Daƙiƙa:Salati
- Wannan wata maƙala ce game da fahimtar salati, domin fahimtar aya ta 56 suratul ahzab ku duba shafin ayar salati.

Salati, (Larabci: لصلاة على النبيصلی الله عليه وآله وسلم) yana daga cikin umarnin Kur'ani wanda a cikin aya da take da alaƙa da salati an umarci muminai da yin salati. Wannan aiki yana matsayin alama ta nuna godiya da girmama Annabi kuma sababi ce ta ƙarfafa soyayyarsa wanda cikin adadin litattafan hadisi aka yi bayani game da fa'idojinsa, ciki har da goge zunubai, buɗe ƙofofin sama da samun ceton Annabi.
Mafi shaharar sigar salati shi ne «اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّد» (Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ali Muhammad) wace cikin ba'arin riwayoyin Shi'a aka yi umarni da ita, bayan salati ana faɗin "Wa Ajjil Farajahum". Bisa fatawar malaman Shi'a, wajibi ne yin zikirin salati a zaman tashahhud na sallah (Zaman tahiya), barinsa da gangan yana ɓata sallah, haka nan wajibi yin zikirin salati cikin huɗubobin sallar juma'a da sallar jana'iza.
Yin salati abun yabawa ne a ko wane lokaci, amma yayin jin ambaton sunan Annabi, ruku'u da sujjada a sallah cikin da wasu lokuta na musamman, an yi nasiha mai yawa da yin salati a waɗannan wurare.
Salati a wurin ƴanshi'a ƙari kan ɓangare na ibada da ya ƙunsa, a cikin bukukuwa, tarurrukan addini da ayyuka na yau da kullun ya yaɗu sosan gaske, ƴanshi'a su kan yi salati domin neman biyan buƙatunsu, kuma suna yin khatamar salati.
Falsafa da hikimar salati ta haɗa da neman rahama da ƙarin ɗaukaka ga Annabi da iyalansa, tunawa da su da sunansu da biyayya ga sunnarsu. A cikin al'adun Shi'a, ƙara Alu (Ahlul-Baiti) cikin sigar salati ya yaɗu matuƙa kuma cikin da yawa-yawan madogarai ana lissafa hakan cikin hukunce-hukunce na larura, sai dai kuma Ibn Taimiyya da mabiyansa wahabiyawa, suna rinjayar barin irin wannan sigar salatin na (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad) saboda gujewa kamanceceniya da ƴanshi'a.
Wasu daga Ahlus-Sunna suna fifita salatul Ibrahimiyya kan dukkanin sauran sigogin salati.
Matsayi Da Muhimmanci
Salati, umarni na Kur'ani[1] cikin ayar salati, Allah da mala'iku sun yi salati ga Annabi (S.A.W) kuma Allah ya umarci muminai da su yi salati ga Annabi.[2] Yin salati ɗaya ne daga cikin Sha'a'ir na addini (Alamomi na addini).[3]Salati wata al'ada ce da ta yi matuƙar yaɗuwa tsakankanin ƴanshi'a.[4]
Wasu daga Ahlus-Sunna suna fifita salatul Ibrahimiyya kan dukkanin sauran sigogin salati. sigar salatul Ibrahimiyya shi ne "Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed"[5]
Zikirin salati ya zama wata al'ada da baka raba Musulmi da ita cikin tarurrukansu da ya haɗa da bukukun farin ciki da makoki.[6] Cikin al'adun Shi'a da zarar sun ji ambaton sunan Annabi sai kawai ka ji suna salati suna faɗin Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad, haƙiƙa ana ƙyamar barin yin zikirin salati musamman a irin wannan wurare da ake ambaton sunan Annabi.[7] Wasu ƴanshi'a sun kasance a kodayaushe cikin ko wane hali da lokaci ba sa rabuwa da yin salati, ko kuma yin bakance idan buƙatarsu ta biya za su yi wani ayyanannen adadi na salati.[8]
Bayan wajiban shari'a da karatun Kur'ani haƙiƙa salati ya kasance daga mafi ɗaukaka da darajar ibada,[9] Cikin addu'o'i da aka samo daga Ma'asumai musamman Sahifa Sajjadiyya salati ya zo wurare da daman gaske a cikinsu.[10] Cikin Riwaya an bayyana cewa marowaci na gaske na haƙiƙa shi ne wanda zai ji an ambaci sunan Annabi amma tare da haka ya yi rowar yi masa salati.[11]
Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi ittifaƙi kan wajabcin yin salati cikin tashahhud (Zaman tahiya), kuma idan wani da gangan ya ƙi yin salati to sallarsa ta ɓaci.[12] Wasu malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna suma suna kan wannan ra'ayi.[13] Ƙari kan tashahhud (Tahiya) yin salati ga Annabi da iyalansa a cikin huɗubobin sallar juma'a[14] da sallar jana'iza wajibi ne.[15] Haka nan a cewar Nasir Makarim Shirazi, sanannen malamin tafsiri a Shi'a, bisa abin da ya zo a ayar salati, yin salati ga Annabi (S.A.W) a sau ɗaya wajibi a cikin rayuwar ko wane.[16]
Salati A Cikin Al'adun Musulmi
Salati a cikin al'adun Musulmi yana faruwa a wurare daban-daban kamar lokacin rarrashin jarirai da ƙananan yara, cikin karin magana, lokacin shuka da girbar amfanin gona.[17] A wuraren wasan gargajiya na Zurkhune a ƙasar Iran, musamman ma nau'ukan salawate carke miyan dari (Wani nau'i ne na girmamawa da ake yi ga ɗan wasa yayin da yake gabatar da wasan gargajiya)[18] A ƙasar Iran yana da sasanni na siyasa da zamantakewa, a lokacin da sarki Rida Shah Pahlawi ya kori Imam Khomaini daga Iran, ta kai ga mutane da sun ji an ambaci sunan Imam Khomaini sai su yi salati wanda hakan ya taimaka sosan gaske cikin ƙarfafuwar marja'iyya da jagorancinsa cikin al'umma.[19]
Khatamar salati, wani aiki ne da wasu mutane suke yi da niyyar Ma'asumai kuma domin samun biyan buƙatunsu,[20] sai su yi wani ayyanannen adadin nasalati kamar ƙafa 100, 100 ko 1400 akai-akai babu yankewa[21] Galibi wannan aiki yana kasancewa ne bisa bakance.[22] Khatamar salati ana yinsa da tsarin tara jama'a da za su yi wani ayyanannen adadi a tare da juna.[23] A ƙasar Iran bayan idar da sallar jam'i ɗaya daga cikin masu sallah zai ɗaga murya ya karanta ayar salati sai sauran masallata su yi salati da sigar Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad har sau uku. A cikin littafin Misbahul Mutahajjid an yi nasiha da karanta ayar salati a matsayin ta'aƙibat na sallah (Addu'a da ake yi bayan idar da sallah).[24]
Hikimar Yin Salati
Salati, wani nau'i ne na girmamawa da godiya ga ƙoƙari da wahalar da Annabi ya sha tsawon shekaru 23 kuma ana ɗaukarsa tsani da hanya da yake ƙarfafa soyayyar Annabi a zukatan muminai.[25] Masu bincike suna da ra'ayin cewa yin salati, muminai suna ajiye Annabi da iyalansa a matsayin tsani da tsakaninsu da Allah domin samun rahamar Allah.[26] Kwakwayon kammalallen mutum,[27] girmama Annabi da iyalansa, tunawa da sunansa da tunawa da zaɓaɓɓun Allah, himmatuwa cikin bin tafarkin annabta da wilaya da kuma nuna cewa annabta da imamanci ba sa rabuwa da juna.[28]
Dangane da batun cewa ko yin salati ga Annabi da iyalansa yana da wani alfanu da amfani ko babu, akwai ra'ayoyi guda biyu[29] Mutane kamar Shahidus Sani babban malamin fiƙihu na Shi'a,[30] Allama Ɗabaɗaba'i marubucin Tafsirul Almizan[31] da almajirinsa Hassan Hassan Zade Amoli[32] suna da ra'ayi cewa matsayi da maƙamin Annabi ya kasance da girma da ɗaukakar kuma ya wadatu daga buƙatuwa da salatin muminai, saboda haka alfanu da fa'idojin yin salati suna komawa zuwa ga masu yin salati[33] Akasin wannan ra'ayi, Muhammad Baƙir Majlisi da Murtada Muɗahhari suna da ra'ayin cewa duk da kasancewar Annabi da iyalansa suna da maɗaukakin matsayi da maƙami, amma tare da haka sun kasance suna tafiya kan tafarkin kamala da kammaluwa kuma yi musu salati zai taimaka wajen ƙara ɗaukakuwar matsayi da maƙamansu a wurin Allah.[34]
Idan aka danganta salati ga Allah, to yana da ma'anar rahama, idan kuma aka danganta shi ga mala'iku to yana nufin istigfari, idan kuma aka danganta shi ga mutane to yana nufin addu'a.[35]
Falala Da Fa'idoji
Cikin litattafan hadisai an lissafa lada da fa'idoji masu tarin yawa na ruhaniya da zahiri ga salati. Wasu daga cikin fa'idojin salati sun kasance kamar haka:
- .Kaffarar zunubai[36]
- .Goge zunubai[37]
- .Mafi nauyin aiki kan sikelin auna ayyuka shi ne salati[38]
- .Buɗe ƙofofin sama da zubewar zunubai[39]
- .Soyayya tare da Allah[40]
- .Samun ceton Annabi[41]
- .Daga cikin abin da yake tafiyar da munafunci daga cikin zukata (Ɗaga murya da salati)[42]
- .Tunatar da mutum abin da ya manta[43]
- .Mala'iku suna istigfari ga masu rubuta zikirin salati[44]
- .Amsa addu'a[45]
- .Tsira daga shiga wutar Jahannama[46]
- .Samun biyan buƙata[47]
- .Allah da mala'iku suna salati ga mai yin salati[48]
- .Mafi kyawun aiki a ranar Juma'a[49]
- .Riskar Imam Zaman (A.F) (Zikirin salati bayan sallar asubahi da azahar)[50]
- .Buɗe ƙofa daga cikin ƙofofin lafiya.[51]
- .Mafi alherin addu'a a Ka'aba[52]
- .Tsarkake ayyuka[53]
- .Haskaka kabari, siraɗi da aljanna[54]
- .Mai yin salati zai kasance mutum mafi kusa da wurin da Manzon Allah yake a ranar alƙiyama[55]
- .Zikirin salati daidai yake da zikirin hailala da tasbihi da takbir.[56]
Shin Dole Ne Mu Yi Salati Ga Muhammad Da Iyalansa
Cikin jama'ar Shi'a duk sanda za su yi salati ga Annabi suna haɗawa da ali (Iyalansa)[57] A cewar Sahibul Jawahir, ƙara ali cikin sigar zikirin salati yana daga cikin hukunce-hukunce na larura a mazhabar Shi'a[58] Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, daga cikin shahararrun maraji'an taƙlidi na Shi'a, tare da dogara da wasu riwayoyi[59] ya rinjayar da cewa yin salati ga Annabi ba tare da haɗawa da iyalansa ba haramun ne.[60]
Haka nan bisa wata riwaya wace aka naƙalto ta a madogaran Shi'a da Ahlus-Sunna, an yi hani da yiwa Annabi gutsirarren salati, cikakken salati shi ne wanda aka haɗa da iyalansa (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad).[61] Ƙazi Nurullahi Shushtari ya tattaro waɗannan riwayoyi cikin littafinsa mai suna Ihƙaƙul Haƙƙi.[62]
Abin nufi da Alu bisa ittifaƙin malaman Shi'a, suna mutanen biyar na cikin bargo (Annabi, Ali, Faɗima, Hassan da Husaini) waɗanda ayar taɗhir ta sauka game da sha'aninsu. A cewar Muƙaddasul Ardadili babban malamin Shi'a, wannan ayar ta haɗa da baki ɗayan Imamai Ma'asumai da Sayyida Faɗima, saboda haka dukkaninsu ana lissafa su a matsayin Alu Muhammad.[63] Ahlus-Sunna suma suna ɗaukar cewa abin da ake nufi da Alu su ne mutanen da ayar taɗhir ta sauka game da su, duk da cewa akwai saɓani tsakanin malaman Ahlus-Sunna game da su wane ne masu amsa wannan take da suna.[64]
A cewar Ibn Hajar Haisami daga malaman Ahlus-Sunna, ingantaccen salatin Annabi da aka sani shi ne (Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad) da wannan dalili ne a mazhabar shafi'iyya wajibi yin salati ga Muhammad da ali Muhammad.[65] Amma tare da haka, Ibn Taimiyya daga malamai mabiya tafarkin salafiyya yana cewa duk da cewa daidai da umarnin da Annabi ya bayar wajibi ne idan za a yi salati ga Annabi a ƙara da alu Muhammad, amma sakamakon kasancewar wannan sigar irin wannan salati ta zama wata alama ga ƴanshi'a, to rashin haɗawa da alu Muhammad ya fi alheri.[66] San'ani shima ya yi ishara da cewa goge kalmar "Alu" ta faru a zamanin mulkin Banu Umayya ne sakamakon tsoro da taƙiyya da mutane ke yi.[67]
Bisa wata riwaya da aka naƙalto a cikin Sihahus Sitta na Ahlus-Sunna (Ingantattun litattafai guda shi na Ahlus-Sunna), wajibi yin salati ga Annabi tare da jumlar "Alu Muhammad"[68] Subki daga malaman Ahlus-Sunna, a cikin littafinsa Shifa'us Saƙam ya tattaro lafazi guda (52) da suka zo cikin hadisan Annabi game da salati, mafi yawansu sun ƙunshi "Alu Muhammad" baki ɗayan riwayoyin babu wace aka kawo salati ga sahabbai kamar yadda galibi Ahlus-Sunna suke aikatawa.[69]
An ce Ahlus-Sunna suna da saɓani game da yin salati ga waɗanda ba Annabawa, wasu suna ganin hakan matsayin makaruhi wasu kuma suna ganin cewa yana halatta idan da farko an fara da salatin ga Annabi daga baya aka yi wa wani mutum daban.[70]
A Wanne Wurare Ne Ya Kama Mu Yi Salati

Bisa shahararren ra'ayin malaman fiƙihu na Shi'a[71] yin salati yayin ambaton suna ko alkunya ko laƙabin Annabi (S.A.W), hatta a cikin sallah yana daga cikin aiki na mustahabbi.[72] Wasu malaman suna ɗaukar wannan aiki a matsayin wajibi.[73] Husaini Wahid Khurasani, daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a yana da ra'ayin cewa yin salati yayin ambaton sunan Imam Ali (A.S) aiki ne mai kyawun gaske.[74]
Bisa wasu riwayoyi,[75] an bayyana cewa mafi alherin lokacin yin salati, shi ne dare da ranar juma'a.[76] daga cikin sauran wurare da aka yi nasiha da yin zikirin salati za a iya ishara da wuraren da bayaninsu zai zo a ƙasa:
- Cikin ruku'u da sujjada na sallah[77]
- Farkon fara huɗubobi da laccoci
- Yayin ɗawafi da sa'ayi tsakanin safa da marwa
- A cikin watan Rajab da Sha'aban da Ramadan
- Yayin shiga masallacin harami
- Farko da ƙarshen alwala
- A cikin addu'o'in bayan idar da sallah
- Lokacin ido biyu da masallacin haramin Annabi (S.A.W)
- Kafin da bayan addu'a
- Lokacin shaƙar ƙamshin fure
- Yayin atishawa
- Lokacin tafiye-tafiye.[78]
Mabambantan Sigogi Da Lafuzzan Salati
Mafi shaharar sigar salati shi ne "Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad", amma cikin wasu riwayoyi akwai wasu sigogin daban da aka yi bayaninsu.[79] A cewar wasu masu bincike haƙiƙa a cikin littafin Sahifa Sajjadiyya an kawo bayanin sigogi 210 na zikirin salati.[80]
Bisa wani hadisi, Annabi ya bayyana ingantacce salati da sigar "Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad" ya kuma hana faɗin "Allahumma salli ala Muhammad wa ala ali Muhammad"[81] Sayyid Ali Khan Kabir, marubucin littafin Riyadus Salikin, bai yarda da ingancin wannan hadisi ba,[82] amma Muhammad Baƙir Majlisi yana da ra'ayin cewa haƙiƙa sira tana tabbatar da ingancin hadisi.[83]

Salati Tare da Faɗin Wa Ajjil Farajahum
Wasu daga cikin ƴanshi'a bayan zikirin salati suna faɗin jumlar "Wa ajjil farajahum" ma'ana Allah ka gaggauta sauƙaƙawarsu"[84] wannan zikiri da aka ƙara wata addu'a ta neman gaggauta bayyanar Imam Mahadi (A.F). Bisa wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S), cikin wasu sharuɗɗa da ayyanannen adadi, an yi alƙawarin lada ga wannan aiki, ciki har da samun dacewa da ganin fuskar Imam Mahadi (A.F).[85] kasancewa cikin keɓantattun mataimakansa[86] samun cetonsa a ranar alƙiyama.[87]
Bayanin kula
- ↑ Zamani, "Kayfiyyat-i Salawat az Nigah-i Fariqayn" , shafi na 31.
- ↑ Ibrahimi, Athar wa Barakat al-Salawat, 1432 Hijira (2010-2011 Miladiyya) , shafi na 27-28.
- ↑ Alawi, Athar al-Salawat fi Rihab al-Riwayat, 1437 Hijira (2015-2016 Miladiyya) , shafi na 17.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 3.
- ↑ MuryarHausa:https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/09/Me-Ne-Ne-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW-Karanta-Yadda-ake-Yin-Salatin-Annabi-Muhammd-SAW-a-Mahangar-Sunnah-Falalar-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW.html
- ↑ Fayyad, "Fiqh Fariqayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 165.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariqayn" , shafi na 74.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariqayn" , shafi na 74.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 21.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 21.
- ↑ Misbah Yazdi, Sahba-yi Huzur, 1391 Hijira Shamsi (2012-2013 Miladiyya) , shafi na 459.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariqayn" , shafi na 63.
- ↑ Mawardi, Al-Hawi al-Kabir, 1419 Hijira (1998-1999 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 137.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 11, shafi na 213-214.
- ↑ Husayni Amili, Miftah al-Karamah, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 478.
- ↑ Makarim Shirazi, Payam-i Imam Amir al-Mu'minin, 1386 Hijira Shamsi (2007-2008 Miladiyya) , juzu'i na 3, shafi na 200.
- ↑ Shayesteh Rukh, "Karburd-shenasi-yi Salawat dar Taraneh-hayi Kasht wa Bardasht-i Kishawarzi" , shafi na 165-167.
- ↑ Jawed, "Salawat-khani Hunar-i 'Ibadi-yi Mazhabi az Yad Rafteh" , shafi na 58.
- ↑ Ruhbakhsh, "Salawat-i Siyasi" , shafi na 40.
- ↑ Qazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Nassaji, "Rayihah-yi Ruh-afza-yi Salawat" , shafi na 59.
- ↑ Qazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Qazawi, "Khatm-i Salawat" , shafi na 371.
- ↑ Shaykh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 Hijira (1990-1991 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 50-51.
- ↑ Zamani, "Kayfiyyat-i Salawat az Nigah-i Fariqayn" , shafi na 30.
- ↑ Durudgar, "Asrar wa Athar-i Salawat bar Payambar (S.A.W.) wa Al-i Payambar (S.A.W.)" , shafi na 15.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 24.
- ↑ Kamali, "Naqd-i Didgah-i 'Adam Intifa'-i Payambar (S.A.W.) az Du'a wa Salawat-i Ummat, ba Ta'kid bar Imkan-i Rif'at-i Darajah-yi An Hazrat dar Qaws-i Su'ud" , shafi na 175.
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 13.
- ↑ Duba: Tabatabai, Barresi-hayi Islami, 1388 Hijira Shamsi (2009-2010 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 150..
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 13.
- ↑ Amoli, Hezar wa Yek Nukteh, 1365 Hijira Shamsi (1986-1987 Miladiyya) , shafi na 186.
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 13. .
- ↑ Majlisi, Mir'at al-'Uqul, 1404 Hijira (1983-1984 Miladiyya) , juzu'i na 12, shafi na 112-113; Mutahhari, Majmu'ah-yi Asar, 1389 Hijira Shamsi (2010-2011 Miladiyya) , juzu'i na 23, shafi na 316..
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 Hijira (1996-1997 Miladiyya) , juzu'i na 16, shafi na 329.
- ↑ Shaykh Saduq, Uyun Akhbar al-Rida (A.S.), 1378 Hijira (1958-1959 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 294, Hadisi na 52.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Himyari, Qurb al-Isnad, 1413 Hijira (1992-1993 Miladiyya) , shafi na 14, Hadisi na 45.
- ↑ Shaykh Saduq, Al-Amali, 1376 Hijira Shamsi (1997-1998 Miladiyya) , shafi na 580, Hadisi na 18.
- ↑ Shaykh Saduq, Al-Amali, 1376 Hijira Shamsi (1997-1998 Miladiyya) , shafi na 580, Hadisi na 18.
- ↑ Shaykh Saduq, Ilal al-Shara'i', 1385 Hijira (1965-1966 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 34, Hadisi na 3.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 493, Hadisi na 13.
- ↑ Shahid Thani, Munyat al-Murid, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) , shafi na 347.
- ↑ Shaykh Tusi, Al-Amali, 1414 Hijira (1993-1994 Miladiyya) , shafi na 172, Hadisi na 42.
- ↑ Shaykh Saduq, Thawab al-A'mal, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) , shafi na 155.
- ↑ Shaykh Saduq, Thawab al-A'mal, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) , shafi na 156.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 492, Hadisi na 7.
- ↑ Shaykh Saduq, Al-Khisal, 1362 Hijira Shamsi (1983-1984 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 394, Hadisi na 101.
- ↑ Shaykh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 Hijira (1990-1991 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 368.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, shafi na 59.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 494, Hadisi na 17.
- ↑ Ibn Ash'ath, Ja'fariyyat, Maktabat al-Naynuwa, shafi na 215-216.
- ↑ Rawandi, Al-Da'awat, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , shafi na 216, Hadisi na 581.
- ↑ Tabrisi, Makarem al-Akhlaq, 1412 Hijira (1991-1992 Miladiyya) , shafi na 312.
- ↑ Shaykh Saduq, Al-Amali, 1376 Hijira Shamsi (1997-1998 Miladiyya) , shafi na 73, Hadisi na 4.
- ↑ Fayyad, "Fiqh Fariqayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 165.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 10, shafi na 262.
- ↑ Alal misali, duba: Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 495, Hadisi na 21; Shaykh Saduq, Al-Amali, 1376 Hijira Shamsi (1997-1998 Miladiyya) , shafi na 200, Hadisi na 9.
- ↑ Khu'i, Mawsu'at al-Imam al-Khu'i, 1418 Hijira (1997-1998 Miladiyya) , juzu'i na 15, shafi na 256.
- ↑ Alal misali, duba Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 495; Khargushi, Sharaf al-Mustafa, 1424 Hijira (2003-2004 Miladiyya) , juzu'i na 5, shafi na 107; Haytami, Al-Sawa'iq al-Muhriqah, 1417 Hijira (1996-1997 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 430.
- ↑ Shushtari, Ihqaq al-Haqq, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) , juzu'i na 9, shafi na 524-611.
- ↑ Muqaddas Ardabili, Majma' al-Fa'idah wa al-Burhan, 1403 Hijira (1982-1983 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 277.
- ↑ Rida'i, "Kayfiyyat wa Chigunagi-yi Salawat bar Payambar-i A'zam (S.A.W.) Nazd-i Fariqayn" , shafi na 74.
- ↑ Haytami, Al-Sawa'iq al-Muhriqah, 1417 Hijira (1996-1997 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 667.
- ↑ Ibn Taymiyyah, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) , juzu'i na 4, shafi na 154.
- ↑ San'ani, Subul al-Salam, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 554.
- ↑ Alal misali, duba Bukhari, Sahih al-Bukhari, 1410 Hijira (1989-1990 Miladiyya) , juzu'i na 5, shafi na 351; da juzu'i na 7, shafi na 385; da juzu'i na 10, shafi na 103; Ibn Hajjaj Nishaburi, Sahih Muslim, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 305.
- ↑ Duba: Subki, Shifa' al-Siqam, 1429 Hijira (2008-2009 Miladiyya) , shafi na 407-412.
- ↑ Musawi, "Salawat, Ahkam wa Athar-i An" , shafi na 11.
- ↑ Naraqi, Mustanad al-Shi'ah, 1415 Hijira (1994-1995 Miladiyya) , juzu'i na 5, shafi na 336.
- ↑ Tabatabai Yazdi, Al-'Urwah al-Wuthqa (Al-Muhashsha) , 1419 Hijira (1998-1999 Miladiyya) , juzu'i na 2, shafi na 619.
- ↑ Alal misali, duba: Fadil Miqdad, Kanz al-'Irfan, 1373 Hijira Shamsi (1994-1995 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 133; Shaykh Bahai, Miftah al-Falah, 1405 Hijira (1984-1985 Miladiyya) , shafi na 38.
- ↑ Wahid Khurasani، «yin salati lokacin jin sunan Amirul Mumina (A.S.) a cikin Azan da Ikamah»،Shafin yanar gizo na hukuma na Ofishin Mai girma Ayatullah al-Uzma Wahid Khorasani.
- ↑ Alal misali, duba Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 3, shafi na 429.
- ↑ Nassaji Zawareh, "Salawat Ramz-i Mahabbat wa Wafadari ba Payambar (S.A.W.) wa Khwandanish (A.S.)" , shafi na 64.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) , juzu'i na 3, shafi na 324.
- ↑ Nassaji Zawareh, "Salawat Ramz-i Mahabbat wa Wafadari ba Payambar (S.A.W.) wa Khwandanish (A.S.)" , shafi na 65-66.
- ↑ Fayyad, "Fiqh Fariqayn wa Jaygah-i Ahlulbait (A.S.) dar Salawat" , shafi na 168-169.
- ↑ Samadaniyan, da Saburi, "Salawat wa Payambar (S.A.W.) dar Sahifah-yi Sajjadiyyah" , shafi na 76-77.
- ↑ Majlisi, Lawami' Sahibqarani, 1414 Hijira (1993-1994 Miladiyya) , juzu'i na 6, shafi na 647.
- ↑ Madani Shirazi, Riyad al-Salikin, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 427.
- ↑ Majlisi, Lawami' Sahibqarani, 1414 Hijira (1993-1994 Miladiyya) , juzu'i na 6, shafi na 647.
- ↑ «فرستادن صلوات با عجل فرجهم»، Shafin Tibyan.
- ↑ Shaykh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 Hijira (1990-1991 Miladiyya) , juzu'i na 1, shafi na 368
- ↑ Daylami, A'lam al-Din, 1408 Hijira (1987-1988 Miladiyya) , shafi na 367
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Jamal al-Usbu', 1330 Hijira (1911-1912 Miladiyya) , shafi na 450
Nassoshi
- «Yanayin Salati (Hanyar Salati) daga Mahangar Firkoki Biyu (Ahlus-Sunnah da Shi'a)»، , a Mujallar Hikima da Falsafar Musulunci, lamba ta 8, bazara ta shekarar 1382 Hijira Shamsi (2003 Miladiyya).
- "Firkoki Biyu (Ahlus-Sunnah da Shi'a) da Matsayin Ahlulbait (A.S.) a cikin Salati"
- Alawi, Adil, Athar al-Salawat fi Rihab al-Riwayat (Tasirin Salati a Fagen Ruwayoyi), Qom, Mu'assasah Islami Tabligh wa Irshad, 1437 Hijira (2015-2016 Miladiyya) .
- Alƙur'ani.
- Askari, Sayyid Murtada, Min Sunan al-Nabi (S.A.W.) al-Salat 'ala Muhammad wa Ali Muhammad (S.A.W.) (Daga Sunannin Annabi (S.A.W.): Yin Salati ga Muhammad da Alin Muhammad (S.A.W.)), Tehran, Mash'ar, babu ranar bugawa .
- Baƙiri Baidahendi
- Bukhari, Muhammad ibn Isma'il, Sahih al-Bukhari, Cairo, Wizarat al-Awqaf, 1410 Hijira (1989-1990 Miladiyya) .
- Dailami, Hasan ibn Muhammad, A'lam al-Din fi Sifat al-Mu'minin (Tutocin Addini a Siffofin Muminai), Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (A.S.), 1408 Hijira (1987-1988 Miladiyya) .
- Durudgar, Muhammad Jawad، «"Sirrika da Sakamakon Salati ga Annabi (S.A.W. da kuma Alayansa (A.S) " ko "Asrar da Falalolin Salati ga Annabi da IyalanSa "»،a Mujallar Al'adun Ziyara, lamba ta 7, bazara ta shekarar 1390 Hijira Shamsi (2011 Miladiyya).
- Fadil Miqdad, Miqdad ibn Abdullah, Kanz al-'Irfan fi Fiqh al-Qur'an (Taskar Ilimi a Fikihun Alƙur'ani), Tehran, Murtadawi, 1373 Hijira Shamsi (1994-1995 Miladiyya) .
- Fayyad, Muhammad Ishaq, Al-Istifta'at al-Shar'iyyah (Fatawoyi na Shari'a), babu wurin bugawa, Al-Kalimah al-Tayyibah, 1435 Hijira (2013-2014 Miladiyya)
- Fayyad, Muhammad Sadiq
- Hasanzadeh Amoli, Hasan, Hezar wa Yek Nukteh (Dubu da Daya Nuktehi), Tehran, Rija', 1365 Hijira Shamsi (1986-1987 Miladiyya) .
- Haytami, Ahmad ibn Muhammad, Al-Sawa'iq al-Muhriqah 'ala Ahl al-Rafd wa al-Dalal wa al-Zandaqah (Walƙiya Mai Ƙonawa a kan 'Yan Rafidha da 'Yan Bidi'a da 'Yan Zindiga), Beirut, Mu'assasat al-Risalah, 1417 Hijira (1996-1997 Miladiyya) .
- Himyari, Abdullah ibn Ja'far, Qurb al-Isnad (Kusancin Isnad), Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (A.S.), 1413 Hijira (1992-1993 Miladiyya) .
- Husayni Amili, Sayyid Muhammad Jawad, Miftah al-Karamah fi Sharh Qawa'id al-'Allamah (Mabudin Karama a cikin Sharhin Qawa'id al-'Allamah), Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, babu ranar bugawa.
- Ibn Ash'ath, Muhammad ibn Muhammad, Ja'fariyyat, Tehran, Maktabat al-Naynuwa, babu ranar bugawa.
- Ibn Hajjaj Nishaburi, Muslim, Sahih Muslim, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, babu ranar bugawa.
- Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad Ahmad, Beirut, Mu'assasat al-Risalah, 1421 Hijira (2000-2001 Miladiyya)
- Ibn Taymiyyah, Ahmad ibn Abd al-Halim, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah fi Naqḍi Kalam al-Shi'ah al-Qadariyyah, Riyadh, Jami'at Muhammad ibn Sa'ud al-Islamiyyah, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) .
- Jawed, Hawshang، «"Salati (Karatun Salati) Fasaha ce ta Ibadar Addini da aka manta" ko kuma "Salati: Fasahar Ibadar Addini da ta ɓace"», a Mujallar Astan-i Hunar (Fagen Fasaha), lambobi 4 da 5, bazara ta shekarar 1392 Hijira Shamsi (2013 Miladiyya).
- Kamali, Muhammad Hadi, da sauransu
- Khamseh'i Qazwini, Ali, Al-Salawat Miftah Hall al-Mushkilat (Salati Mabudin Warware Matsaloli), Beirut, Dar Kamil, babu ranar bugawa.
- Khargushi, Abd al-Malik ibn Muhammad, Sharaf al-Mustafa (Darajin Annabi Mustafa), Makkah, Dar al-Basha'ir al-Islamiyyah, 1424 Hijira (2003-2004 Miladiyya) .
- Khu'i, Abul Qasim, Mawsu'at al-Imam al-Khu'i (Kundin Imam Khu'i), Qom, Mu'assasat Ihya Athar al-Imam al-Khu'i, 1418 Hijira (1997-1998 Miladiyya) .
- Kulayni, Muhammad ibn Ya'qub, Al-Kafi (Wanda Yake Isasshe), Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) .
- Madani Shirazi, Sayyid Ali Khan Kabir, Riyad al-Salikin (Lambunan Masu Tafarki), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) .
- Majlisi, Muhammad Baqir, Mir'at al-'Uqul fi Sharh Akhbar Al al-Rasul (S.A.W.) (Madubin Hankaluka a cikin Sharhin Hadisan Iyalan Manzo (S.A.W.)), gyara da bincike: Sayyid Hashim Rasuli Mahallati, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1404 Hijira (1983-1984 Miladiyya) .
- Majlisi, Muhammad Taqi, Lawami' Sahibqarani (Haske Masu Walƙiya na Sahibqaran), Qom, Isma'iliyan, 1414 Hijira (1993-1994 Miladiyya) .
- Makarim Shirazi, Nasir, Payam-i Imam Amir al-Mu'minin (A.S.) (Saƙon Imam Shugaban Muminai (A.S.)), Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1386 Hijira Shamsi (2007-2008 Miladiyya)
- Mawardi, Ali ibn Muhammad, Al-Hawi al-Kabir fi Fiqh Madhhab al-Imam al-Shafi'i (Babban Tarin a Fikihun Mazhabar Imam Shafi'i), Beirut, Dar al-Kutub al-'Ilmiyyah, 1419 Hijira (1998-1999 Miladiyya) .
- Misbah Yazdi, Muhammad Taqi, Sahba-yi Huzur (Jin Dadin Kasancewa), tsarawa da rubutu: Asadullah Tusi, Qom, Mu'assasah-yi Amuzishi wa Pazhuheshi-yi Imam Khomeini, 1391 Hijira Shamsi (2012-2013 Miladiyya) .
- Muqaddas Ardabili, Ahmad ibn Muhammad, Majma' al-Fa'idah wa al-Burhan fi Sharh Irshad al-Adhhan (Tarin Amfani da Hujja a cikin Sharhin Irshad al-Adhhan), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1403 Hijira (1982-1983 Miladiyya) .
- Musawi, Sayyid Rida
- Mutahhari, Murtada, Majmu'ah-yi Asar (Tarin Ayyuka), Tehran, Sadra, 1389 Hijira Shamsi (2010-2011 Miladiyya)
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam (Lu'ulu'u na Magana), Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, babu ranar bugawa.
- Naraqi, Ahmad ibn Muhammad Mahdi, Mustanad al-Shi'ah fi Ahkam al-Shari'ah (Abin dogaron Shi'a a Hukunce-hukuncen Shari'a), Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (A.S.), 1415 Hijira (1994-1995 Miladiyya).
- Nasa'i, Ahmad ibn Shu'ayb, Sunan al-Nasa'i (Sunan Nasa'i), Aleppo, Maktab al-Matbu'at al-Islamiyyah, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) .
- Nassaji Zawareh, Isma'il
- Nassaji, Zahra
- Qazawi, Iffat, "Khatm-i Salawat" (Ƙarshen Salati), a cikin littafin Kilku Kitab (Kalmi da Littafi), wanda Rasul Ja'fariyan ya rubuta, babu wurin bugawa, babu mawallafi, 1393 Hijira Shamsi (2014-2015 Miladiyya).
- Rahimi, Ma'suma
- Rawandi, Sa'id ibn Hibatullah, Al-Da'awat (Addu'o'i), Qom, Madrasat Imam al-Mahdi (A.S.), 1407 Hijira (1986-1987 Miladiyya) .
- Rida'i, Asadullah
- Ruhbakhsh, Rahim
- Sajistani, Abi Dawud Sulayman ibn Ash'ath, Sunan Abi Dawud, Beirut, Al-Maktabah al-'Asriyyah, babu ranar bugawa.
- Samadaniyan, Muhsin, da Omid Saburi
- San'ani, Muhammad ibn Isma'il, Subul al-Salam Sharh Bulugh al-Maram (Hanyoyin Aminci, Sharhin Bulugh al-Maram), Riyadh, Maktabat al-Ma'arif, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) .
- Shafi'i, Ali, Gawhar-hayi Mansur (Lu'ulu'u Masu Tarwatsa), Tehran, Gustarish-i Rayaneh, 1398 Hijira Shamsi (2019-2020 Miladiyya) .
- Shah Ni'matullah Wali, Diwan-i Ash'ar-i Shah Ni'matullah Wali (Diwan na Wakokin Shah Ni'matullah Wali), Kerman, Khidmat-i Farhangi-i Kerman, 1380 Hijira Shamsi (2001-2002 Miladiyya) .
- Shahid Thani, Zayn al-Din Amili, Al-Rawdah al-Bahiyyah fi Sharh al-Lum'ah al-Dimashqiyyah (Lambun Kyakykyawa a cikin Sharhin Lum'ah Dimashqiyyah), gyara da bincike: Hasan Qarubi Tabrizi, Qom, Dar al-Tafsir, 1427 Hijira (2006-2007 Miladiyya) .
- Shahid Thani, Zayn al-Din ibn Ali, Munyat al-Murid fi Adab al-Mufid wa al-Mustafid (Burin Ɗalibi a cikin Da'a na Malami da Ɗalibi), Qom, Maktab al-I'lam al-Islami, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) .
- Shayesteh Rukh, Elaheh
- Shaykh Bahai, Muhammad ibn Husayn, Miftah al-Falah fi 'Amal al-Yawm wa al-Laylah min al-Wajibat wa al-Mustahabbat (Mabudin Nasara a cikin Ayyukan Rana da Dare daga Wajibai da Mustahabai), Beirut, Dar al-Adwa', 1405 Hijira (1984-1985 Miladiyya) .
- Shaykh Mufid, Muhammad ibn Nu'man, Al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-'Ibad (Shiriya a cikin Sanin Hujjojin Allah ga Bayi), Qom, Kungar Sheikh Mufid, 1413 Hijira (1992-1993 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Al-Amali (Majalisai), Tehran, Kitabchi, 1376 Hijira Shamsi (1997-1998 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Al-Khisal (Halaye), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1362 Hijira Shamsi (1983-1984 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Ilal al-Shara'i' (Dalilan Hukunce-hukunce), Qom, Kitabfurushi-yi Dawari, 1385 Hijira (1965-1966 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Ma'ani al-Akhbar (Ma'anoni na Hadisai), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1403 Hijira (1982-1983 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Thawab al-A'mal wa 'Iqab al-A'mal (Ladan Ayyuka da Azabar Ayyuka), Qom, Dar al-Sharif al-Radi, 1406 Hijira (1985-1986 Miladiyya) .
- Shaykh Saduq, Muhammad ibn Ali, Uyun Akhbar al-Rida (A.S.) (Maɓuɓɓugan Labaran Imam Rida), Tehran, Nashr-i Jahan, 1378 Hijira (1958-1959 Miladiyya) .
- Shaykh Tusi, Muhammad ibn Hasan, Al-Amali (Majalisai), Qom, Dar al-Thaqafah, 1414 Hijira (1993-1994 Miladiyya) .
- Shaykh Tusi, Muhammad ibn Hasan, Misbah al-Mutahajjid wa Silah al-Muta'abbid (Fitilar Mai Yin Qiyamullail da Makamin Mai Bauta), Beirut, Mu'assasat Fiqh al-Shi'ah, 1411 Hijira (1990-1991 Miladiyya) .
- Shu'ayri, Muhammad ibn Muhammad, Jami' al-Akhbar (Tarin Hadisai), Najaf, Al-Matba'ah al-Haydariyyah, babu ranar bugawa
- Shushtari, Nurullah ibn Sharif al-Din, Ihqaq al-Haqq wa Izhaq al-Batil (Tabbatar da Gaskiya da Rushe Ƙarya), Qom, Maktabat Ayatullah Mar'ashi Najafi, 1409 Hijira (1988-1989 Miladiyya) .
- Subki, Ali ibn Abd al-Kafi, Shifa' al-Siqam fi Ziyarat Khayr al-Anam (S.A.W.) (Magani ga Cututtuka a Ziyarar Mafi Alherin Halitta), Tehran, Mash'ar, 1429 Hijira (2007-2008 Miladiyya) .
- Tabarani, Sulayman ibn Ahmad, Al-Mu'jam al-Kabir (Kundin Hadisi Mai Girma), Cairo, Maktabat Ibn Taymiyyah, 1415 Hijira (1994-1995 Miladiyya) .
- Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-'Urwah al-Wuthqa fima Ta'ummu bihi al-Balwa (Al-Muhashsha) (Ƙaƙƙarfar Hannu a cikin Abubuwan da Balo'in Ya Kamanta (Tare da Ƙarin Bayani)), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1419 Hijira (1998-1999 Miladiyya) .
- Tabatabai, Muhammad Husayn, Barresi-hayi Islami (Bincike-binciken Musulunci), tare da ƙoƙarin Sayyid Hadi Khosrowshahi, Qom, Bustan-i Kitab, 1388 Hijira Shamsi (2009-2010 Miladiyya) .
- Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an (Al-Mizan a cikin Tafsirin Alƙur'ani), Qom, Daftar-i Intisharat-i Islami, 1417 Hijira (1996-1997 Miladiyya) .
- Tabrisi, Fadl ibn Hasan, Makarem al-Akhlaq (Kyawawan Halaye), Qom, Dar al-Sharif al-Radi, 1412 Hijira (1991-1992 Miladiyya) .
- Tha'lubi, Ahmad ibn Muhammad, Al-Kashf wa al-Bayan 'an Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, 1422 Hijira (2001-2002 Miladiyya)
- Tirmidhi, Muhammad ibn Isa, Sunan al-Tirmidhi, Cairo, Sharikat Maktabah wa Matba'at Mustafa al-Babi al-Halabi, 1395 Hijira (1975-1976 Miladiyya) .
- Wahid Khorasani, Husayn
- Zamani, Muhammad Hasan
- «Muhimmancin yinn salati tare da fadin wa ajjil farajahum», a shafin Tabyan, ranar buga labarin: 29 Azar 1390 Hijira Shamsi (20 Disamba 2011 Miladiyya), ranar da aka ziyarci shafin: 1 Azar 1403 Hijira Shamsi (21 Nuwamba 2024 Miladiyya).
- «Kamshin Salati Mai Raya Ruhi», a Mujallar Pasdar-i Islam (Majalisar Islama), lamba ta 303, Isfand 1385 Hijira Shamsi (Fabrairu-Mar 2007 Miladiyya) da Farwardin 1386 Hijira Shamsi (Maris-Apr 2007 Miladiyya).
- «Takardar salati», a Mujallar Ilmin Hadisi, lamba ta 13, kaka ta shekarar 1378 Hijira Shamsi (1999 Miladiyya).
- "Sukar Ra'ayin Rashin Amfanin Annabi (S.A.W.) daga Addu'a da Salatin Al'umma, tare da Jaddada yuwuwar Hawan Darajar wannan Mai girma a Baka na Hawan (Qaws Su'ud). "،a Mujallar Ma'rifat-i Kalami (Ilimin Tauhidi), lambobi 26, bazara da kaka ta shekarar 1400 Hijira Shamsi (2021 Miladiyya).
- «"Sukar Ra'ayin Rashin Amfanin Annabi (S.A.W.) daga Addu'a da Salatin Al'umma, tare da Jaddada yuwuwar Hawan Darajar wannan Mai girma a Baka na Hawan (Qaws Su'ud). "»،a Mujallar Ma'rifat-i Kalami (Ilimin Tauhidi), lamba ta 26, bazara da kaka ta shekarar 1400 Hijira Shamsi (2021 Miladiyya).
- "Matsayin Salati ga Annabi (S.A.W) da Ahlulbait (A.S) a Alƙur'ani, Hadisi da Addu'o'in da aka ruwaito (Ma'thura) "،a Mujallar Tunanin Alƙur'ani, lambobi 15 da 16, bazara da hunturu ta shekarar 1400 Hijira Shamsi (2021-2022 Miladiyya).
- «"Amfani da Harshe na Salati a Wakokin Shuka da Girbi (Kashi da Bardasht) " ko kuma "Karatu da Nazarin Amfanin Salati a Wakokin Noma na Lokacin Shuka da Girbi "»،a Mujallar Al'adun Mutanen Iran, lamba ta 71, hunturu ta shekarar 1401 Hijira Shamsi (2022-2023 Miladiyya).
- «"Yanayi da Hanyar Salati ga Babban Annabi (S.A.W.) a kusa da ɓangarori Biyu (Ahlus-Sunna da Shi'a) "», a cikin Jaridar Bincike ta Hikima da Falsafar Musulunci, lamba ta 23, hunturu ta shekarar 1386 Hijira Shamsi (2007-2008 Miladiyya).
- «"Salati Alama ce ta Soyayya da Aminci ga Annabi (S.A.W.) da IyalanSa (A.S.) "، a Mujallar Darussa daga Makarantar Musulunci, lamba ta 6, watan Shahrivar na shekarar 1382 Hijira Shamsi (Agusta-Satumba 2003 Miladiyya).
- MuryarHausa:https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/09/Me-Ne-Ne-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW-Karanta-Yadda-ake-Yin-Salatin-Annabi-Muhammd-SAW-a-Mahangar-Sunnah-Falalar-Salatin-Annabi-Muhammad-SAW.html
- «صلوات سیاسی»a Mujallar Zamane, lamba ta 21, Khurdad 1383 Hijira Shamsi (Mai- Yuni 2004 Miladiyya).
- [https://www.noormags.ir/view/fa/articlepage/879829 «فقه "ɓangarori Biyu (Ahlus-Sunnah da Shi'a) da Matsayin Ahlulbait (A.S.) a cikin Salati"
- «"Salati, Hukumce-hukumcenshi da kuma Sakamakonshi (Tasirinshi) "»،a Mujallar Tauhidi da Doka (Ibranci), lamba ta 30, hunturu ta shekarar 1387 Hijira Shamsi (2008-2009 Miladiyya).
- ]،a cikin Jaridar Bincike ta Fikihu (Fiqhu), lamba ta 5, kaka ta shekarar 1390 Hijira Shamsi (2011 Miladiyya).
- ، «yin Salati lokacin jin sunan Amirul Mumina (A.S.) a cikin Azan da Ikamah»،21 Nuwamba 2024 Miladiyya (a kalandar Miladiyya ta yau da kullum).
- ، "Salati da Annabi (S.A.W) a cikin Sahifa Sajjadiyya"»،a Mujallar Alƙur'ani ta Kawsar, lambobi 23, hunturu ta shekarar 1385 Hijira Shamsi (2006-2007 Miladiyya) da bazara ta shekarar 1386 Hijira Shamsi (2007 Miladiyya).