahalhalu dubu na Lahira mafi saukin cikinsu itace azabar Kabari 27 Kan asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) ya zo cewa: idan mutum ya karanta lokacin da yake fama da ciwon ido kuma ya karantata da niyyar samun lafiya insha Allah zai samu lafiya 28 a imanin Mutanen gari suna ganin dacewa dora hannu kan idanu lokacin da ake karantata sai dai cewa wannan abu da suke bai da ingantaccen isnadi [] amma Kaf’ami cikin littafin Junnatul Al-Amanul Al-Wakiya daga Sayyid Tawus ya kawo wata kissa da take da danganta kan wannan al’ada 29

Wuraren da ake Karantata

Kan asasin Riwayoyi hakika an wasiyya da karanta Ayar Kursiyu abu ne mai kyau a kowanne wuri musammam bayan idar da Sallah da kafin kwanciya bacci, lokacin fita daga gida da lokacin da mutum yake fuskantar wani hatsari ko wahala, da lokacin hawan abin hawa, haka nan tana da matukar amfani kan tsari daga Kambun Baka, da neman lafiya 31 a wata riwaya daga Imam Ali (A.S) ya zo cewa: da kun san mece ce wannan aya ko kuma cikin me take ba zaku taba sakaci da karanta ta taba a kowanne hali 32 Malamin Fikhu suna ganin mustahabbancin karanta a wadannan wurare kamar haka: bayan gama Alwala, karantawa wanda yake daf da mutuwa, bayan idar da sallolin Farali, lokacin kwanciya bacci, lokacin tafiya da sauransu. 33 haka karanta wannan sura cikin ba’arin Nafilfili misalin Nafilar Ghadir da sallar daren farko cikin Kabari (sallar Wahasha) 34

Sanin Littafi

Malamai masu tarin yawa sun rubuta littafi sukutum kan wannan ayar daga cikinsu akwai Abdur-Razak Kashani, shamsud-Addini Khafari, d Mulla Sadra karkashin Taken (Tafsir Ayatul Kursiyu) haka Muhammad Takiyu Falsafi shima ya rubuta littafi da taken (Ayatul Kursiyu Payam Asimani) Husaini Suzanci shi ya tsara. an buga a cibiyoyi daban-daban