Jump to content

Shuraihu Ɗan Hani Alharisi

Daga wikishia

Shuraihu ɗan Hani Alharisi Alminhaji Alkufi, (larabci:شريح بن هاني الحارثي المذحجي الكوفي) ya yi wafati a shekara ta 78 hijira, ɗaya ne daga cikin shuwagabanin sojojin Imam Ali (A.S) a yaƙin Jamal, Siffin da kuma Nahrawan.[1] Imam Ali ya aika mishi da wasiƙa a lokacin da ya naɗa shi a matasayin kwamandan sojojin da ya tura zuwa yankin Sham.[2] a cikin wasiƙar ya yi mishi wasiyya da jin tsoran Allah, kuma yana jan kunnan shi daga ruɗuwa da yaudara ta duniya da kuma son zuciya.[3] amma malam Makarim shirazi a cikin sharhin Nahjul Balaga yana ganin dalilin yin wannan wasiyya ta Imam Ali (A.S) ga Sharaihu, shi ne shaiɗancin Mu'awiya kan yaudara, musammam shi mutum ne da aka sani wajen yaudarar kwamandojin sojojin Imam Ali (A.S), ko kuma dalili shi ne sabo da shi Shuraihuhu yana da saɓani da wani shugaban sojojin Imam Ali (A.S) kamar Zayad ɗan Nadar.[4]

Wasika daga Imam Ali (A.S) zuwa ga Shuraihu bin Hani Kaji tsoron Allah safe da maraice, kuma kaji tsoron ruɗuwa da duniya, kuma kada ka amince da ita ta kowacce hali, kuma ka sani cewa idan ba ka kau da kai daga yawancin abin da kake so ba, don tsoron wani abu mara kyau, lallai zata kai ka zuwa ga cututwa su yi maka illa mai yawa, don haka ka zama mai hanawa kanka, kuma ka zama mai hana kanka da sha'awarka idan ka yi fushi.

[5]

Bayan faruwar matsalar tahkim tsakanin sojojin Imam Ali (A.S) dana maƙiya, Shuraihuhu ya yi jayayya da Amru bin Asi. Domin kuwa ya yaudari Abu Musa Al-Ash'ari, ya buge shi da bulala.[6] kuma sunan shi ya zo cikin waɗanda suka ba da shaida a kan Hujur ɗan Udai, amma bisa abin da ya zo a cikin tarihi na ɗabari shi Shuraihu ya ce baya cikin waɗanda suka bada shaida kan hujuru ɗan Udai, kuma ya dauki wasikar zuwa ga Muawiyah a matsayin aikin Ziyad bin abihi.[7]

Shuraihu ya ruwaito daga babanshi, Imam Ali da A'isha da Sa'ad ɗan Abi Waƙas da Umar ɗan Khattab.[8] da sauransu.[9].tabbas mutane dayawa sun rawaito daga gare shi daga cikin su akwai babanshi mai suna Muƙaddam da Muhammad.[10] Kamar yadda Ibn Hajar Al-Asƙalani ya ce, Al-Nasa'i da Ibn Mu'ayyan sun ɗauke shi a cikin Suƙat wato waɗanda basa ƙarya a wajan rawaito hadisi, kuma ɗan Hibban ya ambace shi a cikin Suƙat.[11]

Baban Shuraihu ya kasance shi ne Hani ɗan yazid Alharisi ɗaya daga cikin sahabban Annabi (s.a.w) kuma Annabi ne ya kira shi da wannan laƙabin Aba Shuraihu.[12] kuma an anbace tarihin Shuraihu a cikin wasu litattafai da aka rubuta a kan sahabbai.[13] kuma shi Shuraihu ya riski Annabi, amma bai haɗu da shi ba.[14] sai dai cewa ɗan Sa'ad ya ce shi Shuraihu yana cikin Tabi'ai ne a Kufa.[15] kuma an kashe shi a yaƙin Sajistan a shekara ta 78.[16] kuma Ibni Hajar Al'asƙalani ya ce shi Shuraihu ya yi shekara ɗari da goma a duniya.[17]

Bayanin kula

  1. Al-Tabari, Tarikh Al'umam wa Al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 565; Ibn Saad, Al-Thabaqat Al-Kubra, juzu'i na 6, shafi na 180.
  2. Nahj al-Balagha, Tashihu Subhi Saleh, Al-Risala 56, shafi na 447.
  3. Nahj al-Balagha, Tashihu Subhi Saleh, Al-Risala 56, shafi na 447.
  4. Makarem Al-Shirazi, Payam Ayyam Amirul Muminin (a.s) (Shafi na 11, shafi na 182).
  5. Nahj al-Balagha, Tashihu Subhi Saleh, Al-Risala 56, shafi na 447.
  6. Al-Masoudi, Murooj al-Dhahab, juzu'i na 2, shafi na 399.
  7. Al-Tabari, Tarikh Al-umam wa AL-muluk, juzu'i na 5, shafi na 270.
  8. Ibn Saad, Al-Thabaqat Al-Kubra, juzu'i na 6, shafi na 180.
  9. Ibn Hajar al-Asqalani,Al-isaba, Mujalladi na 3, shafi na 308.
  10. Ibn al-Atheer, Usudul Al-ghaba, juzu'i na 2, shafi na 628.
  11. Ibn Hajar al-Asqalani, Tahdheeb al-Tahdheeb, juzu'i na 4, shafi na 330.
  12. Ibn Hajar Al-Asqalani, Al-Isaba, juzu'i na 3, shafi na 308.
  13. Ibn al-Atheer, Usudul Al-ghaba, juzu'i na 2, shafi na 628; Ibn Hajar Al-Asqalani, Al-Isaba, juzu'i na 3, shafi na 308.
  14. Ibn Hajar Al-Asqalani, Al-Isaba, juzu'i na 3, shafi na 308.
  15. Ibn Saad, Al-Thabaqat Al-Kubra, juzu'i na 6, shafi na 180
  16. Ibn al-Atheer,Usudul Al-ghaba, juzu'i na 2, shafi na 628.
  17. Ibn Hajar Al-Asqalani, Al-Isaba, juzu'i na 3, shafi na 308.

Nassoshi

  • Nahj Al-Balagha, ingantacce daga Subhi Saleh, Qum, Hijira, bugu na daya, 1414H.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, 'Payam Ayyam Amirul Muminin (a.s) ( Sharhin Nahj Al-Balagha) , Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1386 AH.
  • Al-Masoudi, Ali bin Al-Hussein bin Ali, 'Muruj Az-zahab, bugun: Asaad Dagher, Qum, Darul Hijrah, bugu na biyu, 1409 Hijira.
  • Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, 'Tarikh Al-Tabari, bugun: Muhammad Abu Al-Fadl Ibrahim, Beirut, Dar Ihya' al-Tarat al-Arabi, bugu na biyu, 1387H/1967 AD
  • Ibn Hajar Al-Asqalani, Ahmed bin Ali, ' Al-isaba fi tamyizil Sahaba, bugun: Adel Ahmed Abdel-Mawjoud, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, bugu na 1, 1415 Hijira / 1995 AD.
  • Ibn Hajar al-Asqalani, Ahmed bin Ali, 'Tahdheeb al-Tahdheeb, Beirut, Dar Sader, 1325H.
  • Ibn Saad, Muhammad bin Saad bin Muni', thakat al-kubra, editan: Muhammad Abdulkadir Atta, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, bugu na daya, 1410 Hijira/1990 miladiyya.
  • Ibn al-Atheer, Ali bin Abi al-Karam, 'Zakin Jungle a cikin Ilimin Sahabbai, editan: Ali Muhammad Moawad, da Adel Ahmed Abd al-Mawjoud, Beirut, Dar al. -Kutub al-Ilmiyyah, bugu na daya, 1415H/1994 Miladiyya.