Waki'ar Kai Hari Gidan Fatima (S)

Daga wikishia

Waki’ar Kai Hari Gidan Hazrat Fatima (S) wannan lamari ya faru lokaci da Umar Bn Khaddad tare da Mutanensa suka hallara a kofar gidan Fatima diyar Manzon Allah domin fito da Ali da sauran mutanen da suke cikin gidan domin tilasta su yin Mubaya’a ga Abubakar, kan dogara da abin da Masadir din Shi’a da Ahlus-sunna suka nakalto. Wannan Waki’a ta faru bayan Wafatin Annabi (S.A.W) 28 ga watan Safar, Umar Bn Khaddab ya yi barazana da cewa idan basu fito daga cikin wannan gidan ba zai bankawa gidan wuta ya kona shi. Cikin littafin Salim Bn Kaisi da Isbatul Wasiyyati, da kuma Tafsirul Ayyashi daga cikin Masadir na farko-farko a wurin yan Shi’a ya zo cewa cikin wannan Waki’a an karya Kashin awazarta an kuma bankawa gidan wuta, wanda hakan ya jawo barin jarririn da yake cikinta me Suna Muhassin, sannan bayan wani lokaci ta yi shahada, Masadir din Ahlus-sunna sun karyata batun bankawa gidanta wuta da jima sannan sun bayyana cewa dukkanin Marawaitan Waki’ar Rafilawa ne kuma ababen tuhuma. Dangane da sabubban bayyanar wannan Waki’a ance Abubakar ya bukatu da Mubaya’a daga Imam Aliyu (A.S) domin karfafa Halifancinsa, a cewar Muhammad Hadi Yusufi Garawi wanda aka haifa 1327 hijirar tafiyar rana wanda ya kasance Mai bincike kan Tarihin muslunci, wannan Waki’a ta faru ne bayan kusan kwanaki 50 da wafatin Annabi (S.A.W). Kan asasin nakalin littafin Salim Bn Kaisi da littafin Al’imama was-Siyasa, Fatima (A.S) cikin ganawar da Abubakar da Umar da suka yi da ita, ta tuna musu Hadisin Bad’atu (tsokar jikin Annabi) ta kafa musu shaida da shi wanda haka ya bata musu rai matuka, cikin masadir din Ahlus-sunna an nakalto daga Abubakar cewa a karshen rayuwarsa ya fadi cewa: Inama dai bai bada umarni shiga gidan Fatima (A.S) ba.

Matsayi da Muhimmanci

Waki’ar hari kan Gidan Fatima ta faru ne bayan Waki’ar Sakifa da hadafin karbar Maubaya’a daga Imam Ali (A.S) kan Halifancin Abubakar. [1] wanda hakan ya haifar da sanadiyar Shahadar Fatima (S) [2] suna daga cikin Mas’aloli masu tasirin gaske cikin alakokin Shi’a da Ahlus-sunna, wasu ba’arin masadir na farko-farko ga Shi’a misalil Kitabu Salim Bn Kaisi, Isbatu Wasiyya, Tafsirul Ayyashi, Dala’ilul Imama, sun kawo bayanin [3] Waki’ar kai hari kan gidan Fatima (A.S) kishiyar Masadir din Ahlus-sunna da suka karyata bankawa gidanta wuta da barin `danta Muhassin suka kuma yi inkari kai Marawaitan da bayyana su matsayin Rafilawa wanda ba a yarda da riwayoyin su [4]

Zaman Makokin `yan Shi’a a ranakun Fatimiyya Yan Shi’a duk shekara a lokacin zagayowar ranar shahadar Hazrat Fatima (S) su na shirya zaman makoki tsawon kwanakin da ake kira da Ayyamu Fatimiyya [5]

Matsayin Gidan Fatima da Mutanen Gidan

Ka duba Makalar mai taken: Ahlil-Baiti Wa-Kunehaye Fatima (S) A wata riwaya daga Shi’a da Ahlus-sunna ya zo cewa Annabi (S.A.W) ya na ganin Gidan Fatima da Ali matsayin gida mafi daraja, ya zo cikin wannan aya:

فِی بُیوتٍ أَذِنَ اللهُ أَن تُرْ‌فَعَ وَیذْکرَ فِیهَا اسْمُهُ یسَبِّحُ لَهُ فِیهَا بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ

Cikin wasu gidaje da Allah ya bada izini a ambaci sunan sa cikin su ana tsarkake shi cikin wadannan gida Safe da Yamma. [6] Masadir din Ahlus-sunna sun bayyana sha’anin saukar wasu ayoyin Kur’ani da cewa ya na dangantaka da mutanen gidan Hazrat Fatima da Ali (A.S) da Hassan da Husaini (A.S) daga cikin jumlar wadannan ayoyi akwai ayatu Id’amu [7] da ayatu Tadhir [8] A yanzu haka a wannan zamani gidan Fatima (A.S) yana nan kusa da wasu Amudai hudu.

Sabubba da Damammaki

Asalin Makala: Waki’eh Ghadir wa-Waki’eh Sakifeh Bani Sa’ideh Bayan wafatin Annabi (S.A.W) wasu adadin jama’a daga Muhajirun da Ansaru a taron da aka shirya a Sakifatu Bani Sa’ida sun cimma daidaito kan Halifancin Abubakar [9] a cewar Ibn Kasir Mubaya’ar Abubakar ta faru tun kafin a binne Annabi (S.A.W) [10] daidai lokacin da Imam (A.S) ya shagaltu da shirya jana’izar Annabi (S.A.W) domin binne shi [11] A sha takwas ga watan Zil-Hijja shekara ta goma bayan hijira a hanyar dawowa daga Hajjin Bankwana Annabi (S.A.W) ya nada Ali Bn Abi Talib (A.S) a matsayin Magajin sa [12] Hakika Umar Bn Khaddab a wannan rana yana cikin mutane da suka taya shi murna [13] A cewar Husaini Muhammad Jafari Mawallafin littafin Tashayyu Dar Masiri Tarikh, hakika Abubakar da Umar saboda tsoran raddi mai tsanani daga Imam (A.S) da Magoya bayan sa ne suka kiraye su zuwa yai ma Abukakar Mubaya’a a matsayin Halifa, lokacin da suka fuskanci rashin amincewar su sai suka ga babu abin da ya rage sai yin amfani da karfi da tilasta su [14]

Sharhin Waki’ar

Kan asasin abin da Yakubi Masanin Tarihi a karni na uku ya nakalto, a lokacin taron Sakifa Banu Sa’ida wasu ba’arin Sahabbai misalin Abbas Bn Abdul-Mudallib, Fadlu Bn Abbas, Salmanul Farisi, Abu Zar Gifari, Ammar Bn Yasir da Barra’u Bn Azib sun ki yi ma Abubakar Mubaya’a [15] Sayyid Murtada Askari Mai binciken tarihi a karni na sha biyar hijiri, ya bayyana cewa dukkanin wadanda ba su yi wa Abubakar Mubaya’a ba, sun kasance tare da Ali (A.S) cikin gidan Fatima (A.S) sun boye kawukansu a gidan [16] Tabari ya kirga Dalha da Zubairu cikin wadanda suka gudu suka boye kawukan su a gidan [17]

Umarnin kan Karbo Mubaya’a daga Ali (A.S) da Wadanda suke Tare da Shi

Abubakar bayan gama yi masa Mubaya’a a Sakifa sai ya waiwaya zuwa ga wasu mutane da basu amince da Halifancin sa ba [18] bisa abin da ya zo cikin littafin Al-Imamatu Was-Siyasa wanda ake danganta shi ga Ibn Kutaiba ya kawo cewa karo hudu Abubakar yana aika Umar da Kunfuz gidan Fatima domin karbo Mubaya’a daga Ali da mutanen da suka gudu gidan suka fake a can [19] kan asasin wannan nakali, a karo na farko mutanen da suke cikin gidan sun fito waje sun yi Mubaya’a bayan barazana da Umar ya yi musu, Ali (S.A.W) bai fito ba sakamakon ya yi rantsuwa cewa bazai fito sai an tattaro Kur’ani an harhada shi, a karo na biyu da na uku Abubakar ya aika Kunfuz gida domin kiran Ali ya fito ya yi Mubaya’a, a wannan karo ma sai yaki, a karo na hudu sai Umar da wasu mutane suka kara zuwa gidan Fatima (S.A.W) suka fito da Ali suka kaishi wurin Abubakar [20] a cewar Muhammad Hadi Yusufi Garawi Mai binciken Tarihin Muslunci da Shi’anci, Abubakar sau uku ya aika mutane Gidan Ali (A.S) yana neman ya yi masa Mubaya’a, a karo na farko da na biyu Imam ya komar da su, a karo na uku sai suka yi amfani da karfi.[21] A cikin littafin Al’iktisas wanda ake danganta shi ga Shaik Mufid ya zo cewa lokacin da suka dauko Ali (A.S) suka fuskanci Masallaci da shi, Zubairu daya daga cikin wanda suka kasance sun gudu gidan Fatima (S) ya zare Takobi ya ce: Ya ku `ya`yan Abdul-Mudallib shin wai kuna raye kuwa da ake ma Ali irin wannan wulakanci haka?! Ya kai Hari kan Umar sai dai cewa Khalid Bn Walid ya wurga Dutse kan Takobin da ke hannun sa ta fadi kasa, Umar ya yi wuf ya dauke Takobin ya bugata kan wani Dutse ya karya ta [22] bisa nakalin Tabari Malamin tarihi na karni na uku, Zubairu lokacin da yake fitowa daga gidan Fatima (S) kafar sa ta girgiza Takobin ta fadi daga hannunsa [23] Bayan nan suka tafi da Ali (A.S) wurin Abubakar sun masa barazana idan bai yi Mubaya’a ba za su sare masa kai [24] a cikin littafin Salim Bn Kaisi ya zo cewa a wurin wannan taro Ali (A.S) ya kafa musu hujja da maganar Annabi (S.A.W) ranar Ghadir da wasu wuraren dangane da Halifancinsa ya tunanar da mutanen da suka hallara wannan wuri, sai dai cewa Abubakar ya ce wai ya ji daga bakin Annabi (S.A.W) Annabta da Halifanci ba za su tattaru ba duka a wurin Ahlil-Baiti [25] A cewar Shaik Mufid Ali bai yiwa Abubakar Mubaya’a ba a ranar Sakifa, amma batun cewa bayan wannan rana ya masa mubaya’a ko bai yi ba, an nakalto maganganu daban-daban, daga cikinsu akwai maganar cewa bayan kwanaki Arba’in ko wata shida da Shahadar Fatima (S) ya yi masa Mubaya’a, Shaik Mufid ya tafi kan cewa babu lokacin da Ali (A.S) ya yi Mubaya’a ga Abubakar [26] Kan asasin wata riwaya a lokacin da aka yi barazana ga Ali (A.S) idan bai yi Mubaya’a ba za su sare kansa, Abbas Baffan Annabi (S.A.W) a yunkurinsa na ceton ran Ali (S.A.W) ya kama hannun sa ya dora kan hannun Abubakar, sannan suka kyaleshi [27] littafin Al-Imamatu Was-Siyasa ya nakalto cewa Abubakar ya fadi cewa matukar Fatima tana kusa da shi to ba za su tilasta mata yin mubaya’a [28]

Martanin Fatima (A.S)

Bayan mutanen da Abubakar ya aiko a karo na farko domin tafiya da Ali (A.S) da wadanda suke tare da shi sai suka je gidan Fatima (A.S) sai ta je bakin kofa tace: ban taba ganin mutane mafi muni daga gare ku ba kun bar mana Jana’izar Manzon Allah (S.A.W) kun yi tafiyar ku kun yanke shawarar kanku (cikin Halifanci) baku tuntubemu ba kun ji menene ra’ayinmu baku bar mana hakkinmu ba [29] A karo na hudu da Umar ya je gidan domin tafiya da Ali (A.S) Fatima (S) ta yi kara da daga sauti tana fadin: ya Baba ya Manzon Allah, bayanka kalli abin da muke fuskanta daga `dan gidan Khaddabi da dan gidan Abu Kuhafatu! Wasu ba’ari daga wadanda suke tare da Umar sun tasirantu da abin da ta fada jikin su ya yi la'asar sun janye kan su sun koma [30] A cewar Yakubi, Fatima ta yi Magana ga wadanda suka shigar mata gida da karfin tsiya (Na Rantse da Allah Idan Baku Fita ba Sai na Daga Sautina Na Nemi Taimako Daga Allah) bayan jin wannan Magana da ta yi sai suka fice daga gidan [31] Abubakar Jauhari wanda ya bar duniya shekara ta 323 h a cikin littafin (Assakifa wa Fadak) ya kawo cewa lokacin Umar ya fito da Ali (A.S) daga gida da karfin tsiya Fatima (S) taje bakin kofa ta cewa Abubakar: mamakin saurin da kuka yi cikin kai hari kan Ahlin Manzon Allah! Na rantse da Allah ba zan taba Magana da Umar ba har komawa ta ga Allah [32] kan asasin wannan riwaya ne daga baya Abubakar ya je wurinta ya nemawa Umar afuwa Fatima ta yafe [33] tare da haka kan asasin riwayar da Bukhari ya kawo cewa dalilin karbe Gonar Fadak Fatima ta yi fushi da Abubakar har karshen rayuwarta bata yafe masa ba kuma bata kara Magana da shi ba [34] Cikin Tafsir Ayyashi nan ma ya zo cewa lokacin da suka fito da Ali (A.S) daga gida, Fatima (S) taje wurin Abubakar ta ce idan ba ku kyale Ali ba zan tafi Kabarin Annabi (A.S) tare da gashin nuna damuwa zan kaiku kara wurin Allah, sai Imam Ali (S) ya aika Salmanul Farisi wurin Fatima ya hanata yin wannan aiki, bayan Fatima (S) taji sakon Ali (AS.) sai ta koma gida [35]

Yin Barazanar Kona Gida

Kan asasin abin da ya zo cikin Masadir din Ahlus-sunna daga cikin su littafin Ikdul Farid [36] Tariku Dabari [37] Ansabul Ashraf [38] Almusannif [39] Al’imamatu Was-Siyasatu [40] an ambaci cewa Umar karkahin umarnin Abubakar ya je gidan Fatima domin fito da Ali (A.S) da wadanda suke tare da shi domin su yi Mubaya’a ga Abubakar, lokacin da suka fuskanci turjiya da naki daga mutanen gidan sai Umar ya bada Umarnin a nemo itatuwa ya kuma yi barazanar kona gidan da mutanen cikinsa, a cewar Abdu Rabbihi Masanin Adabi da Tarihi a karni na 3-4 Abubakar ya cewa Umar idan wadanda suke cikin gidan suka ki fito ka yake su kawai, Umar a lokacin da yake rike da itacen bakin wuta a hannunsa ya yi barazana cewa idan basu fito ba zai bankawa gidan wuta [41] kan asasin abin da ya zo a littafin Al’imamatu Was-Siyasa Umar ya yi barazana sai aka ce masa Fatima fa tana cikin gidan sai Umar ya bada amsa: (eh ko da tana cikin gidan) [42] Cikin masadir na tarihi an kawo sunayen wadanda suka raka Umar zuwa gidan Fatima kan wannan danyen aiki; daga cikin su akwai Usaidu Bn Kudairi, Salamatu Bn Wakash [yadasht] Sabitu Bn Kaisu Bn Shimasu Kazraji [43] Abdur-Rahman Bn Aufi Muhammad Bn Maslamati [44] Zaidu Bn Aslam [45] Sayyid Jafar Shahidi ya tafi kan cewa kona gidan Fatima da Umar ya yi wanda aka nakalto cikin littafan Ahlus-sunna Ansabul Ashraf [46] da Al’ikdul Farid [47] ba zai yiwu ace kagaggen labari bane da shi’a suka kage shi kom kuma wasu `yan siyasa da suka dace da ra’ayin Shi’a, saboda su Shi’a a wannan zamani basu da wani iko da karfi sun ma kasance cikin tsiraru, kari kan wanann bayani a masadir yammacin Muslunci da a can kwata-kwata babu samuwar `yan Shi’a an kawo batun wannan waki’a [48] Shahidi ya yi Imani cewa wanda suka halarci Sakifa Bani Sa'ida abin da yafi damunsu shine mulki ba wai batun addini ba [49]

Kunna Wuta ya Haifar da Ga Fatima (S) da Barin Muhassin

Cikin tsofaffin masadir na Shi’a an nakalto cewa a lokacin waki’ar kai hari a gidan Fatima sun bankawa gidan wuta kuma hakan ya sa ta tabu taji ciwo lamarin da ya haifar da barin cikin danta Muhassin, a littafin Sulaim Bn Kaisi ya zo cewa Umar Bn Khaddab ya zartar da barazanar da ya yi ya bankawa gidan wuta ya shiga ciki lokacin da ya fuskanci turjiyar Fatima sai ya doke a awazarta da Kuben Takobi [50] hakama ya zo cikin littafin Isbatul Wasiyya wanda ake danganta shi da Aliyu Bn Husaini Mas’udi Malamin Tarihi a karni na hudu cewa: sun kai hari gidan kuma sun banka wuta a kan gidan suka fito da Ali (A.S) daga gidan da karfi suka danna kofar gidan daidai lokacin da shugabar matayen duniya take bayan kofar wanda hakan ya jawo barin cikin danta Muhassin [51] a cikin Dala’lul Imama ya zo cewa Umar ne ya baiwa Kunfuz Umarni ya doki Fatima (A.S) [52] Ayyashi Malamin Hadisi na Shi’a a zamanin Gaiba Sugra shima ya ce Umar ya shuri kofar gidan wacce akayi da itacen Dabino sai kofar ta karye suka shiga gidan suka daure Ali (A.S) suka fito da shi waje da karfin tsiya [53]

Lokacin Waki’ar

Ka duba: Ayyamul Mahassiniya Muhammad Hadi Yusufi Garawi Mai binciken tarihin muslunci da Tashayyu. Kan asasin shaidu ya tafi kan cewa lokacin waki'ar bai kasance kai tsaye bayan Taron Sakifa da mubaya’ar Abubakar ba, ya faru kusan kwanaki Hamsin bayan wafatin Annabi (S.A.W) 5 daya daga cikin shaidu shi ne cewa wani mutum da ake kira da suna Buraidatu Bn Husaibi Aslami wanda tare da Sojoji ya tafi Mutata bayan dawowa Madina da jin labarin abin da ya gudana a Sakifa, shi da wasu daga Kabilar su sun karkata ga goyan bayan Imam Ali (A.S) sun ce matukar dai Ali (A.S) bai yi mubaya’a ba mu ma ba zamu yi mubaya’a ba, bayan faruwar wannan abu sai Halifa da mutanen sa suka fara tunanin karbar mubaya’a daga Ali (A.S) a cewar Yusufi Garawi bisa la’akari da lokacin fitar Sojoji da dawowar su da abubuwan da suka faru gabani da kuma baya zamu ga cewa wannan waki’a ta faru ne kusan kwanaki hamsin da wafatin Annabi (S.A.W) [54]

Sakonni

An ambacii wasu sakonni da suka biyo bayan hari gidan Fatima (S) Fushin Fatima (S) kan Abubakar da Umar Ka duba: Hadisu Bad’atu Cikin littafin Sali Bn Kaisi da Al’imamatu Was-Siyasatu, ya zo cewa bayan waki’ar hari kan gidan Fatima (S) Abubakar da Umar sun je gidan ta domin neman uzuri da afuwa sai dai cewa Fatima (S) bata karbe su ba, sai dai cewa sun yi kamun kafa da Imam Ali (A.S) suka ganta, a wannan ganawa ta su Fatima (S) ta juya musu fuska ta kuma tunatar da su fadin Manzon Allah (S.A.W): (Fatima tsokar jikina ce duk wanda ya cuta mata ya cutar da ni ) sannan ta ce ina shaidawa Allah wadannan mutane biyu sun cutar dani sun fusata ni. [55] [yadasht]

Barin Cikin Danta Muhassin da Shahadarta (S)

Asalin Makala: Muhassin Bn Ali (A.S) Shahadat Fatima (S) wa-Ayyamu Muhassiniya Mafi tsufan Masdarin Shi’a da ya nakalto barin Muhassin (A.S) da waki’ar kai hari gidanta shine littafin Sulaim Bn Kaisi daga Masadir din karni na farko galibin masadir din da suka zo daga bayan sa misalin littafan Ihtijaj talifin Ahmad Bn Ali Dabarasi, Gayatul Maram talifin Sayyid Hashim Bahrani, Biharul-Anwar talifin Allama Majlisi dukkanin su daga littafin Sulaim Bn Kaisi suka nakalto [56]

Nadamar Abubakar

A wasu ba’arin Masadir din Ahlus-sunna misalin littafin Tarikh Madinatu Damashk [57] talifin Ibn Asakir, Mujamu Alkabir [58] talifin Dabarani, Tarikh Islam [59] talifin Zahabi ya zo cewa Abubakar a karshen mintunansa na rayuwa ya yi takaici da nadama kan wancan danyen aiki, daga ciki ya fadi cewa inama dai bai bada umarnin shiga gidan Fatima ba.

Mahangar Ahlus-sunna

Bayanin game da barazanar da Umar Bn Khaddab ya yi kan kona gidan Fatima ya zo a cikin littafan Ahlus-sunna misalin Ansabul-Ashraf [60] Tarikul Dabari [61] Al’ikdul Farid [62] Almusannif [63] Al’imamatu was-Siyasa [64] sai dai cewa sun yi inkarin cewa Umar ya bankawa gidan wuta kuma Fatima ta yi barin cikin Muhassin sakamakon danne Kofa, sannan sun bayyana cewa dukkanin Marawaitan Waki’ar Rafilawa ne ababen tuhuma. Muhammad Bn Abdul-Karim Shahristani masanin Firkoki kuma Ba’Ash’are wanda ya bar duniya 548 h cikin bayanin ra’ayoyin Abu Huzaili wanda ya kafa Firkar Huzailiya daya daga cikin Firkokin Mutazilawa yana cewa sun tafi kan cewa Umar a ranar karbar Mubaya’a ya jima Fatima ciwo wanda haka ya haifar da barin danta Muhassin, sai dai cewa Abdul-Karim Shahristani bayan kawo wannan rahoto sai ya karyata shi [65] Khalil Bn Abik Safadi wanda ya bar duniya 746 h marubucin littafin Alwafi Bil-wafyat cikin bayanin Ibrahim Bn Hashim Bn Sayyar wanda aka fi sani da Nazzam daya daga cikin Manyan Mutazilawa, ya zarge shi da karkata da Rafilanci ya nakalto maganarsa cewa Umar ya jiwa Fatima ciwo wanda hakan ya zama sababi da sanadiyyar zubar da cikin danta Muhassin [66]


Bayanin kula

 1. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 2. Tabari Imami, Dala'il al-Imamah, 1413H, shafi na 134.
 3. Sulaim bin Qays, littafin Sulaim bin Qays, 1420H, juzu’i na 1, shafi na 150; Masoudi, Hujja ta nufin, 2004, juzu'i na 1, shafi na 146; Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
 4. Safadi, Al-Wafi Balofyat, 1420 AH, juzu'i na 6, shafi na 15; Dahhabi, “Siyar al-Alaml al-Nubala”, 1405 AH, juzu’i na 15, shafi na 578; Ibn Hajar Asqlani, Lasan al-Mizan, 2002, juzu'i na 1, shafi na 609.
 5. «ایام شهادت حضرت فاطمه الزهرا سلام الله علیها در پاکستان‎»، خبرگزاری ایرنا؛ «مراسم سوگواری شهادت حضرت فاطمه(س) در جمهوری آذربایجان و تاجیکستان»، رادیو ایران تاجیک؛ سوگواری ایام فاطمیه در مرکز اسلامی مرکز اسلامی هامبورگ»، خ
 6. Suratul Nur, aya ta 36; Siyuti, Durrul al-Manthor, Dar al-Fikr, juzu'i na 6, shafi na 203; Erbali, Kashf al-Ghamma, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 313.
 7. Misali, duba: Tusi, Al-Tebyan, Faruwar Al-Tarath Al-Arabi, juzu'i na 10, shafi.211; Tabarsi, Majmael al-Bayan, Daral al-Marefa, juzu'i na 10, shafi na 611 da 612; Haskani, Shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 403-408; Fakhr Razi, al-Tafseer al-Kabir, 1420H, juzu'i na 30, shafi na 746.
 8. Duba: Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1403 AH, juzu'i na 5, shafi na 699; Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi:403; Tabari, Jame al-Bayan, 1420 AH, juzu'i na 20, shafi na 264-267; Ibn Abi Hatim, Tafsir Kur'an al-Azeem, Makaranta Nizar Mustafa al-Baz, juzu'i na 9, shafi na 341-343.
 9. Tabari, Tarikh Al’umam wal Al-Muluk, 2006, juzu’i na 3, shafi na 206; Ibn Athir, Al-Kamal fi al-Tarikh, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 327.
 10. Ibn Kathir, al-Bedaya wa al-Nehaya, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1408 AH, juzu'i na 5, shafi na 268.
 11. Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 2, shafi na 212.
 12. Ibn Kathir, Al-Bedaya wa Al-Nehaya, Darul Fikr, juzu'i na 5, shafi na 209-210; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 233; Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 177.
 13. Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi.284; Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 177.
 14. Jafari, Tashayyu dar Masiri Tarikh, 2006, shafi na 67-68.
 15. Yaqoubi, Tarikh Al-Yaqoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 124.
 16. Askari, Saqifa: Barasi Nahwu Shakli Giri Hukumat fas Payambar, 2007, shafi na 99.
 17. Tabari, Tarikh Alumam wa Al-Muluk, 1387H., juzu’i na 3, shafi na 202.
 18. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 19. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 20. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 21. Yousefi Gharavi, "Tarikh Hujum be Kuneh Hazrat Zahra", shafi na 14.
 22. An jingina shi ga Sheikh Mofid, Al-Khatsas, 1413H, shafi na 186.
 23. Tabari, Tarikh Alumam wa Al-Muluk, 1387H., juzu’i na 3, shafi na 202.
 24. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 25. Sulaimu bin Qays, littafin Sulaim bin Qays, 1420H, mujalladi na 1, shafi na 153-155.
 26. Mufid, Al-Fusul al-Mukhtarah, 1413 AH, shafi na 56-57.
 27. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 68.
 28. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 29. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31; Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 33, shafi na 360.
 30. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31; Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 33, shafi na 360.
 31. Yagoubi, Tarikh Elyagoubi, Dar Sader, juzu'i na 2, shafi na 126.
 32. Johari, Al-Saqifah da Fadak, 1401H, shafi na 53 wa Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, Publisher: School of Ayatullah al-Azmi al-Marashi al-Najafi (RA), mujalladi na 2. shafi na 57.
 33. Johari, Al-Saqifah wa Fadak, 1401H, shafi na 53.
 34. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 AH, juzu'i na 8, shafi na 149, H6726.
 35. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
 36. Ibn Abdu Rabbihi, Al-Eqdul al-Farid, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1404H, juzu'i na 5, shafi na 13.
 37. Tabari, Tarikh Al’umam wa Al-Muluk, 1387H., juzu’i na 3, shafi na 202.
 38. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 586.
 39. Ibn Abi Shaiba, al-Musannaf, 1425H, juzu'i na 13, shafi na 469.
 40. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30.
 41. Ibn Abdu Rabbihi, Al-Eqdul al-Farid, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1404H, juzu'i na 5, shafi na 13.
 42. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30-31.
 43. Shaibani Baghdadi, Al-Sunnah, 1406 AH, juzu’i na 2, shafi:553; Diyar Bakri, Tarikh al-Khamis, Dar Sader, juzu'i na 2, shafi na 169.
 44. Ibn Kathir, al-Bedaya wa al-Nehaya, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1408 AH, juzu'i na 5, shafi na 270.
 45. Allameh Hilli, Nahj al-Haq, 1982, shafi na 271.
 46. Balazari, Ansab al-Ashraf, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 586.
 47. Ibn Abdu Rabbihi, al-Eqdul al-Farid, 1404H, juzu'i na 5, shafi na 13.
 48. Shahidi, Zendagi Fatemeh Zahra, 1363, shafi 109.
 49. Shahidi, Zendagi Fatemeh Zahra, 1363, shafi na 111-112.
 50. Sulaimu bin Qays, littafin Sulaimu bin Qays, 1420H, juzu’i na 1, shafi na 150.
 51. Masoudi, Esbatu Wasiyya, 2004, shafi na 146.
 52. Tabari, Dala'il al-Imamah, 1413H, shafi na 134.
 53. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
 54. Yousefi Gharavi, "Tarikh Hujum Be Kuneh Hazrat Zahra", shafi na 9-14.
 55. Sulaimu bin Qays, littafin Sulaimu bin Qays, 1420H, juzu’i na 1, shafi na 869; Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 31; Tabari Imami, Dala'il al-Imamah, 1413 AH, shafi na 134-135.
 56. Allah Akbari, “Mohsen bin Ali (a.s.)”, shafi na 69.
 57. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damascus, 1415 Hijira, juzu'i na 30, shafi na 422.
 58. Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, Alkahira, juzu'i na 1, shafi na 62.
 59. Dhahabi, Tarikhul Islam, 1413 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 118.
 60. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 586.
 61. Tabari, Tarikh Al’umam wa Al-Muluk, 1387H., juzu’i na 3, shafi na 202.
 62. Ibn Abdi Rabbihi, Al-EqdUL al-Farid, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1404H, juzu'i na 5, shafi na 13.
 63. Ibn Abi Shaiba, al-Musannaf, 1425H, juzu'i na 13, shafi na 469.
 64. Ibn Qutaiba, al-Imamah wa al-Siyasah, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 30
 65. Shahrashtani, Al-Melal wa Al-Nehal, Daral-e-Marefa, Mujalladi na 1, shafi na 57.
 66. Safadi, Al-Wafi Bel wofyat, 1420H, juzu'i na 6, shafi na 15.

Nassoshi

 • Ibn Abi Hatim, Abdul Rahman Ibn Muhammad, Tafsir al-Qur'an al-Azeem, research: Asad Muhammad al-Tayeb, Makkah, School of Nizar Mustafa al-Baz, Beta.
 • Ibn Abishaibah, Abdullah bin Muhammad, al-Musannaf, bincike na Muhammad Lahidan, Riyadh, al-Rashad School, 1425 AH.
 • Ibn Hajar Asqlani, Ahmed bin Ali, Lasan al-Mizan, Beirut, Dar al-Bashaer al-Islamiyya, 2002.
 • Ibn Saad, Muhammad, Tabaqat al-Kubra, Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugun farko, 1410H/1990 miladiyya.
 • Ibnshahrashob, Muhammad bin Ali, al-Manaqib, Kum, Allameh, 1379H.
 • Ibn Abd Rabbah, Ahmad, al-EqdUL al-Farid, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, bugun farko, 1404H.
 • اIbn Asaker Aliyu Bn Hassan تاریخ مدینة دمشق، Darul Fikr Bertut 1415 kamari
 • Ibn Qutaiba, Al-Imamah wa Al-Siyasa, Kum, Sayyid Razi, 1413H.
 • Ibn Kathir, Al-Bedaya wa Al-Nehaya, bincike na Ali Shiri, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na farko, 1408H.
 • Ibn Hisham, Hisham Ibn Abd al-Malik, Al-Sira Al-Nabawiyah, Misr, Mustafa Al-Babi Al-Halabi da Kamfanin Makarantar Sons, II, 1375H.
 • Abuhian Tawhidi, Ali bin Muhammad, Al-Basair da Al-Zhakhar, Beirut, Dar Sadr, 1408H.
 • Abu Naim Isfahani, Ahmed bin Abdullah, Marafah al-Sahaba, Riyadh, Darul Watan, 1419H.
 • Arbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, Kum, Razi, 1421H.
 • Allah-Akbari, Muhammad, "Mohsen bin Ali (a.s.)", Tolo, shekara ta 8, lamba 29, 2008.
 • Amin, Seyyed Mohsen, Ayan al-Shi'a, Beirut, Dar al-Taarif, 1403H.

«ایام شهادت حضرت فاطمه الزهرا سلام الله علیها در پاکستان‎»

 • Bahrani, Seyyed Hashem, al-Burhan fi Tafsir al-Qur'an, Ba'ath Institute, Bita.
 • Muhammad Bn Isma'il Bukhari صحیح البخاری،Binciken Muhammad Zuhair bin Nasser al-Nasser, Dartouq al-Najat, bugun farko, 1422H.
 • Balazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Beirut, Darul Fikr, 1417H.
 • Tabrizi, Hakikat Hujum Be Kuneh Hazrat Fatimah Zahra (a.s.) daga majiyoyin jama'a, Darul Sadiqah al-Shahida, 1397.
 • Tirmizi, Muhammad bin Isa, Sunan al-Tirmidhi, bincike da gyara na Abdul Wahab Abdul Latif, Beirut, Darul Fikr, bugu na biyu, 1403H.
 • Jaafari, Hossein Mohammad, Tashayyu dar Masiri Tarikh, Tehran, Mohammad Taghi Ayatollahi, Cibiyar Buga Al'adun Musulunci ta fassara, 14th, 1386
 • Johari Basri, Abu Bakr Ahmad bin Abdul Aziz, Al-Saqifah wa Fadak, Beirut, Al-Katbi Company for Printing and Publishing, II, 1401 AH.
 • Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed Al-Tanzil Likawa'idul al-Tafdil, Bincike na Mohammad Baqer Mahmoudi, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, bugu na 1, 1411H.
 • Diyar Bakri, Hossein, Tarikh Al-Khamis, Beirut, Dar Sader, Bita.
 • Zahabi, Muhammad bin Ahmad, تاریخ الاسلامBeirut, Darul Kitab al-Arabi, 1413H.
 • Zahabi, Muhammad bin Ahmad, Siyar Al-Alam Al-Nubalah, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1405H.
 • Salim bin Qays, littafin Salim bin Qays, Kum, Al-Hadi, 1420H.
 • Samhodi, Ali bin Ahmed, "Wifea al-Wafa" in Dar al-Mustafa's news, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 2006.
 • Siyuti, Jalaluddin, Alder al-Manthor, Beirut, Dar al-Fekr, Bita.
 • Shahrestani, Mohammad bin Abdul Karim, Al-Melal wa Al-Nehal, Beirut, Daral-e-Marefa, B.T.A.

Shahidi, Sayyid Jafar, Zendagi Fatemeh Zahra, Tehran, Gidan Buga Al'adun Musulunci, 1363.

 • Shushtri, Qazi Nurullah Ahqaq al-Haq da Izhaq al-Batil, Kum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, 1409H.
 • Shibani Baghdadi, Abdullahi bin Ahmad, Al-Sunnah, Dammam (Saudi), Dar Ibn Al-Qayyim, 1406H.
 • Sadouq, Mohammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza, Tehran, Nash Jahan, 1378.
 • Sadooq, Muhammad bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, Research by Ali Akbar Ghafari, Qum, Islamic Publications, 1403 AH.
 • Safadi, Khalil bin Aibak, al-Wafi Bel wofayat, Beirut, Dar Ihya al-Trath, 1420H.
 • Tabrani, Suleiman bin Ahmad, المعجم الکبیر،Alkahira, mazhabar Ibn Taimiyyah, 1415H.
 • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan, Beirut, Daral al-Marefa, Bita.
 • Tabari Imami, Muhammad bin Jarir bin Rostam, al-Mustarashd fi al-Imamah, Kum, Kushanpur, 1415H.
 • Tabari Imami, Muhammad bin Jarir bin Rostam, Dala'il al-Imamah, Qum, Ba'ath, 1413H.
 • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Musa al-Alami, Beirut, 4th, 1403H.
 • Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Taweel al-Qur'an, Beirut, Al-Risala Foundation, 1420 AH.
 • Tusi, Muhammad bin Hasan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Darahiya al-Tarat al-Arabi, Bita.
 • Abdul-Zahra,Mahdi,Nagareshi be Asnad wa Madarik Hujum be Kuneh Sikkeh Zahra shafi na 5, 1391.
 • Allameh Hilli, Hassan bin Youssef, Nahj al-Haq da Kashf al-Saddeq, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, 1982.
 • Eyashi, Mohammad Bin Massoud,Tafsirin Ayashi,Binciken Sayyid Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Mattabah Al-Alamiya, bugu na farko, 1380H.
 • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath, 1420H.
 • Ganji Shafi'i, Muhammad bin Yusuf, Kefaiya Talib fi Manaqib Ali bin Abi Talib, Tehran, Dar Ehiya Tarath Ahl al-Bait, II, 1404H.
 • «مراسم سوگواری ایام فاطمیه در مرکز اسلامی مرکز اسلامی هامبورگ»،Kamfanin dillancin labarai na Mehr, wanda aka buga a ranar 14 ga Maris, 1395, aka duba ranar 2 ga Yuni, 1400.
 • «مراسم سوگواری شهادت حضرت فاطمه(س) در جمهوری آذربایجان و تاجیکستان»،Rediyo Iran Tajik, wanda aka buga a ranar 25 ga Afrilu, 1392, aka duba ranar 2 ga Yuni, 1400.
 • Masoudi, Ali bin Hossein, اثبات الوصیةKum, Ansari, 1384.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Muruj Zahabi wa ma'adin al-Jawhar, Bincike: Asad Daghar, Qum, Dar al-Hajra, karni na 2, 1409H.
 • Mufid, Muhammad bin Muhammad. الفصول المختارهEdited by Ali Mirshrifi, Qom, Sheikh Mofid Congress, bugu na farko, 1413 AH.
 • Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-EKtesas, Ali Akbar Ghafari da Mahmoud Moharrami Zarandi, Qom, Al-Utmar Alami Lalfiya Al-Sheikh Al-Mufid, suka yi bita, 1413 AH.
 • Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Ershad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, 1413H.
 • Muntzari Moghadam, Hamed, "Rashak bar Amirul Muminin (S.A.W) gabatarwa ne ga ilimin halin dan'adam a tarihin Musulunci", Mujallar Tarikh a madubin bincike, 2013, lamba ta 3.
 • Haitami, Ali bin Abi Bakr, Majma al-Zawaed, Alkahira, Mazhabar Qudsi, 1414H.
 • Yaqoubi, Ahmed bin Ishaq, احمد بن اسحاق،.ir/10382/2/3 تاریخ الیعقوبی،Darul Sadek
 • Yousef Gharavi, Mohammad Hadi, [،https://www.noormags.ir/view/fa/articlepage/755042 «تاریخ هجوم به خانه حضرت زهرا (علیها السلام)»]،ayeneh Fajuheshi Shumareh 27Fayiez 1379 shamsi